0⃣7⃣: Rest in peace

1.3K 114 3
                                    


*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

An kammala shirya Ruma cikin school uniform dinta mai kyau wadanda suke kara mata haske da kyau, haka kawai takeji gabanta na faduwa idan ta tuno da Abdallah, jiki a sabule ta kama hanya zuwa school, da mufida ta fara haduwa a compound, sukayi hugging juna cikin kewar juna, Ruma tace "mufida kinga ya Abdallah kuwa?" mufida ta girgiza mata kai, Ruma lokaci daya taji babu dadi a ranta, ko yaya dai ai ya kamata ace yazo sun gaisa tunda dole yasan ta dawo, har aka tashi a school babu Abdallah babu labarinshi, Ruma bata bata lokaci ba sam suna fitowa taja hannun mufida suka tsallaka titi, suka dangana da gidansu Abdallah, a hankali Ruma ta janye kyauren suka shiga, tsaya sukayi suna kallonshi, yana zaune a dandariyar kasa, ya hada kai da gwiwa da alama wani mugun abun ya faru,,, Ruma ta saki hannun mufida ta karaso gurinshi da sauri ta tsugunna, kamshin perfume dinta yaji ya dago da mamaki, hawayene malale a kan fuskarshi, da madaukakin mamaki Ruma ta kalleshi "ya Abdallah kuka kuma?" ta fada tana kwabe fuska alamar itama zatayi kukan, Abdallah yayi hanzarin goge hawayenshi amma bai kaiga gogewa ba wasu masu zafi suka zubo, nan da nan ya shiga yin kuka sosai tun anajin sauti har aka denaji, sai gunji da ajiyar zuciya irin na mazan fama, jijiyoyin kanshi sun fito rada rada fararen idanunshi sun sauya kala gabadaya ruwan hawaye ya taru taf a ciki, ya rame sosai ya qara yin duhu kamar wani skeleton, mufida data kasa motsawa tun zuwansu tana tsaye, itace ta motsa ta karaso kusa dasu ta tsugunna tana gogewa Ruma hawayenta wacce ke taya Abdallah kuka ba tareda tasan nashi dalilin yin kukan ba, mufida tace "ya Abdallah meya faru haka dan Allah ka fadamana dalilin yin kukan" Abdallah cikin dasasshiyar murya mai nuni da alamun yayi kuka sosai yace "mama ta rasu 😭" Ruma ji tayi kamar ya buga mata guduma a tsakar kai, tayi saurin rike kanta da hannu biyu saboda yadda taji kamar ze tarwtse, "mama ta tafi ta barni tun sati daya daya wuce" hawaye suka kwaroro daga idon mufida, tana tsananin jin tausayin Abdallah cikin ranta, "Ruma mama ta tafi batareda ta sanar dani waye ni ba?"ya fada yana jin daci hawaye na zuba sosai kamar an kunna famfo kawai diga sukeyi, innalillahi wa inna ilahi raji'un kurum suke maimaitawa dukka su ukun, har tsayin wani lokaci, sannan nutsuwa ta dan sauko a kirajen su, Ruma ta dubi Abdallah wanda ke cikin mawuyacin hali tace "ya Abdallah, kayi haquri dan Allah, Allah yaji kan mama" ta fada tana jin sabon kuka yana taho mata tayi azamar ficewa waje, mufida ta bita da sauri, a kofar gidan ta tadda ta tana share hawaye, mufida ta dafata tace "dangana zakiyi Ruma...." Abdallah ne ya karaso inda suke yayi dan murmushi na yake dan murmushin ma kamar kuka haka yake yace "Ruma, mufida nagode sosai kunga yanxu yamma tanayi kar azo nemanku ba'a sameku ba, muje na rakaku" mufida tayi saurin fadin "a'a ya Abdallah kayi zamanka zamu iya tafiya" daga haka sukayi gaba shikuma ya koma cikin gidan shi kadai, ruma tunda ta koma gida take a kwance, tunanin rayuwar Abdallah ta addabeta, ashe akwai mutane kamar Abdallah? shikuwa ya zeji ya rasa mama, ni ina can ina hutawa ashe shi yana nan mama ta rasu Allah ya jikanki mama, Allah yayi miki rahama yasa kin huta" ita kadai duk take wannan tad'in zucin zuwa can kuma maganar shi ta fado mata "Ruma mama ta tafi batareda ta sanar dani waye ni ba?" me ubangiji ke nufi daya dauke mama daga rayuwar Abdallah? yanxu mene ne future dinshi kenan?, dama mama ce hop dinshi na samun en uwanshi da danginshi yanxu gashi ta rasu itama, hakan na nufin wahalar dayake ciki zata ninku tafi ta da kenan, haka Abdallah ze kare rayuwa cikin kunci da wahala?" ita kadai takewa kanta tambayoyin amma babu mai amsa mata, ta dan girgiza kai "ni Ruma zanyi iyakar kokarina dan naga ya Abdallah bai kare rayuwarshi cikin wahala ba, in Allah yaso yanadaga cikin masu rabon jin dadi duniya da lahira".....

kashegari Ruma ta tashi dason ganin Abdallah, saidai tasan ba lallai ta ganshi dinba dukda maman tayi sati da rasuwa amma halin dataganshi jiya ya bata tsoro, ta sawa ranta idan an tashi zataje ta dubashi taga wanne hali yake ciki kafin ta koma gida, Ruma da mufida sukaje garden dan cin abinci as always, turus sukayi saboda ganin Abdallah yanata faman aiki, sai lokacin Ruma ta tuna yaufa tuesday ne, Ruma a ranta tace "shi wai baya gajiya ne bayason hutu? sai kuma ta bawa kanta amsa to idan ya hutama dame ze rayu", da azama suka karasa gareshi, Ruma tana mai farincikin ganinshi, Abdallah kamar babu abinda ya dameshi yayi musu murmushi bayan sun gaisa ne Ruma tace "ya Abdallah na dauka bazan ganka ba, saboda rashin da ya samemu" Abdallah yaji dadin yadda take nuna kulawa sosai a kanshi yace "Rumaisa, rasuwar mama kaddarace a rayuwata, kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, na rungumi tawa kaddarar na gane kuka baida amfani, hakan yasa na ajiye komai a baya na cigaba da rayuwa" Ruma taji dadi ta miqa mishi lunchbox din suma suka barshi suka samu guri suka soma cin abincin,, Abdallah yabisu da kallo sannan yace "Allah nagode, domin Ruma, wata hanyace da ubangiji ya turo mishi dayakeji zatazama alkhairi a gareshi, saidai baisan manufar dauke mama da ubangiji yayi ba, amma ya kyale hakan da cewar wa'adinta na zaman duniya ne suka cika, saidai har yau yana mamakin ciwo irin na maman tashi, bataji bata kuma iya mayarwa, amma idan kayi mata bayani da sassan jiki zata gane, saidai ita koda sassan jikinma bazata iya mayar maka ba, kawai dai bazata iya Expressing kanta ba"

rayuwar ta cigaba da tafiya inda Ruma ke fito da sabbin abubuwan da zata daukewa Abdallah kewar mama, Abdallah dayaje tambayar addmission a makaranta baisamu ba sai zuwa next session haka ya haqura, Ruma da Abdallah rannan suna zaune tana karayi mishi bayani kan dalilanta nason zama likita, ya Abdallah likitoci suna kokari, suna taimakon rayuwar Al'umma suna cetan rai da ikon Allah, kuma suna taimakon marasa karfi inaso na zama babbar likitar da kasata zatayi alfahari da ita inda zan dinga taimakon al'ummar annabi" Abdallah yace "nima haka Rumaisa, inaso nazama likita, ruma tace "yawwa ya Abdallah wai kuwa a rayuwarka me kafi so?" Abdallah yayi murmushi yace "Rumaisa" ta dan zaro ido ta nuna kanta da yatsa ni? ya gyada kai tareda dan lumshe ido, tayi dariya sosai hadi da jin dadin wannan kalami nashi, sai tace "to me kafiso kayi? yace "kasancewa tareda Rumaisa" ta kalleshi sosai na wasu seconds sai tace "to menene matsayin Ruma kuma a gurinka?, Abdallah ya nuna kirjinshi da yatsa yace "zuciyatace", *RUMAISA ZUCIYAR ABDALLAH CE* ,,, Ruma ta kura mai ido dukda karancin shekarunta amma ta dan fahimci wani abu cikin kalaman nashi

SHARE 🙏
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

ina qaunarku masoyana a duk inda kuke kuma kuna sakani nishadi ba kadan ba....

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora