Page 73&74

78 13 10
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 73&74

"ALEEYA TA MUTU" Kamar saukar aradu haka wannan kalmar ta ɗira a cikin kunnuwansa wanda hakan ya sakasa suman zaune,ji da ganinsa suka ɗauke na tsawon lokaci mai tsayi har hakan ya tsoratar da su Ummu.Ita kanta Ummu da taji maganar Inna Saude sai da mamakinta ya cikata,jijjiga Kabeer take tana kiran sunansa amma baya motsi,idanuwansa sun ƙafe gurin kallon Inna Saude yayin da numfashinsa ya ɗauke zuciyarsa ta ɗaina bugawa,Ummu ɗuk ta rikice sai faɗa take yiwa Inna Sauɗe,Inna Saude ita kanta ta tsorata da halin da Kabeer ya shiga amma batajin zata sare ga abunda take kokarin aikatawa, domin hakanne kawai mafitar da ta rage, shiyasa bata mayar da hankali gurin surutun da Ummu take ba burinta kawai Kabeer ya farka basai an kaisa Asibiti ba,hakan ne zai bata damar kammalar da aikin da ta fara domin bata da isashshen lokaci.

Ƙarar da Ummu tayi tana kiran sunan Kabeer ya saka Inna dije lekawa ta ta ga domin taga abunda ke faruwa,lokacin da taga Kabeer a zaune idanuwa sun ƙakƙafe ba ƙaramin farinciki bane ya cika zuciyarta,addu'a take Allah yasa mutuwa ya yi da tafi kowa farinciki,watakil har azumi uku sai tayi tsabagen murnar hakan,kallonsu kawai take suna kelaya mai ruwan sanyi amma ya ki motsawa,ƙanƙara taga Inna Sauɗe ta ɗauko ta nufo gurin da Kabeer yake ko miye zasu yi da ita oho,wata irin ɗariya ce tazo mata sai da tayi sauri ta toshe bakinta,da taga dariyar ba tsayawa zata yi ba ta juya izuwa ɗakinta tana kyalkyala abarta.

"Sauɗe sai da na faɗa miki komi ba abunda na ɓoye miki amma dubi abunda kika sakamun dashi,na rasa gane ki ɗin masoyiyar muce ko maƙiyiyarmu,ku da kanku kuka ce mu fita daga rayuwarku kuma muka fita don Allah nima ina rokonki ki fita daga rayuwata da ta ɗana,bana bukatar taimakon naki ko kaɗan,na dogara da Allah shine zai yaye masa" waɗannan sune ire-iren maganganun da Ummu ke yi,gabaɗaya itama tana kokarin fita daga hayyacinta,ko kulata Inna Saude bata yi ba ta saka ƙanƙarar acikin ruwan sanyin sai da fara narkewa ta ɗaura sauran a saman kirjinsa ta dannata,ruwan sanyin kuma ta kelaya masa su tun daga fuskar sa har zuwa kirjinsa,wani irin numfashi da sheɗa yaja kamar wanda rayuwarsa zata tsaya,a hankali suka ga idanuwansa na kyaftawa,wata irin ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke ganin ya fara motsi.

Daƙatawa Ummu tayi daga kokarin kiran Abbansa da take ta nufi ɗanta da gudu tana tattaɓasa tare da tambayarsa yana lafiya,shiru ya yi mata yana bin kowa da idanuwa "kamun magana Muhammad ina bukatar jin muryarka da lafiyarka,ko suna nane ka kira ka ji"

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now