Page 79&80

133 11 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 79&80

"Bazaka mutu ba Kabeer,zaka rayu a cikin a halinka kamar yadda muke a baya,zaka rayu har ka sakawa ƴarka da zaka haifa suna Aleeya"

  Shiru Doctor Abdallah ya yi yana saurarensu,tun sa'adda yaji sunan Aleeya ya bisu da kallo tare da kasa kunne yana saurarensu,jikinsa yana bashi ko dai Aleeya patient ɗinsa suke magana amma ai ita tana raye.

Kammala checking patient ɗinsa ya yi tare da ƙarasawa gaɗon da Kabeer yake shima checking ɗinsa ya yi tare da duba sunan da ke ƙaramin katinsa wanda ya ƙarba a wajen Ummu.

Bayan ya kammala duba  patient ɗin da zai duba a emergencyn ya fito,har ya kawo bakin kofar fita wasu yara ko nace ƴan mata biyu suka tsayar dashi suna tambayarshi inane mara lafiya suke? Tambayarsu ya yi wa suke nema suka gayamasa  "Ku shiga ciki sai kuyi left side yana nan a gado na biyar"

"Mun gode" har sun fara tafiya ya dakatar dasu

"Sorry na tsayar daku,amma ku twins ne ko?"

"Eh"

"Yaya sunanku"

"Fatima ni kuma Batul"

"Nice name"

"Thanks"

"I wan't to ask one more question,don Allah wacece Aleeya? "

Wani irin kallo suka bishi dashi

"Sorry ban muku introducing ɗin kaina ba,ni likitan Kabeer ne inason sanin bayanai akanta ne domin nasan yadda zan shawo kan matsalarsa"

"Ok badamuwa,amma ina ganin ba fa'idar hakan domin bata raye !"

"Nasan da hakan"

Yanzun ma kallonsa suka sake yi da mamaki

"Da yayanku naji"

"Ok"

Kallon Batul ya yi domin ya ga fuskarta tafi sakewa da'alama kuma zatayi surutu yace mata

"Ku ƙarasa ciki kuga jikin nasa,in yaso in anjima ko gobe idan na samu time sai muyi maganar"

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now