Page 5&6

375 46 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔

     *page* 5~~6

    Itace tadauka tasaka cikin murhu ta fara hasa wuta domin daura sanwar tuwon, yayinda inna Saude Ta shige daki abunta.
 

   Da cups  ya fara cin karo daga shigarsa cikin gidan na shi.........
   ko ina a hargitse yake chan kayan wanke- wanke ne tsulii guda ba'a wanke ba,
      Kayan wanki ma duk a yashe suke,
Ga poo chan Maleek Yayi kashi bata zubda ba...

      Wani kololon bakin cikine ya to kare masa wuya alokacin da ya shiga palon da ko arzikin shara bai samu ba.
            Zaune take bisa karfet tana karatun littafan hausa da ta saba yi .
Ya yi sallama har sau ukku kafin ta amsa domin hankalinta ya tafi a karatun littafin da take.......

               "Abban Khaleel Nidai gaskiya ka rage yi min wannan kallon na kuriila haba kamar na chanxa maka" cewar Azeema Kenan ya yin da take turo bakin ta cikin dan shagwaba,yanda takeyi baza kace ta haifi yara biyu ba.
   " Soory dear baxan kara ba kinjiii" cewar Abban Khalil,
"ok najii kar ka sake, ko jiya haka kace baza ka koma ba amma gashi yanxu ka sake yiii"
" Ai kedin ta da ban ce shiyasa ako da yaushe bana gajiya da kallanki, dear ko da yaushe kara zama yarinya kike kamar ba kece kika haifi khaleel Da khaleela ba".

"Ohho yanxu na fahimceka dear"
   "Kamar ya dai Umman Khaleel"?? Ya fada cikin sigar tambaya.

"Eh mana ai na fahimce so kake na tsufa ka kawomin wata .." tafada tana bata fuska Alamu bataji dadi baa.

    "Sorry ba haka nake nufi ba dear, ai daga ke ba karii, kece Uwar gidana kuma Amaryata inshaallah ."

   "Humm Abban Khaleel karkasa na sakankance da zantukanka rana tsaka najii kace Aure zaka karaaa nidai abar maganar kawaii "

" Najii amma kesan irin tarin san da nake miki ko??
Kina ganin cewa akwai wani gurbi A zuciyata bayan nakiii ?
Ke kadaice muradin zuciyata, ban rasa komii a wajenki ba to karin aure namii?
Kisa a ranki ni Abubakar Na kine ke kadaiii har abadaaa.

   Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, ya yin da ta afka cikin kogin tunani....

Shiyasa a koda yaushe take alphari da jarumii kuma gwarzon sahibintaaa,shi tafara so a duniya kuma har karshen rayuwarta hakanne da yardar Allah.

    A duniya bata tantamar kaunar da Abban Khaleel Ke mata, shiyasa bata sama ranta cewa ita kad'ai zata zauna dashi ba kamar yadda *WASU MATAN*  Keyi idan suga miji na son su sosai.

      Tasan cewa Aure lokaci gare shi kuma muddin na Miji ya yi niyar kara Aure to ba fashi sai wani ikon Allah.

  Guiwar ta tana sanyi ne a duk lokacin da ta tuna cewa Uwar Mijinta ba son ta ta take yi ba.

         Bawai tana tsoron kishiya bane,a'a tana dai tsoron Abunda zai rabata da Mijinta Abun Alfaharin ta.
         A Wannan zamanin da muke ciki da mutane ba tsoron Allah a zukatan su, bata san wace za'a kawo mata ba.

     Tasan halin *WASU MATAN* ba Imani gare su ba shiyasa take jin tsoro.

   " Hmmmmmm" ta sauke gwairon numfashi."
       "Ina sanka fiye da kaina Mijina"," haka ne nima ina sanki sosai Umman Khaleel Ya fada yana k'waik'wayon muryarta. "

     Gidan Mallam Abubakar Kenan shida matarsa kuma y'ar uwar sa Azeema Tare da  y'ay'an su twins  Khaleel da Khaleela.

   Rayuwar su suke cikin farin ciki da kaunar junansu.

     Mallam Abubakar Wanda yakasance d'a ne ga limamin Unguwar Mallam Usman.

   Mallam Usman Yana da Mata biyu Y'ay'a biyar Hawwa'u Da Hadiza  Sune Matansa.Inda Hawwa'u Keda Y'ay'a hudu duk mata. Aisha,Fatima,Firdausi,Fareeda , inda suke kiranta da Mama.
Itako Hadiza d'a d'aya Allah ya bata Abubakar, suna kiranta da umma.

   Mama ta kasance mutum mai hakuri da kawaici ,Umma kuwa masifaffiyar mace ce ta bugawa da jareeda ga shegen kishin tsiya .
 
     Allah bai had'a jinin ta da na maman Azeema ba, dan kawai suna mugun shiri da mama.Itako ana ta tunanin duk mai son mama mak'iyin ta ne.

    Malam Abubakar  Mallamin Islamiyya ne  acikin unguwar su Aleeya Mabera A Garin Sokoto.
Ya kasance  d'an uwa ne ga Azeeema.
  Yan zu haka shekarar su biyar da Aure da Azeema Kawar Aleeya; Kuma ya kasance shi ke karba musu hadda a Islamiyya.

       Tawannan hanyar ne soyayya mai zafi ta kullu tsakanin sa da k'anwar shi  Azeema har ya kai ga sunyi aure Allah ya albarkace su da y'ay'a biyu, yanxu haka shakarar yaran hudu da  watanniii .

Rayuwar Gidan abun burge wa ce ga kowa domin zallar soyyayya suke shinfidawa a cikin gidansuu.

     Matsala dayace suke fuskanta  Arayuwar Auren su;wannan matsala kuwa itace k'iyayyar da Ummarsa ke wa Azeema Tayi yawa bata san Azeema Ko kad'an; dan k'awai  takasance y'ar aminiyar mama.

    Da Mahaifinsa da Mahaifin Azeema Uwar su d'aya ubansu d'aya; su yan Asalin garin sakkwato ne (A karamar hukumar wurno ).

      A lokacin da Umma ta matsa masa ya fidda mata yayi Aure bai dace ya zauna haka ba tunda ya Kammala Digree dinsa a fannin computer,kuma yana Koyar Wa a Islamiyya yana samun abunda ke shigo masa; "yace mata ai Azeema ce zabinsa"," fada ta dingayi ba ka'kk'autawa, a duk cikin y'ay'an abokannan ta dake sansa baza yazabi wata cikin su ya aura ba sai yace wai sai Azeema ba Azeema ba wallah uwarta ita da ta haifeta. "Dallah tashi ka bani guriii dan neman shanyayye kawai an wanke an baka ka ka shanye dan anga kai d'aya ne gareni,to bara a bid'i hanyar ra bani da kai"," tasss ta masa tare da ce wa kar ta sake jin maganar".

     Mama na jinsu ko k'ala ba ta ce ba ta sa musu i'do kuma ta hana ya'yan ta tank'awa musamman Aisha Uwar jidali.

              Ha kuwa a kayi Abubakar bai k'ara tada maganar ba sai da ummansa tayi tapiya, bayan  tapiyar ta k'auyen su buki y'ar d'an uwanta ne Abubakar Ya tunk'ari mahaifinsa da maganar kuma ya yi farin ciki sosoi har da sa masa Albarka, k'oda Umma ta dawo ta iske har an yana ka sadakin Abubakar da  Azeeema. Ranar gidan sai da ta tashi  hank'alin kowa na gidan ta hana su barci lafiya tace danta baza ya Aure waccan abar ba.....
    Shiko Malam Usman Yace mata tayi karya wallahi dan aure tsakanin Abubakar da yar d'an uwansa anyi angama, in ko tace bahaka ba saidai takoma gidansu da zama, da taga malam yadau zafi da yawa har da batun sakii sai ta hakura amma tayi alkawarii sai Abubakar ya aure binta diy'ar k'awarta Hinda wacce ita ke kara tinzira ta.
       Haka akayi bukii Uwar Ango bata so balle k'auna kuma har yanxu ta tsane Azeema fiye da da dan cewa take sun shanye mata d'a kuma tanan kan bakan ta na Abubakar sai ya kara Aureee ...............................✍️✍️✍️
Tofah wai matar d'an sanda ta haifi barawo, ku biyoni domin  ganin yadda wannan chak'wakiyar zata k'aya.
    

   
        *Zeesardaunerh ce*

               ( ~Y'ar karamar su babar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now