0⃣8⃣: the ring 💍

1.3K 105 2
                                    

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ruma tazo school saidai abin yayi mata banbarakwai, bataga mufida ba kwata kwata, batazo ta tarbeta ba kamar yadda ta saba, Ruma ta tsaya tana kalle kalle, gabanta ya dan fadi kodai mufida ta tafi batayi mata sallama ba? Ruma ta karasa ajinsu jiki a sabule, nan ma bataga mufida ba, hanyar garden ta nufa da sauri har tana hadawa da sassarfa, a tsaye ta hangi mufidan ta juya baya, Ruma ta ganeta dukkuwa da ta juya din ta karasa da sauri taje ta rungumeta ta baya, ta rintse ido tana maida numfashi, kin tsoratani dayawa mufida, for some moments i thought na rasaki ne, dan Allah karki karayimin hakan" mufida bata motsa ba tunda Ruma ta soma maganar, Ruma jin shiru yasata bude ido a hankali, ta saki mufidan, mufida kuma ta dan matsa gefe kadan, wani cake ne babba ya bayyana a idon Ruma, mufida sai sannan ta juyo tace "HAPPY BIRTHDAY BEAUTIFUL" ta fada tana dariya tana kallon Ruma, Ruma ta tsaya a wajen for some seconds tana kallon cake din, an rubuta happy birthday sister a gefe aka saka 12, ma'ana shekarunta sha biyu, ko ita kanta Ruma bata tuna birthday dinta ba balle kuma iyayen nata da basu damu ba dama, amma mufida ta tuna ras harda sakawa ayi mata cake, Ruma ta rungume mufida  hawaye na qoqarin zuba daga idonta amma bataso ta bata farincikinta, ta dan goge kwallar, sannan ta kalli mufida tace thank you my sister, u re indeed a true sister, thank you thank you, ba karamin dadi taji ba, nan suka yanka cake din, suka rabama classmate bayan sunci sunyi wasa dashi, Ruma ta ajiyewa Abdallah ma nashi, da aka tashi ta bashi, ya tambayi na mene, mufida ce ta sanar dashi yau ne birthday din Ruma ai, ya tayata murna sannan ya saka a ranshi zai kawo mata gift shima amma bai fada mata ba, hira sukeyi su biyu bayan mufida ta tafi, Ruma tace ya Abdallah yaushene naka date of birth din, ya kalleta, ya danyi yake yace "Rumaisa ni kaina ban sani ba" Ruma sai taji wani iri, meyasa ma ta tambaya tunda tasan waye Abdallan, sai ta kawar da zancen da son gyara abinda tayi tace "to shikkenan daga yau na baka ranar birthday na kadinga amfani da ita kaima" Abdallah yaji dadi yayi dariya itama tayi murmushi tace "happy birthday" yace thank you yana mai annashuwa, yace yau na cika 18 kenan tayi dariya tace congrats, dayake Abdallan yasan shekarunshi exact date ne kawai bai sani ba, kashegari kamar yadda ya saka a ranshi hakan kuwa ta faru bayan sun fara hira sai ya ciro abu a aljihunshi a nannade a takarda, ya miqa mata Ruma ta karba tana son sanin mene da dalilin kawo mata din amma bata bude ba sai kallanshi da tayi ta tsareshi da idanu, yace "zobene na kawomiki as ur birthday gift" tana dariya ta bude with lots of excitement all over her face, zobe ne dan karami na gwal bamai tsada sosai ba dan siriri yadda zai shiga hannunta dukda kibar hannun, sai ta kalleshi tace "a ina ka samu kudi ka siyi zobe ya Abdallah" ya gyara zama baison boye mata komai yace "ba siya nayi ba Rumaisa, wannan zoben tun ina karami mama ta damka min shi a hannuna, dukkuwa da bansan me hakan ke nufi ba data bani, kuma nasan bazeyu na saka zoben mata ba, shiyasa na baki dan ke kikafi cancanta daki sanyashi a hannunki" taji dadi sosai, ta dauki zoben ta saka a hankali a yatsanta har ya shige kuma ya zauna amma ya danyi mata yawa, yayi wa farar fatarta kyau ta nuna mai tana murmushi tace "nagode ya Abdallah" ya girgiza kai, banda godiya rumaisa, abuna nakine duka" tayi dariya kawai....

tsakanin momy ko dady babu wanda ya damu da sanin inda ta samo zoben, tadai ce musu birthday gift ne aka bata, ita har mamaki take yadda suke nuna halin ko in kula a kanta, Rumasa'u da Abdallah sun shaqu sosai kamar en uwa, abu kadan ne basu sani ba gameda juna amma kusan komai kowannensu ya sani a gameda d'an uwanshi, sun koma tamkar en uwa ma, saura wata daya suyi hutu, inda Abdallah ke saka ran fara zuwa makarantar boko next session zai fara daga primary, Ruma kuwa tashin hankalinta daya ne, shine tafiyar da mufida tace zatayi idan sunyi hutun, duk tabi ta damu har tafi mufida damuwa, mufidan ce ke kwantar mata da hankali saboda bata qaunar ganin Ruma cikin wata damuwa kwata kwata, wata ranar Alhamis, Ruma da Abdallah suna zaune ta ciro wata paper ta miqa mai, fuskarta dauke da damuwa tace "ya Abdallah inaso na iya zane amma ban iya ba, kalli abinda na zana" ya bude takardar, dariya yayi sosai, saboda wani mummunan zane dayaga tayi, yace mene wannan din kika zana, Ruma tace "kaine" dariya ta kwace mai ya dinga darawa, sosai har yana tsugunnawa kasa saboda dariya, Ruma kuwa ta cika tayi fam, sai ya lura da yadda ta hade rai, ya dan tsagaita yace "am sorry, Ruma" ta tabe baki ta juya mai baya, ya zagayo gabanta ya tsugunna, dan Allah kiyi haquri Rumaisa, ya fada yana rike kunnuwanshi biyu yayi kalar tausayi, saida ya dan jima a tsugunne sannan tayi murmushi alamar ta haqura, ya miqe yana dariya shima, sai kuma ya zauna ya kalleta a tsanake, with serious tone yace "ban taba attempting yin zane ba but nayi miki alkawarin koyan zane kuma na koya miki" Ruma ta kalleshi fuskarta da dumbin farinciki tace "nagode ya Abdallah" ya girgiza kai banda godiya, tayi dariya tanajin dadi a ranta, its been in her dream to know how to draw perfectly musamman data san she can't be a good doctor without knowing how to draw well, yau gashi wani daban wanda babu dangin iya babu na baba yana qoqarin cika duk wani buri nata

Sharee 🙏
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now