Page 77&78

120 14 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 77&78

Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarci Umman Khaleel,wanda ya haddasa mata suma a tsaye;cikin mamaki da kuma matsanancin tsoro take kallon mijinta,wai itace yau Abban khaleel yake yiwa tsawa? Mi yake damunsa ne? Hakan bata taɓa faruwa tsakaninsu ba fiye da shekara biyar da aurensu;mi yake shirin faruwa ne ?

Cikin tattausan lafazi tace  "Wa ya taɓamin gwarzon mijina,har ya saka ransa ɓaci haka"

Kamar wani mayunwacin zaki ya taso mata "Ki fita nace bana bukatar jin muryarki.."

Da gudu ta fita daga cikin ɗakin domin ba ƙaramar tsorata tayi ba da yanayinsa,a yadda yake tabbas zai iya aikata koma miye

"Innalillahi wa inna illaihi raji'un" ta samu damar faɗa a lokacin da takai tsakiyar palonta,zaune tayi a kasa ta rasa wane tunani zata yi.
   Tun wayewar safiyar yau takejin yawan faɗuwar gaba,jikinta ma duk a sanyaye, mike shirin faruwa da rayuwarsu ne? Mike damun sahibinta?

Waɗannan sune tambayoyin da suka yiwa zuciyarta ƙawanya,yadda taga safiyar yau haka taga daren,idanuwanta sunyi hulu_hulu,sunyi ja kamar Gauta,duk wanda ya ganta yasan ta kwana kuka kuma bata samu bacci ba.

   A bangaren Abban Khaleel ma bai yi bacci ba,haka ya kwana da matsanancin ciwon kai mara iyaka yayin da zuciyarsa ta cunkushe ya rasa mi ke masa daɗi hakama nutsuwarsa.

   Kiran Sallar farko a kunnuwansa aka yi shi amma ko kaɗan ya kasa tashi,sai da rana ra fito sannan ya haɗa har na jiya da bai yi ba.

Har misalin karfe goma sha biyu yana cikin ɗaki batare da ya saka komi a cikinsa ba,hakama Umman Khaleel,yau da safe ma da taje gurinsa kai masa abun ƙari korar kare yayi mata, hakan ya haddasa mata zazzaɓi mai tsanani.Su Khaleel ma dakyar sukayi breakfast,sai da ta musu karyar Abbansu yayi tafiya tun jiya sannan suka saka wani abu a cikinsu suka tafi makaranta a adaidaita sahu,bayan ta tabbatar da sun shiga makaranta sannan ta dawo gida.

"Hanne kenan,meyasa kike son jin labarin gidana?"

"Ki fara bani bayani ƴata sannan na faɗamiki daddaɗan labari.."

"Bansan wane irin labari kike tafe dashi ba,amma dai yanayin gidan namu a yau sai a slow,gidan ya zama so silent,gabaɗaya yinin yau ban saka tsuntsayen biyu a idanuna ba"

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now