Page 35&36

180 28 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN* 👩‍👩‍👧‍👧
@2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*_Dr.Aysha Team_* _how market_ _wannan page naku_ _ne_ (🤣🤣😂)

*Page* 35~~36

Ta lalibo numbersa ta d'an na masa kira....har ta katse har ta katse bai daga ba ......
wani takaici ne ya ziyarci zuciyarta mara iyaka, ita daya kamar zararra take cewa " dama nasan cewa yana chan tare da tsinanniyar matarsa (ma'ana Suhailat🤣) .

Wasu hawaye ne suka wanke mata fuska yayin da d'ayar zuciyarta ke sanar da ita cewa "a'a Aysha shi d'aya yake kwance kin manta wace ce Suhailat?Kin manta halayen ta."

Wani sanyayyen murmushi ta saki tana cewa " na rantse da ubangijin daya busa mini rayuwa sai na ruguza miki farincikin ki Suhailat saina aure Aliyu domin na fiki da cewa dashi,sonsa da kaunarsa acikin jinina yake na fiki bukatarsa a rayuwa,saina mallake sa ko ta wani hali ne"
sake kiransa tayi a karo na biyu..

A bangaren Haidar kuwa,baccinsa yake sha mai dadi cike da mafalkai masu tsayawa arai da zuciya,wayarsa yaji tana ringing bai samu damar dagawa ba har ta yanke,bayan wasu yan mint aka sake kiransa cikin yanayin baccin da bai gama sakin saba ya daga wayar aransa yana mamakin wazai kirashi a wannan lokacin kuma wannan number famlinsa ne kawai ke da ita.

Wani sihirtaccen murmushi ne ya kwace mata a yayin da taga an amsa kiranta harda wani shauki ta tsinci kanta aciki a yayin da ta diba lokaci ukku da rabi saura minti biyar na dare,wannan shike nuna cewarr ba ya tare da waccan abar.

Cikin yaudararrar murya mai murya mai kashe jiki tare da sanya kasala tace "Assalamu Alaika ya habiby"

Bayan ya daga wayar ne ya d'aura a kunnensa ba tare da ya binciki number ba,muryar da tayi amfani da ita wurin yi masa sallama ta daki dodon kunnensa,hakika muryar ta ratsa gangar jikinsa yayin da tayi nasarar kara kashe masa jiki dalilin mafarkin da yayi,wannan abun yasa takara tasiri akansa amma bai nuna hakan ba illa mikewa zaune da yayi cikin mamaki,aransa yake cewa"a ina tasamu number na ?ubanwa ne yabata ita ?".
wani irin b'aci ransa ya kara yi a yayin da yatuna mafarkin da yake ta katsesa.Duk d ya gane muryar domin ba boyayya ce a garesa ba duk da yakasance ako da yaushe da wani kalan salo da take zuwar masa dashi ta hanyar lanqwashe murya da kararrayata cikin kissa,shiru ya mata baice komi ba amma ya amsa sallamar a zuciyarsa(🤣sabon salo).

Jin tayi sallama amma bai amsa ba yasa itama tayi shiru duk da tana fatan taji muryarsa ko kad'anne domin tasamu damar yin bacci cikin salama.Tsawon wani lokaci bai ce mata komi ba, ya sa tasake magana zuciyarta achinkushe tana mamakin miye dalili,muryarta tana ta tsiri akan kowa amma banda haidar d'inta "hello heartbeat kana jina ?" ta fada cikin yaudarar murya.

shirun da yaji tayi yasashi jan tsaki cikin ransa yana cewa *_CHINGOM_* kawai,yayin yayi jifa da wayar chan karshen bed d'insa ba tare ya katse kiran ba.chan side guda na bed d'in ya koma ya kwanta yana ja mata Allah ya isa na tadaa shi daga baccinsa da tayi,ayayin da chan take masa magana shiru ba amsa.

"Hello dear kana jina?plss say something dan Allah",shiru bai amsa mata ba.
"my haidar wlh ina azabtuwa da rashin jin muryar yarka! dan Allah kamun magana ko naji sanyi araina".har dai yanzun baice komi ba atunaninta,kallon wayar tayi amma ba'a katse kiran ba wannan shike nuna yana jinta,cikin narke murya ta kara cewa" pls and pls haidar kamun magana ko nasamu yin bacci cikin salama wlh zuciyana zafi take na rashin jin ganin ka, kunnuwana na mararin jin sautinka suke,idanuna ciwo suke na rashin tozali da kai,hancina kewar kamshinka yake yayin da gangar jikina take jin kamar ace kana kusa da ita.

Duk wannan zubar da takeyi har yanzu bataji yace mata kanzil ba (ko numfashinsa ba taji ba amma hankalinta bai kai ga hakan ba ta lula duniyar masoya🤣).

My dear Haidar Dan Allah kace wani abu mana,dagaske nakeyi *ina sonka* na mallaka ma zuciyata da gangar jikina, plss ko na minti biyu kace min biyu ne kace mun wani abu wlh ina kishin muryarka.
Yanzu kam shirun nasa ya kular da zuciyarta a yayin da kuma ta kasa jin haushinsa, sai tunaninta da karkata kan cewa Suhailat ce ta daga kiran ba Haidar ba,cikin bakin cikin tuanin da yazo cikin ranta ta cillar da wayar itama ba tare da ta yanke kiran ba tafada jicce tana zubar da hawayen kishi (tofah wata sabuwa inji y'an chacha)tana k'ara daukar alwashi a kan Suhailat tare da tsanarta dake kara lunkuwa cikin zuciyarta,take sosai tanaji ajikinta zata iya rasa rayuwarta idan bata samu Haidar ba dimin shine muradin zuciyarta da rayuwarta,adadin kwallar dak fita tu daga zuciyarta izuwa idaniyar ta wadanda ke zubar da anbaliyar hawaye suke adadin kiyayya da tsanar Suhailat da kuma soyayyar Haidar dake lunkuwa adukkan zuciyarta da rassanta.

Haidar kuwa ya katsa komawa baccinsa juyi kawai yake yi bisa makeken gadonsa da ya gaji da juyin ne ya mike ya shiga bathroom ya watsa ruwa,bayan ya fito ya saka white jallabiya ya nufi wani corridor mai kyau design dinta kamar masallaci ga qur'an nan masu yawa d littafai nan kala kala na musulunci agefe,bisa shinfidadd'iyar dardumar dake gurin ya hau ya kabbarta sallar nafila,sai da aka kira subhi ya sallace ta sannan bacci ya dauke sa yana karatun Al-qur'ani mai girma.

Bangaren Suhailat kuwa.........✍️✍️✍️

*Zeesardaunerh ce*

( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*Comment and vote d'inku suke* *karamin karfin guiwar typing*💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now