page 59&60

198 25 3
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

*Page* 59~~60

Amma ba mai bashi amsar wannan tambayar.

   Cikin bacin ran da Maryama ta dasa masa ya nufi hanyar gidan su dake Runjin Sambo saman mashin ɗinsa.

      Yana chan yana tuna ni ba tare da ya lura ba kuma baisan ya akayi ba ji kawai ya yi mashin ɗinsa ya ɗan bugi mutum sai karar matashiyar budurwar da yaji ta kwalla kara tana kiran Adda...!

Yau Assabar mun tashi da murnar zuwa gidan mama Kareema da zamu yi,shiri muke cikin farin ciki da annashuwa ya yin da inna Saude sai cin magani take tace baza muje ba Baffa ya ce zuwa ba fashi,

"Haba malam taya zakace sutafi bayan nace a'a to aikin gidan waye zai yi ne"inji inna Saude cikin bacin rai

"dama hala wa ke aikin gidan lokacin da basunan?ko kuwa sune matar gidan"

"ko daya,amma ƴaƴana ne kuma idan ban koya musu ba ai ni za'a zaga idan sukayi aure"

"Naji duk zancenki amma zuwan su ba fashi tunda ita kanta Kareemar ta bukaci hakan.watan su nawa rabon su da chan da har zaki ce baza suje ba ko kuwa don ke bakya zuwa shine zaki hana musu zuwa? ki hana musu zumunci da y'an uwana"

Wani kololon haushi ya turnike inna saude jin abinda yace,

"Tanan kuma ka ɓullo malam,la'ilaha illalahu muhammadurasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama tafada tana rike haba,ni ban hana ɗiyanka zuwa gidan kanwar ka ba cewa nayi baza suje yau din ba domin inada aikin da nake son suyi min,sannan kana batun ba xuwa inda Kareema koh?to idan naje inyi mi,idan har ita bazata zo gidana ba ni ba inda zanje umhmm "

"Allah ya shiryaki Saude, zuwa kam sun gama yi nai kuma ba yini ba har kwana biyu za suyi sai attanin idan sun dawo daga makaranta sai su wuto nan kinji"

"Ameeeeeeeeeen malam,waye ne bai bukatar shirin Allah aikowa komi hankalinsa yana bukatar wannan ehhe,sannan kuma inada tambaya shin wai hala so kake hayaki ya kashe min glas din ido ne kaje ka auro wata?
   in ba haka ba haka ba taya zaka tashi ka turamun yara wani wuri wai suyi kwana biyu"
tafada ciki. Masifa da jidalin da ke cinta kuma ga haushin mama Kareema na kuɗin da ya bata amma ita da ke matarsa bai bata komi ba,kuɗin su _AGLA_ da ta kwallafa rai ɗan iskan barawo ya santale ya tsere.

   Ko cikan ki Baffa bai ce mata ba illa fita batunta da ya yi ya zauna bisa tabarmar da na shinfida masa ya kara sautin redion inna Saude wanda take saurara yana sauraren *_Sakkwatawa kwallahiya daga Vision FM radio_* ya lura  fitarnar ta ta ce ta motsa da sassafen nan.

Shirun na Baffa ya kara kular da inna Saude,

"Ni fa na lura tunda bawan Allah nan ya baka kuɗi ka chanzamin kana wani shareni don kaji taro da sisi na shiga aljihunka to bara kaji wlh,duk wacce ta shigo gidan nan sai tafita da kafafunta domin wannan gidan na Saude ne ba yadda ka iya dani ehhe yadda na hakura na zauna dakai lokacin da babu  kaina hakannne yanzu zakayi hakuri ka zauna dani ba yadda ka iya wlh"

Ta wuce ta bubbuttai,

"ni Saude naci dubu sai ceto ba yadda mutum ya iya dani sai hakuri "

Abun ma dariya ya koma ba Baffa amma ys gimtse ya yin da inna Saude zuba kawai take kamar y'a'an ƙanya,Salmat kam sai da ta dara sosai,taso ta tankawa inna Saude amma tana gudun ta kara harzukata taci gidansu amma da farko har gabanta ya fadi da inna taso ta hana da ga baya kuma abun na mahaifiyarta ya koma bata dariya.

     Nidai aikina kawai na cigaba da yi ina da sabo munsaba da halin inna duk da ta rage kwanakin nan,naji daɗi da zamu yi kwana biyu wurin mama amma ina rokon Allah ya sa yah Anwar ba yanan har mu dawo.

Duk abinda zamuyi mun kammala ko da sha biyu tayi mun gama shiryawa muka yiwa inna sai an jima ciki_ciki ta amsa dama Baffa ya bamu kuɗin adai_adaita na saka liqab dina muka dau hanya sai RUNJIN SAMBO

Mai adai_adaitan baishiga da mu cikin kwanar gidan mama Kareema ba yace gaskiya shi anan bakin hanya zai sauke mu,har Salmat taso ta tsaya jayayya da shi na hanata domin da'alama mutumin ba yada kirki irin samarin nan ne na zamani.

  Haushin hanata chachar bakin da nayi da mai napep din yasa tayi tafiyarta bata jirani ba.

Bayan na sallami mai napep na biyo bayanta ina mata magana amma taki saurarena kawai jinayi  mashin ya bugeni da kafa tare da karar Salmat tana cewa,

"Adda.........✍️✍️✍️

Zeesardaunerh ce

          ( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now