Page 81&82

88 17 4
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 81&82

Da idanuwa Aleeya ta bishi domin sam bata fahimci wane yare yake ba

"Why are you looking me like that? Let's go idan ba haka ba nayi tafiyata na barki,you know what will be the end,bazaki samu abun hawa ba"

Dakatar dashi tayi tana cewa
"I'm sorry ka yi misunderstanding banice wacce kake nema ba "

Murmushi yayi yana cewa "Lil sis please don't waste my time,i wan't to go somewhere"

"Ba ka jin hausa ne,baka ji abun da nace maka ba"

"Common Amna stop joking, please ki wuce mu tafi" a zuciyarta tace "Amna again a Abujar ma? Hmm to ita hala a gari nawa take zama,no wonder shima ya zata nice ita" a fili sai tace masa  "Sorry i'm not Amna my name is Aleeya;zaka iya bincika wacce kake nema a ciki" ta ƙarisa tare da barin gurin.
  Binta da kallo yayi sai yanzu ya fahimci tabbas ba Amna bace,gabaɗaya ya rikice ne saboda saurin da yake,sam baby Amna bata saka long hijab sannan ma bata cika saka hijab ba idan zata fita sai dai sallah kawai,but wacece wannan da take tsananin kama da cutie? ko dai itace takeson ta raina masa hankali don ta saka hijab,ta gani ko zai ganeta ? Bin bayan Aleeya ya yi yana kiran sunanta amma wayam bai ganta ba.

  Tsaye ya yi tare da saka hannuwansa ya rike kunkuminsa kamar mace "WHO IS SHE"

"Who are you talking about ya Amar?" yaji sautin muryar Amna a bayansa,cikin hanzari ya juyo yana kallonta;sanye take cikin Abaya ash colour,ta yafa gyalen abayar ta rataya jaka itama ash colour kamar yadda takalmanta suke ash.Kallonta yake cikin mamaki ya kuma juya ya kalli direction ɗin da Aleeya tabi,at all ba ma hanya guda suka bi ba,that means they are diffrent.

"Me kake kallo ne ƙaramin yayana kuma abokina.." ta faɗa cikin raha da annashuwar da take ji tun daga zuciyarta

"Shine kika sakani zaman jiranki ko?"

"I'm sorry dear,nasan na maka laifi that's why ina fitowa na biya shop na siya maka your fav sweet"

"Ga ƙaramin yaro ko? Sweet ɗin da kika siyomun itace zata hana na miki korafi.."

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now