51&52

209 25 2
                                    

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
        *⚜️©J.A.W📚🖌️*

*PAGE*51~~52

Muna shiga cikin dakin da kud'i muka fara cin karo dasu kan hanya aiko salmat ta wage baki tana rafka salati da kalima inn ta dauko daga farko kafin ta ida ta dauko,

"da d'a shikenan Inna,ashe kema ranar zakka tayi? tunda har barawo ya shigo dakin ki,yanzufa shikenan ya kumushe miki kudin da duk ke gare ki da wadanda kike boyewa?da d'a inna kam sai hakuri amma barawon ya gama damu.."

ta fara sheshsheka tana cewa,

" amma da saura inna tunda gashi ke ya ragamiki wasu a kasa mukuma da bayaso ga badaya ya kundume su"

Shiru ta yi da bakinta ganin Inna ta sulale kasa ta zauna.

Durkusawa muka nayi ina bata baki ganin gabadaya takai matakin da ko magana ta kasa yi ,domin wannan abun yasata cikin wani yanayi,hakuri na dinga bata ina mata kalamai masu sanyi har muka samu ta d'an dawo daidai.
    Ita Salmat Dariya abun ya bata domin ganin yadda innarta tayi zaman y'an bori sai baki agla ke bata.

   Ta buda baki da niyar magana domin ta kara zautar da inna na katse cikin kakkausar murya ina cewa,

"kinsan Allah wallahi kina cewa tak wurin nan sai na baki mamaki"

gum tayi da bakinta amma dariya sai son kubce mata take yi,harara na ballamata tayi saurin hadiye dariyar.

   munkai tsawon minti goma kafin inna ta dafa gina ta mike tana tattara kud'in ta ba tare da tace mana kanzil ba,sai da ta hada kudinta wadanda ke a yashe kasa da wadanda ke hankadin katifa da barawo (salamutu bata tab'a😂)kuma ta bincika ba'a dauki komi na taba sannan ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tana cewa,

"wai Alhamdulilah,Allah na gode ma ka rudar da wannan dan iskan barawo ya kasa daukar kudina "

ta fada tana murmushi,charaf Salmat ta chabe da cewa ,

"ai kuma inna kin yi b'anna,keda ke godewa Allah kuma kina zagin bawanai ? Addu'a ya dace kiyi masa domin nuna godiyarki ga Allah kinga ko makaranta ana gayamana cewa zagin musulmi fasikanci ne ...."

"yo ai na kudin da ya dauka na yi masa, nufin ki sai naki zaginsa ?"

"eh mana inna, namu ya dauka ko?

"eh"

"to ke ina naki ?"

"gasu"

"to don haka kibar zaginsa kar ya zamana yana da aljannu ya biyo dare ya sace kudin ki ba ruwana, nidai nawa dana Adda ya dauka mun yafe masa domin guziri ne ya yi mana a Aljanna, ba abunda zance face Allah ya yiwa wannan barawon Albarka"

"Nikam bazance Allah ya yi masa Albarka ba amma ko don kudina da bai dauki ko nera ba nace Allah ya shiryar dashi "

"kin yafe masa ?"

" ku ba kun yafe ba"

"eh mun yafe, amma kinga ke mukayi niyar ba kudin"

cewar salmat tana kwabe fuska Alamar bata ji dad'i ba

"in banda wani abu da nayiwa barawon nan Allah ya isa wlh amma dai na yafe"

"yawwa innata ya ko gode"

"saninsa kinka yi da zaki ce ya gode,banason har kar shashanci fa karkisa nace ban yafe ba"

dariya Salmat ta yi ciki ciki tace ga ki ga ni bazance na gode ba(🤣🤣)
amma a fili sai cewa tayi,

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now