page 71&72

198 23 5
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

Page 71~~72

"Antynmu gida za'aje ne,to bissmillah ku shigo na kaiku"

kallon juna naga su Salmat sunyi suna murmushi tare da yin magana kasa_kasa.

cikin dan hanzari nace,
"a'a wlh mungode"
kafin na rufe baki naga Salmat ta antaya mota tana cewa,

"Yawwa gsky ka kyauta,tun dazu ma muke nan bamu samu napep ba gashi dare yayi,nifa ma kazama yaya na daga yau tunda ka ragemin  hanya"
tsaye nayi tamkar wacce aka dasa ji nake kamar in tuma in shako Salmat domin yaseen iskacin ta ya fara tukeni,kafin in ce wani abu naji tana cewa su Batul su shigo ciki dan nan ma suga gidanmu tunda yayansu ne sai ya dawo da su.

    Kamar jira suke suka antaya bayan mota harda Ramlat batare da Izinin yayan nasu ba tunda ga uwarsa Salamatu ta basu umurni.

Nama rasa yarda zanyi ina tsaye ji nake kamar wadda aka sanyayawa kafafu Batul ta dubeni cikin murmushi tace,

"Shigo mana Antynmu ke daya ake jira "
cikin karfin hali nace,
"Aa Batul ku tafi kawai naga ba wuri ni bara na hau napep"

"Amma dai Adda Agla idanunki sun koma irin na inna ko?"

Kallonta nayi cikin mamakin maganarta

"eh mana idan ba haka ba ga kujera guda daya chan gaba muka bar miki zakice babu wuri sai kin haw napep?to dai Allah da kansa ya hana almubazzaranci ehhe"

Dariya kowa yayi ni kuma naja kafafuwana nashiga gaban motar araina ina raya irin hukuncin da zanyiwa Salmat.

Bamuyi nisa da tafiyar ba ya yi parking a wani mall STOP AND SHOP yace mubashi minti biyar yanzu zai dawo.

Salmat ta dubi Fatima tace

"wai ni kuwa Faty na tambaiki"

"eh,inajinki"

"wannan wurin da yayanku ya shiga ina ne hala?naga mutane sai shiga suke,ko da yake nima yanzu yayana ne"

"Oh wurin shopping ne inda ake siyar da kayan makulashe kala kala harda su chocolate"

"toh yanzu mu zaiyi yiwa shopping din"

"Ohho kila"

" ko kuma Antynmu ba"
Cewar Batul tana murmushi

"ai ko muma yaseen sai ya yi muna kuzo mu bishi ciki kowa ya dauki abunda yake so"

"Salma fa zai iya yi muna fada Allah"cewar Fatima

"ba gani ba,zan tare muku "

"ya yi kyau boss,to idan aka samu akasi kema ya hada dake fah "

"Ah to ga Adda nan,tunda antynsa ce sai ta bashi hakuri"

"hakanma za'ayi"
Cewar Batul

Ina kallonsu suka shiga mall din bayan kamar mintin 30 suka fito a tare suka shiga motar ya tada muka cigaba da tafiya.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now