Page 41&42

156 18 4
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 41&42

Duk yadda naso na share wadannan tunanukan abun ya ćutura sai kai da komo wadannan tambayoyin ke yi a cikin zuciyata

Lokacin da muka isa gida ana kiran sallar magrib,mota biyu ne suka zo d’aukar mu,motar Abban Ramlat sai ta yaya Anwar ; Baffa,mama Kareema da mama Yelwa motar Abban Ramlat suka shiga,ni da Ramlat wacce yaya Anwar yazo da ita sai Abokinsa muka shiga motarsa.

Ko da muka shiga gidan suna alwala,Salmat na jin sallamarmu ta rugo a guje tana mana  oyoyo ta rungumeni “oyoyo-oyoyo  oyoyo Adda Aleeya “ hakan kawai take ta fada,Dadda baki yaki rufuwa ta janyoni kusa da ita kamar ance mata tafiya zanyi na barta.

Tabarma aka shimfida muna ya yin da Baffa suka fara alwala domin zuwa masallaci,Inna Saude ma tayi farincikin ganina ko a fuskarta naga hakan.

Bayan munyi sallar magrib na watsa ruwa na dawo gurin Dadda na zauna,sai nan da nan Inna Saude ke yi dani abun har ban mamaki,Salmat ta rasa gurin da zata sakani tsabagen farin ciki,har ce mun take “Adda gidan nan har haske ya kara saboda dawowarki cikin sa amma da bakya nan komai sai ya yi baki ya yi duhu,gidan ma ya koma kamar gidan makoki “

“kai salamatun Inna banda karya “

“Allah Adda Aleeya,ko gidan nan ma yasan bakya nan don kawai baya magana ne da sai ya fada “

“naji amma ban yarda ba,ai yanzu na dawo shikenan “

“Inshaallah Adda,bana fatar ki sake tafiya ki bar gidan nan ko na kwana daya ne matukar batare nake dake ba”

“Inshaallah kanwata ina tare dake a ko’ina nake,ki saka hakan a ranki”

Gidan namu na kalla sai nake ganin kamar an sauya shi

Bayan sallar Isha’i su Baffa suka shigo gidan,babban carpet Inna Saude ta shinfid’a musu,takai musu abinci da ruwa
Kamar almara haka na kalli kulolin da inna ta sakawa Baffa abinci acikinsu abunda har na manta rabon da naga abincin Baffanmu a kula sai dai a langa ko tasa.

Mamaki bai kara kamani ba sai da naga Innarmu ta jeramun abinci kusan kala ukku a gabana tana tambayar wane zanci aciki a zubamin fuskarta dauke da murmushi wacce kwan lantarki ya haska,kallonta nayi nakasa cewa komi

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now