2⃣8⃣: new job 2

1.3K 91 6
                                    


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Koda Rumasa'u ta koma gida haka ta kwana tana tuna fuskar khalil, tareda jinjina irin baiwar da Allah yayi mai, Rumasa'u ta tsara zatayi aiki na watanni ukune kawai a gidan in yaso sai ta koma wannan coffee shop din da manager yayi mata alqawarin samun aiki a can.....
Rumasa'u ta tashi da safiyar tayi ayyukanta tayiwa su momy breakfast kowannensu ta zauna ta bashi, to basu fada ba ruma tasan sunajin dadin yadda take kulawa dasu kuma ko basu furta Allah yayi miki albarka ba, tasan Albarka zata bita kuma tasan sun fada a ransu.... Wata atampa Ruma ta dakko wankakkiya ta saka, kalar ja da lemon green, dama dinkunanta nada ne kuma bata dinka zani, wannan ma doguwar riga ce mai kyau,  ta saka gyalenta daya zama outdated dan rabonda tayi upgrading drowernta har ta mance, saidai ma ta siyar da masu tsadan duk dan neman abinda za'a rayu a saka a bakin salati.....  Rumasa'u dama ba baya ba, ta iya daukar wanka kuma yana mata kyau danma yanxu duk gayun ya tafi just natural her, wanda kuma batasan kyanta yapi kyau yanxun ba.... Tape take tana addu'a da patan Allah yasa aikin da za'a bata bamai wahala bane, sai kuma ta tuna ohh rayuwa, duniya budurwar wawa, a da itace keda ma'aikata iri iri, ko jaka ta ajiye saidai azo a dauke mata, waye zece Rumasa'u zata fada wannan rayuwar?  Kuma da ace iyayenta sun taimaki mutane da suma sun samu inda zasu kai kukansu, ko dayake a hakanma Ruma ta godewa Allah dan akwai wadanda rayuwarsu tapi tata kunci, to shikuma ubangiji yace inka godemin sai na kara maka.... Allah ya azurtamu baki daya.... Da wadannan tunanin ta karasa katon gidan nasu khalil, kwankwasawa tayi maigadin ya bude sannan ya tambayeta gurinwa tazo tace mai hajiar gidan ce tace ta dawo yau, ya bata izinin shiga.... Hanyar main falour din ta nupa, bolcony ne sannan kofar falourn, an kawata bolcony din da flowers masu kyau, haka farfajiyar gidan akwai yawaitar bishiyu ta gefe gefe, kana shiga kukan tauntsaye zai maka maraba..... Rumasa'u tayi sallama ta saka kafarta cikin falourn, lokaci daya ta sauke wata ajiyar zuciya saboda sanyi da kamshi gashi shiruu da dan duhu, sai ruma taji tamkar ta kwanta tayi bacci amma ba hali..... Daidai shigarta, aka bude kofa daga cikin kofofin falourn, budurwar jiya ce ta fito, wacce ta gani da khalil.... hannunta rike da waya tana dannawa, fuskar babu yabo babu fallasa, ta karaso gun ruma, saida ta zauna sannan tace ki zauna mana.... Ruma ta zauna... Tace ruma ko?, Rumasa'u tace eh.... Mami ta fadamin zuwanki, ki jirata ta kusa fitowa, Rumasa'u tace to,,,, suna nan zaune zaman shiru har na kusan mintuna 10,,,,, Rumasa'u ta jiyo karan bude kofar falourn, juya bayanta tayi, me zata gani? .....khalil ne sanye da manyan kayanshi coffee harda hula, ruma ta zuba mai ido, a hankali yayi gyaran murya Ruma ta sauke idonta kasa a kunyace.... Cikakkiyar sallama yayi ya shigo falourn, kan kujerar da ruma take a zaune kasanta ya zauna, dan haka koda Ruma ta kalli kasa, sai shekin kafarshi ya dinga janye mata hankali
Ga kamshin turaren daya fesa ya addabeta, da alama irin mutanen nan ne da basu iya fesa turare ba, a rana daya sai su kusan karar da kwalba, irin fuuuuuuuuuuuu lol😂
Yana zama ya jawo remote yace "sakina, kun wani zauna kamar wasu kurame" ni banason wannan dumm din gurin babu annuri, yana fada ya latsa remote din hakan yasa tv din ta kunnu, ana haka, momy ta sakko daga saman stairs din,
Itama taci kwalliya abinta dagwas, bazaka kalleta kace itace ta haifi zangamemen saurayi kamar khalil ba, tana gyara jikinta da daukar wanka yadda ya kamata, Rumasa'u ta kalleta, hakan sai ya tuna mata da momyn ta, a lokacin da take kan daukar gayu iri iri,  ta dan sauke idonta lokaci daya kuma kwalla ta sauka kan gashin idon nata, ta sa hannu a wayance ta goge batareda sun lura ba, koda mami ta karaso Rumasa'u ta tsugunna ta gaida ta dan already dama a kasa take, kusa da khalil mami ta zauna,,, sannan tace "kin cika alqawari Rumasa'u, kuma kimin afuwa na barki kina ta jira" ruma tayi murmushi kawai.... Momy tace "to nidai a gidan nan Rumasa'u ba wani aiki me yawa, saboda akwai ma'aikata a kowanne fanni to zan baki dama ki zabi aikin da kikeso,  amma banda shara ko wanke wanke ko wanki ko goge goge dan wadannan ayyukan sunyi miki tsauri a shekarunki, saboda yanayin girman gidan, misali in kika dau shara kinayi zaki wahala ne dayawa kawai,  to gara ki dauki wani abun daban inaga hakan zepi," tsulum khalil ya tsomo baki,  mami why not ta dinga bawa flowers ruwa ta kula min da tsuntsaye na.... " momy ta juya ta kalleshi, "kashe er mutane zakayi aiki har biyu bakaga yarinya bace" wata kaunar mami ce ta tsirga zuciya da sassan jikin Rumasa'u yadda ta nuna matuqar kulawarta, Rumasa'u ta dago ta kalleta tace "hajia ai zan iya duka babu wani wahala nayi ma wanda yapi wannan" Ruma ta fada tana tuna aikin datayi gidansu halima, dan ba karamar wahala tasha ba, dukda dai momyn ta sassauta mata data kawo hafeez
Mami tace "a'a ruma aikin sunyi yawa, flowers din gidan nan sunada yawa ga gyaran tsuntsaye abin ai sai yayi miki yawa ki dau daya dai" Rumasa'u tayi dariya sannan tace to shikkenan zan dinga kula da tsutsayen,,, momy tayi murmushi tace "to madalla, sai muyi maganar kuma nawa za'a dinga biyanki a wata amma kafin nan... " momy ta dakko wasu kudi cikin jakarta tace ga wannan kiyi jinyar marasa lpia, a kalla kudaden sunkai dubu takwas zuwa goma....Rumasa'u ta karba da dumbin kaunar hajian da irin karamcinta... Nan tayita godiya kamar kar ta dena...

Halima da maryama sun sami admission a uni... Maryama ta karo wulaqanci,  magana ma sai taga kayi mata zatayi halima kuwa in banda soyayyar Ya Amir dake karuwa a ranta babu abinda ke damunta.....

Sorry for d short page....
Unique online writers forum

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now