3⃣ : the new friend

1.7K 139 1
                                    

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Tunda Rumasa'u ta koma gida tunanin hanyar da zata taimakawa Abdallah takeyi, haka ta yini ta hantse da tunanin abu daya a ranta kashegari bayan taje school kamar yadda tayi zato bata ga Abdallah ba ta fito a sanyaye ta karasa gurin mai gadi ta mika mishi lunchbox din sannan tayi mai kwatancen Abdallah aikuwa ya ganeshi, tace ya bashi idan yazo inji Rumasa'u, maigadi yace to, ta wuce tana murna, ana yin break Rumasa'u taje gun maigadi ya sanar da ita ya bawa Abdallah bata dade da tafiya ba ya hangeshi, taji dadi har cikin ranta sannan ta koma suka cigaba da harkokinsu itada mufida cikin walwala, Ana tashi kuwa saiga Abdallah ya karaso suka gaisheshi ita da mufida yana ta tsokanarsu wai suna bashi girma alhalin babu wanda ya tabayi mai haka Rumasa'u tayiwa mufida sallama dama ta fadamata duk yadda sukayi akan yau zataje gaida maman Abdallah, itama mufida tanaso ta bisu amma tana tsoron ta bisu azo daukarta ba'a sameta ba shiyasa ta haqura, nan Abdallah yace mata ai gidan nasu ma babu nisa, ana tsallaka titin dake gaban makarantar tasu ne, Rumasa'u tsoro duk ya baibayeta dan bata taba tsallaka titi ba, ta rike hannunshi da sauri ganin yana kokarin yin gaba, juyowa yayi a fusace jin ta rikeshi ya dubeta yaga duk ta rude, a hankali yace "Rumaisa" first time daya kira sunanta, ta dago ta kalleshi jin yadda ya furta sunan nata da nutsuwa tareda bawa kowanne harafi hakkinshi cikin salo na daban, tuni taji duk tsoron ya kau sanda ta kalli kawayar idonshi, ta zame hannunta daga nashi ta dan marairaice "ya Abdallah tsoro nakeji ban taba tsallaka titi ba" tausayi ta bashi yace to rikeni bazakiji tsoro ba in kina taredani, ji tayi kamar an zare duk tsoron, a hankali suka tsallaka titin, komai nashi a nutse yakeyi wannan ne ke kara burgeta, suna tsallakawa kuwa tafiyar kadance sai gasu a wani gida me kama da kongo, babu plasta babu kofa sai dan langa langa da aka kara, Abdallah ya bude, tun a kofar gidan taji tausayinsu ya kara baibayeta ta bishi a baya suka shiga, a tsakar gida suka tarar da dattijuwar zaune, kyakkyawa ce sosai kuma dukda irin wahalar datakesha hakan bai hana kyanta fitowa ba, Rumasa'u ta tsugunna ta gaisheta, amma bata amsa ba sai faman kallonta da takeyi, Abdallah ne yayi ma mama bayani da hannu wacece Rumaisan, mama tayi dan murmushi alamar taji dadin ganinta, sun dan zauna sannan Abdallah yace ya kamata tazo suje kada azo daukanta, haka Rumasa'u ta fita tana waiwayen mama, idanta ya taru da ruwa, suna fita kofar gidan ta ciro wata jaka karama a aljihunta ta miqawa Abdallah tace "gashi amma karka bude sai ka koma gida" yayi murmushi yace angama, tayi dariya saboda yadda ya fada din, suka taho ya maidata inda take zaman jiran driver, kusan duk anzo an dauki yaran har mufida ma basu tarar da ita ba, Abdallah yaqi tafiya yace sai ya jira har anzo an dauketa,, hakan ba karamin dadi yayiwa Rumasa'u ba, suka zauna sukayi shiru, Rumasa'u ta katse shirun da fadin, "ya Abdallah zaka zama abokina?" Abdallah ya dubeta a tsanake yace "meze hana?" taji dadi sannan tace "yanxu na samu karin aboki, kaida mufida ne kawai friends dina" yayi murmushi kawai, sai tace "yaushe zan fara koya maka karatun?" Abdallah yace "Allah ya kaimu gobe sai mu fara" haka har akazo daukarta, ta shiga tana mai jin haushin abinda drivern yake mata, ita bata da ikon kai kararshi tunda tasan iyayen nata busy suke babu mai lokacin saurarenta su a tunaninsu kudi na maganin komai tunda sun bata kudi shikkenan bata da wata sauran matsala, ta lumshe idonta tanajin gajiya sosai a jikinta.... kashegari ta kama friday aka shiryata ta fita school, bisa ga mamakinta tun kafin su karasa ta hangeshi a tsaye ya lankwashe kafa daya ya jingina nesa kadan da gate din makarantar, idan ka ganshi da farko zaka dauka almajiri ne amma idan ka duba sosai zakaga tsaf yake babu ce kurun ta maidashi haka, da hanzari ta fito tana murnar ganinshi a ranta ta ayyana "da alama yaji dadin sakon dana bashi jiya" ta karaso da dan gudunta", ta tsaya a gabanshi tana dariya... dagowa yayi a hankali fuskarshi babu alamar walwala sam ya hade rai gaidashi take niyyaryi amma ya katse ta da fadin "meyasa zaki sato kudi ki kawomin? dan kinga ina cikin bukata? kin daukeni almajiri?" tsayawa tayi sororo tana dubanshi bai fasa cigaba da maganar ba "talaucin nawa har ya kai ki sato kudi a gida Rumaisa? me kike nufi dani ne? ko dan kinga kina bani sadakar abinci ina karba?" idanunshi sun kada sunyi jawurr da tsantsar bacin rai a ciki, wani malolo ne ya tsayawa Rumasa'u a wuya ba da fada yake maganar ba amma muryarshi ta sanar mata da bacin rai dan shi din ba mai hayaniya bane shiyasa, hawaye ne suka gangaro kan fuskarta tana kallonshi, bakin na rawa fuskarta a kwabe alamar zata fara kuka tace "sata ya Abdallah?" "waye ze baki uban kudin nan idan ba satowa kikayi ba" yadda ya fada da d'an fada ne yasata fashewa da kuka saboda kazafin satar daya mata ta saka hannu biyu ta rufe fuskarta, yayi shiru itakuma tanata kukanta, saida ta jima sannan ta dago a tunaninta ma ya rigada ya tafi ne, sai kuma ta ganshi a nan ya rufe idanunshi kawai yayi shiru, jin ta dena kukan yasa ya jayo hannunta ya bude tafikan hannun nata ya saka jakar data bashi jiya ya rufe mata hannun yace "nagode sosai amma bazan iya amsar abinda kika bani ba, daga haka yayi gaba abinshi Rumasa'u ta bishi da kallo har ya kule... ta maida idanunta kan hannunta daya damkawa jakar data bashi jiya, abinda Abdallah bai sani ba shine ba sato kudin tayi ba cikin kudinta ne ta dakko ta bashi saboda tana mishi kwadayin ya samu ingantacciyar rayuwa ya samu ilimi kuma kwata kwata kudin dubu biyar ne ba yawa garesu ba, ta goge hawayenta sannan ta juya jiki a sanyaye,,, tana shiga aji ta zayyanewa mufida abinda ya faru tana share kwalla, ita kazafin satar ne ma yafi mata ciwo, mufida ta nisa sannan tace "Rumasa'u ya kamata ki fahimta shifa Abdallah baisaba rike manyan kudi ba, baze taba kawowa cewar ana bawa yara kamar mu kudi kamar haka ba, musamman ma da baisan wacece ke ba, amma ki bari idan an tashi sai mu sameshi ni zan mishi bayani, Ruma ta gamsu da shawarar mufidan ita dai zuciyarta tana so ta taimakawa rayuwar Abdallah bama kamar dataje gidansu taga yanayin gida da mamanshi suna jin jiki.... har aka tashi babu Abdallah babu labarinshi, har akazo daukan mufida, tsoron tsallaka titi ne ya hanata zuwa gidansu Abdallah, yau kuma saiga driver da wuri yazo itama ya dauketa tunda juma'a ce, tanata kalle kalle haka ta tafi zuciyarta a jagule.. yini tayi sukuku babu wata annashuwa ko farinciki gida kato kuma ba jama'a sai ita kadai cikin daki kamar mayya abin duniya yabi ya taru yayi mata yawa, ranar saturday momy bata fita ba tana gida dan takan ware rana daya a sati ta huta, momy katon shagone da ita na siya da saida kayan sakawa wanda ya shahara a garin kano gurin siyan dalla dallan kayayyaki, na sakawa da mayafai da jakunkuna abindai sai wanda ya gani,
momy na zaune a falo Rumasa'u ta sakko bata dade da tashi daga bacci ba yunwa ta tadata, ta karaso kusa da momy ta zauna,, momy tayi mata alama da tai shiru kallo takeyi, Rumasa'u ta tabe baki ta wuce gurin dining, ta debo abinda zataci a plate ta dawo gurin momy da spoon biyu ta ajiye, tace "momy sakko muci abinci tare" momy ta dan daga mata hannu tana nuna tv din alamar kallo take bataso a dameta, Rumasa'u ta dan yi tagumi tana kallon momy wacce ta maida hankalinta gabadaya ga tv din, ta kara cewa "shikkenan tunda bazakici ba nima na fasa" a fusace momy ta juyo da fada "waini Ruma yaushe kika koma haka, haba bakyajin magana wlhy kina gani dai ina abu mai muhimmanci amma kinbi kin dameni to karkici mana aike ba qanqanuwar yarinya bace yanxu" Rumasa'u ta kurawa momy ido ko kiftawa batayi, ranta ya jagule, ta miqe ta hau sama batareda taci abincin ba

Sharee🙏🤝
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

*koda banyi reply wa messages da comments dinku ba, baya nufin bangani bane, a'a nagani kuma naji dadi, yadda kuka karbi littafin nawa dukda banyi nisa sosai ba, kun karamin kwarin gwiwa, ku cigabada biyoni domin jin yadda zata kaya.... Ayshab. takuce

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now