Page 65&66

89 17 7
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
Page 65&66

Shiru Aleeya tayi batare da ta bashi amsa ba, a zuciyarta tana cewa lallaima mutumin nan so yake ya raina mata hankali,idan ba renin hankali ba wa yake bibiyar wani acikinsu ,kara murde hanunta yayi sai da ta ƙara yin ƙara "WACECE KE ?"

"bakowa bace ni face mutum kamar kowa"

"nasan cewa ke mutum ce amma ba kamar kowa ba,who are you? "

"kai ya kamata na yiwa wannan tambayar,kai waye kuma meyasa kake bibiyata? amma duk ban yi hakan ba"

"because? "

"abu mai muhimmanci ake damuwa da a san shi, a wancan lokacin ma na gaya maka hakan da kayi kuskurene, har na baka hakurin marin da na maka amma a wannan lokacin sam baka canci a baka hakuri ba"

"su waye suka turo ki?"

"ban fahimta ba !"

"ai baza ki fahimta ba,wa kike wa aiki ? "

" zaka iya bincikawa da kanka,don Allah idan badamuwa zaka iya sake mun hannu,ina da abun yi"

Shiru yayi without sayin anything kuma bai saki hannu nata ba amma ya ɗauke kansa daga shoulder ɗinta,he's thinking wacece ita da har take masa magana haka,da wa take taƙama?,su wadanda suka turo ta basu sanar da ita wanene shi ba?

ƙira ne ya shigo wayarsa,sassauta rikon da ya yi mata yayi tare da ɗaukar wayar "hello Abdallah "

Tana jin ya sassauta mugun rikon da yayi mata ta fisge hannunta cikin sa'a ta samu hannuwan nasu suka rabu,fisgar hannun nata da tayi ya saka shi kallonta,dama a kufule take dashi tana samun sa'ar fincike hannunta ta juyo tana kallonsa,shima kallon nata yake yana karantar fuskarta

"kayi na farko,kayi na biyu,to kasani this is the end,idan har ka sake yunkurin kai hannunka a likab ɗina ko hannuna ka tabbatar da cewa kotun musulunci ce zata raba mu" tana kammala faɗin hakan ta juya tabar gurin

bin bayanta yayi da kallo na ɗan wani lokaci

"Hello...A.M kana jina"

"ina jinka"

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now