Page 67&68

99 17 15
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 67&68

Yawo ta rinƙa yi da idanuwanta a office ɗin amma bata ga likitan da aka turo ta gurinsa ba,idan har shine likitan gaskiya bazata bari ya dubata ba kallonsa tayi shima har yanzun ita yaje kallo ya ga shin zata shigo ne ko a'a.
  Sakin handle ɗin kofar ta yi tana komawa baya tare da fita daga office ɗin baki ɗaya.

"yadai har kin ga likitan ne?"

"a'a"

"meyasa?"

"banga kowa aciki ba"

"kamar ya baki ga kowa ba?"
tafiya Aleeya ta fara batace komi ba

"mu yiwa likatan da ya ce ki shiga magana,ko na kira Abba ne?"

"a'a ! barshi kawai,dama bana da bukatar ganin likita"

"but Abba ne yace fa.."

"please kibar maganar kawai,don Allah"

"ok badamuwa,muje gida"

Kiler smile ya yi lokacin da yaga ta koma,dama kuma yayi tunanin hakan,a hankali ya furta "kina da muhimmancin da yasa na ke son nasan asalin ke wace" ya ƙarisa ya na jawo file ɗinta,file ɗin da suka sha wahalar neman Umaymah akansa,file ɗin da ya bata masu lokaci rashinsa kuma ya dagula lissafinsa,yanzu ga file ɗin a hospital ɗinsa,office ɗinsa kuma agabansa,tabbas komi da lokacinsa duk saurinka da dagiyarka baka isa ka aiwatar da abu ba matukar lokacinsa bai yi ba.

Ɓuɗa file ɗin ya yi tare da sauke idanuwansa a full name ɗinta,kallon sunan ya yi na wani lokaci, ALEEYA YUSUF MUHAMMAD

Ya maimaita sunan ya fi a kirga ,number mahaifinta ya yi copying tare da saving ɗinta a wayarsa da sunan da ya gani a file ɗin,YUSUF MUHAMMAD
address dinta ya duba,yana tunanin tin da yake bai taɓa jin sunan wannan  Unguwar ba wai MABERA
(kuji iskanci😂)

°°°°°°°°°°°°°

KABEER

Sai da ya ɓari hankalin Ummu ya ɗauko sannan ya samu ya fita daga gidan,direct gidansu Aleeya ya nufa.

Sosai gidan ya sauya masa saboda gyare_gyaren da akayi masa,yaro ya samu a wajen ya tura sa yace ace ana sallama da Aleeya.

Lokacin da yaron yaje inna Saude na madafa ta ɗaura girki ya yin da Salmat ke zaune tsakar gidan tana yankan salatif ɗin da zata yi lalle dashi.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now