Page 17&18

121 14 0
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 17&18

Dukkan su basarwa sukayi kamar basu ganta ba amma Abu daya ke yawo a zukatansu mamakin zuwan nata gidan domin ta jima rabonta da gidan kila since auren Zaki da Suhailat.

Bisa daya daga cikin luntsuma_luntsuman kujerun da ke cikin dakin ya zauna Ummiey ta zauna kusa dashi ya dora kansa a kafadunta,dauke idanuwanta daga kansu Amna tayi domin wannan ba sabon abu bane,yadda ya yi da cute face dinsa da yanayin yadda yake wa Ummiey magana ya kara narkar da Ayshert .

Ciki yauki da karyar da murya take masa sannu da zuwa ya yi kamar bai jita ba saida Ummiey tace masa "Zakina baka ji ba ana greeting dinka"

Sannan ya dago kyawawan idanuwansa masu kama da na Ummiey ya dubeta yana cewa "banji bane"

Ganin ko kanzil Ummiey bata ce mata ba ga kayan haushi da idanuwanta ke ganar mata sai wani yauki Ayshert ke yi don ta burge Haidar,mikewa tayi ta wuce part dinta domin ta watsa ruwa ya Amar ma tun shigowarsu yayi part dinsa.

Haduwar part din Amna baa magana,bakaramin kyau palourn ta yayi ba komi fari har tiles ya yin da furnitures suka kasance red even bedroom hakane,dakin bai cika ado dayawa kamar turai,kai da gani naira tayi kuka anan.

Tube kayan jikinta tayi ta daura towel tanufi wata hanya nan cikin dakin nata wasu numbers ta saka sai gashi gurin ya bude ta shiga,girman bathroom din kamar wani palour,gurin wankan ma abun burgewa ne glass din wurin ta buda ta shiga duk yadda zan misilta muku yadda haduwa da tsaruwar toilet din b'ata lokaci ne,nima mai rubutun banda bathroom na Haidar ban taba ganin irin wannan bathroom na Amna ba, fitowa nayi domin na bata dama ta watsa ruwa cigaba da karewa part din Amna kallo nayi komi dai_dai abun burgewa wani room dake kusa sosai da bedroom dinta na nufa cikin sa'a na murda handle din naji ya bude teddies kala_kala idanuwana sukayi tozali dasu kamar shop masu matukar kyau da daukar hankali,cikin takatsantsan na saka hannuna na dauko guda wani laushi ne naji time din da na tab'ata sunan Companyn dake manufacturing nasu na duba sai naga A.M.A wasu kuma H.H.A, kama kallon teddyn nayi kamar na tafi da ita,bansan adadin time din da na kwashe cikin dakin ba saida naji muryar ya Amar daga chan palour yana kiran Amna,cikin sanda na shiga dakin nata ina mamakin meya hana fitowa? sallah na risketa tanayi na tsaya gefe,ya Amar ma da ya shigo bayan yayi nooking yaji shiru, ganin sallah take yace.."idan kin gama Ummiey tace ki fito kici abinci" ya juya ya fita.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now