Page 93&94

118 12 3
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 93&94

"Don Allah ku nemi guri ku zauna,zan warware muku ruɗanin da kuke ciki"cewar Dadda

Kamar yadda Dadda ta bukata haka kowa ya zazzauna,wasun dama a zune suke wasu kuma a tsungunne,sauran ne kawai a tsaye har kafafunsu sun yi ciwo amma basu fuskance haka ba sai bayan sun zauna.

Kallon Alh.Muhammad Dadda ta yi tana cewa "Minene matsayinka a gurinta?"

"Yayanta nake, wannance mata ta,wannan kuma mijinta ne,sai kuma yaranmu"

"Ina mahaifanku suke?"

"Sun rasu tun da jimawa"

"Allah ya jikansu da rahama" kowa ya amsa da amin

Kallon mama Kareema Anwar yayi yana cewa "A kwanakin baya na tambayeki mama su waye dangin mahaifiyar Agla kika cemin kune danginta bata da wani dangi bayan ku,to ina waɗannan mutanen suka zama danginta,taya hakan ya kasance?"

"Kamar yadda Kareema ta sanar dakai Anwar haka zancen yake babu ƙarya aciki,a shekarun da suka gabata duk wanda yasan Haleema yasan cewa ƴarmu ce kuma jinin mu,mune kuma danginta,Haleema ta kasance bata da kowa sai mu kaɗai,har malam ya rasu bai faɗawa kowa asalin Haleema ba sai mu da mukasan da hakan kuma badan bayyanar waɗannan mutanen ba har mu shafe a doron kasa ba mai iya sanin hakan"

Kallon Dady tabyi tana cewa "ya ya sunanka ?"

"Muhammad"

"Tou Muhammadu, kafin na fara bada labari so nake ka fara sanar dani labarinku naji da kuma labarin abunda ya faru shekaru ashirin da biyar da suka gabata"

Shiru kowa yayi yana sauraren Dadyn jauhar wanda ya fara magana cikin harshen hausa,in birefly ya basu labarin wacece Haleemats-sadiya (Fari) har zuwa ranar ɗaurin aurenta da aka ne meta aka rasa.

Shiru su Mama Kareema suka yi suna jinjina al'amarin mussamman Inna Saude da tasan irin rashin mutunci da iskancin da ta shukawa Haleema a sheƙarun baya,amma a tunanin da take zata nemi gafararta sai su zama ƙawaye tun da dai yanzun kowa mijinta daban ba sauran kishi,da'alama mafarkinta na zama hajiya ne ya kusa tabbata shiyasa Haleema ta dawo garesu ta fuskar alkhairi.Yayin da Baffa yayi shiru yana tuna rayuwar da suka gudanar da Haleema da yadda zamansu ya kasance a baya,tabbas da badon kaddara ba da ko haɗuwa da Haleema bai kai darajar yayi ba ballantana har ta furta tana sonsa ya wofintar da ita kamar yadda ya yi a baya.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now