page 35&36

184 13 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 35&36

Kallon Hajiya Hawwa boka dajjal ya yi bilhakki take wannan maganar tabbas komai zata iya aikatawa domin ya santa tun ba yanzu ba.

Buga kasa yayi tare da wasu y'an tsibbace_tsibbacensa tabbas akwai ga garumar matsala dake shirin tin karota amma kuma bata da alaka da yarinyar! koshi kansa bai san wace matsala bace sai ya yi dogon bincike akan hakan.

Kallon ta ya yi na wani lokaci,shin ya fada mata gaskiya ko ya bari lokaci ya nuna mata?

Wahalar da kanta ne kawai take,kaddarar yarinyar da mijin y'ar ta ba'a had'e suke ba, ko a wanchan lokacin ya so fahimtar da ita,wani lokaci wani abun yana faruwa domin ya zama silar wani abun.

Amma a wannan lokacin ma ko ya fadamata ba yarda zatayi ba bari kawai ya kyaleta ya darji banza.

Dubanta ya yi da jajayen idanuwansa ya bud'e wasgegen bakinsa mai d'auke da jajayen hakora ya fara magana cikin muryarsa mara dad'in sauraro... "matsalar ki ta kau,kin kawo kukanki gurin da za'a share hawayenki,tabbas ina mai tabbatar miki cewa zata bar garin sokoto,za tayi nesa da wannan garin,zamu nesanta ta da mijin y'arki har abada!
amma kuma kisani alamu na nuna cewa akwai gagarumar matsala a gaba!!

"wannan ba damuwa bane Boka,matukar za'a raba yarinyar da Kabeer,inajin ba wata matsalar da zata dameni ko ma akwai zanyi shirin magance ta! Mine ne farashin wannan aikin?"

"Hhhhhhhhhhh Wannan karon ba kud'i ko jini bane"

"ko minene fadi kawai Boka"

"Kece"

"Ni Kuma"

"Eh,zaki kwanta a tare da ni na tsawon kwana biyu,ko baza ki iya ba"
Ya karisa yana murtuke fuska

Kallon sa tayi zuciyarta na tashi amma ko minene zata aikata a domin tsare mutuncinta da farin cikin y'ar lelenta.
Badon taso ba ta amince da bukatar Boka dajjal,shikuma ya dinga washe jajayen hakoransa da basu da kyan gani anjima ba 'a hadu ba.

ALEEYU

Yau baya da aiki a hospital,zaune yake cikin ķawataccen garden d'in sa yana using da system.Since wayewar safiyar yau zuciyarsa ke azalzalarsa,hakan kawai yake jin kamar ya je hospital bai san me yasa hakan ba,he tried his best amma he can't wait any more, dole yaje hospital ko zai samu peace of mind.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now