0⃣1⃣ : Rumasa'u

5.7K 250 6
                                    

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

*follow Ayshab Nasir @ wattpad*

*Alhamdulillah, nagodewa Allah daya bani ikon fara wannan sabon novel din mai suna zuciyar Abdallah kuma ina godiya gareku masoyana a duk inda kuke, sannan wannan labari kirkirarrene ban yarda a sauyaminshi ba ko ayi amfani da wani sashe nashi, fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke, Ayshab. takuce*

Alhaji Abdulkadir sanannen dan kasuwa ne mai shiga da fitar da kayayyaki da harkokin kwangila, ya tara dukiya sosai daidai gwargwado, yanada matarshi guda daya hajiya shamsiyya inda Allah ya azurtasu da samun yarinyarsu kyakkyawa mace *RUMASA'U* ... ita kadaice diyarsu musamman da hajiya shamsiyya bata da sha'awar tara yara saboda gudun kada ta tsufa haka shima mijin nata bai damu ba, suna zaune ne a cikin garin kano a yusuf road, Alhaji  Abdulkadir asalin bafulatani ne, na garin Adamawa hakama matarshi dan auren gida sukayi, saidai bakin hali dason abin duniya ya sakashi barin cikin en uwanshi ya ware daban, musamman ma yana ganin ya fisu abin duniya, burinshi kullum shine ya tarawa iyalanshi dukiyar da za'a dinga misali dasu a duniya, ansha yin fada dashi da 'enuwanshi kan rashin taimako domin yanxu hakama 'en uwanshi babu wanda ke waiwayar shi saboda ko kazo ma wulaqanci ne yake biyo baya, kowa yaja gefe aka zuba mai idanu, idan ba Rumasa'u ba babu wanda ke cin dukiyar sai kuwa matarshi wacce itama bata kaunar dukiyar ta kare hakan yasa sam basu da kyauta, babu abinda sukafi kyama kamar talaka, shiyasa both momy da dadyn Rumasa'u basa qaunar hada hulda da talaka sam, dan ko cook da masu sharar gidan ma wayayyu ne sosai wadanda ma hausa bata ishesu ba... dadyn Rumasa'u matafiyi ne sosai bai cika zama ba saboda harkokinshi na kasuwanci itama kuma matar tashi tana nata harkokin business din dan ba zurfi tayi a bokon sosai ba,,, Rumasa'u ta taso cikin kadaici na rashin samun kulawar iyayen kuma batada enuwa burin mahaifinta da mahaifiyarta bai wuce su tara dukiya mai matuqar yawa ba, wanda itakuma Rumasa'u sam bata jin dadin zama ita kadai din datake tun tasowartata babu wa ko qani, bata rasa komai na jin dadin rayuwa ba dan kuwa da ana saida rashin kadaici da tuni Rumasa'u ta siya,, halayyar Rumasa'u tasha bambam data iyayenta dan sam Ruma bata da wulakanci tanada son jama'a kuma bata wulakanta na kasa da ita,,shekarunta 11 ne yanxu inda kuma bata dade da shiga jss1 ba, komai na rayuwa Rumasa'u ta samu banda kulawa da soyayyar iyayenta,,,

zaune take kan white sofa din, cikin white bedroom dinta hadadde.. takalminta ake sanya mata da alama an kammala shiryata dan tafiya makaranta, daidai ta kammala ne agogon ya kada 7 daidai, a hankali ta miqe ta nufi down stairs, ta karasa bakin dining din da aka shakeshi da nau'ikan abincikan zamani kala kala na breakfast, kujeru a jere guda 8 amma babu mutun ko guda daya a zaune duka empty, a hankali ta lumshe fararen idanunta, sannan ta bude taja kujera daya ta zauna ta soma breakfast din, loma uku tayiwa abincin taji duk ta koshi, bawai dan batajin yunwa ba saidan bata qaunar cin abinci ita daya, ta miqe ta wuce parking lot ta hau farar motar da akayiwa ado da bakaken glass (tint), ta bude ta zauna, guard dinta da driver suka shigo, suka wuce zuwa school... a kofar makarantar driver yayi parking, tun kafin ta bude ta fito take kallon yaran da iyayensu suke kawosu da kansu, wasu suyi musu kiss sannan su tafi, wasu suyi dan wasanni wasu a dagasu a juya sannan su tafi amma itafa? ta dan sunkuyar da kanta kadan, jiki a sanyaye ta bude motar ta fito ta karbi jakarta da lunch box gurin guard din nata ta wuce abinta... tun kafin ta shiga mufida tazo tayi hugging dinta with lots of joy a kan fuskarta, itama Ruma ta rungume bestyn tata da dumbin farinciki kamar wadanda suka shekara basuga juna ba wanda kullum ne se sunyi hakan, kamar yadda suka saba kafin a fara karatu sai suci abincin dake lunchbox din mufida farko idan anyi break suci na Ruma'n, dan tasan kusan mostly haka Ruma ke fitowa bataci komai ba, dan sun dade.. tare sukayi primary, a bangaren itama Ruma, mufida ce kadai mutumin datake farinciki idan ta ganta wanda ko iyayenta ta gani bata yin irin wannan farincikin,

baya wajen wani garden suka zagaya, basu fiya zuwa nan cin abincin ba kasancewar basu dade da shigowa junior ba cos part din primary dabanne a school din, wasu kejru ne masu kyau a gurin suka zauna sannan mufida ta dakko lunch box dinta dan su fara cin abincin, loma daya Ruma tayi ta tsame hannunta hadi da kurawa guri guda ido, idanunta sun cicciko da hawaye, mufida ta dago a hanzarce tana tunanin menene Ruma ta gani Sabida suna fuskantar junane, ta juya tana bin inda taga Ruman na kalla da hanzari, itama mufida sai ta samu kanta da tsame hannunta daga cikin abincin. Ruma ta dauke kanta ta maida idonta kan mufida tace "mu taimaka mishi dan Allah kinji mufida?" mufida ta jijjiga kanta da hanzari saboda tsananin tausayin daya basu suka miqe dukkansu suka karasa da sauri gabanshi, yana durkushe kayan jikinshi sun kode sosai saboda tsabar wanki babu kuma datti a jikinshi kwata kwata amma akwai alamar yunwa sosai da wahala mai tsanani, kanshi a sunkuye sai haki yake ko sharar dazeyi ma ya kasa, dan a yadda yake jinshi ma kamar baze iya daga koda yatsanshi ba,

ya dan dago idon shi kadan saboda yadda suka tsugunna a gabanshi suka zuba mai ido, Rumasa'u ta dubeshi da tsananin tausayawa, fari ne amma wahala da yawan shiga rana da aikin karfi sun maidashi chocolate, akwai rama mai yawa a tattare dashi fuskar nan babu kumari sai idanuwa da tsinin hanci, amma tsoka kam babu, Ruma tayi ajiyar zuciya ta dubi mufida wacce ta narke itama saboda tausayin wannan almajiri wanda akalla zaikai shekaru 16 zuwa 17, mufida tace almajiri ga sadakar abinci kaci sai ka samu karfin yin aikin? ta fada tana tura mai breakfast din nasu a gabanshi, dan gyara zamanshi yayi kadan sannan yace nagode, sai yaja abincin amma kafin ya faraci sai yace "ni ba almajiri bane sunana *Abdallah* inada mahaifiyata ni ba almajiri bane" da sauri Ruma tace "yi haquri dan Allah bata sani bane,
nan fa ya nutsu yayi Bismillahi ya soma cin abincin cikin nutsuwa yana jin farinciki a ranshi dan tun jiya da rana bai sake saka komai a cikinshi ba... Rumasa'u da mufida suka zuba mai ido ba komai ya burge Ruma ba sai yadda ta lura yanada nutsuwa, har yayi Bismillah sannan yakeci a nutse,, saida ya kammala sannan yayi hamdala, ba laipi ya danji karfin jikinshi ya dubi Ruma datake murmushi wanda yasa dimples dinta suka fito, ta karayin wani kyau, nagode ya furta a hankali yana fitar da murmushi shima mai kyau hancin nan ya fito zur tamkar dora shi akayi,  Allah ya saka muku da alkhairi ya albarkaci rayuwarku" Rumasa'u da mufida sun matuqar ji dadin addu'ar musamman ma Ruma... da er siriryar muryarta tace Ameen, nan da nan ya soma aikinshi na gyaran gerden din wanda bai dade da farawa ba, yayinda Rumasa'u ke kallonshi ta kasa dauke idonta a kanshi tausayinshi duk ya cika zuciyarta, mufida ce ta jata ganin lokaci na kurewa suka koma cikin school

Sharee🙏🤝
UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM

♥💍ZUCIYAR ABDALLAH♥💍Where stories live. Discover now