Page 7&8

112 13 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
Page 7&8

Da guda guda yan buki suka koma inda suka fito kowa ya watse face yan uwa makusanta,akalla yau kwana shida da faruwar wannan al'amarin kuma gobe ne su mama Yelwa,Murja da Anty amrah ke shirin komawa Yola duk sai Aleeya taji ba dadi ba karamin debe mata kewa da kuma damuwa zamansu a gidan keyi ba duk ta kara yin laushi fiye da da komi nata a sanyaye yake kamar mara lafiya.

Sosaima mama Yelwa ke kara yiwa Agla Nasiha mai rasa jiki tare da kara bata hakuri tana ce mata kar tasaka damuwa acikin zuciyarta komi mukaddari ne daga Allah.

Suna shirye_shiryen mayar wa Kabeer lehensa tun da ya fasa auren, ba suga amfanin ajiyarsu ba,suna cikin shiryawa wani yaro ya shigo yace wai ana sallama da masu gidan,yaya Umar ne yaje ya bincika bayan yadawo yake sanar dasu cewa ..

"Uwayen waccan yaron ne mara kunyar ya ma sunnansa" ya karisa ya sun tuna sunan

Mama Yelwa tace "kana nufin Kabeer"

"Eh shi nake nufi mama"

A zafafe mama Kareema ta taso tana fada kamar suna kusa da ita mi zasu zo yau suyi wa mutane bayan abunda dan nasu ya aikata ma?mu ai tsakanin mu da su sai kallo daga nesa

Yaya Umar yace "nima shine na gani momy"

Mama Kareema ta so kar abari su shigo amma mama Yelwa da Dadda suka ce a basu dama aji mi ke tafe da su,wulakanci ba dadi kuma ba dabi'un mutanen kirki bane.

"amma Dadda su da wane suna zaa kira abunda d'an nasu ya aikata, kinsan kuwa maganganun da ke yawo a Unguwar nan game da fasa wannan auren da akayi kinsan abunda suke cewa.."

"Dakata Kareema kibi komai a sannu haka rayuwar duniya take bakomi ne zaki biyewa abun da mutane ke fada ba,idan kikace zaki biyewa zantukansu ranki kawai ne zai bachi, nasan maganganu na cin zarafi da suke wa Takwarata amma wannan abun duka jaddada ce da rashin sanin gaskiya, kuma komai zaki yi ko zaki fada musu baza ki iya wanketa a gunsu ba, lokaci ne, komi mai wucewa ne nan da d'an wani lokaci fatanmu kawai Allah ya bamu karfin ikon cinye wannan kaddarar muda ita... Umar je kace su shigo"

Inna Saude na zaune tana jin duk abunda ke faruwa ba tace kanzil ba; da ita da Aleeya baza ace wayafi zama so silent ba ko da yake dama hakan Aleeya take Inna Saude ce dai bakuwa ga wannan halayyar dakin Inna mama Kareema ta wuce zuciyarta nayi mata zafi suma su Salmat da Ramlat suka shiga dakin su da Aleeya ke ciki wacce tunda taji ance ana sallama ta tashi ta shiga Murja ta mara mata baya,Salmat ji take zata iya cin mutuncin dangin su Kabeer gaba dayan su kan abunda Kabeer ya aikata zuciyarta zafi take mata ko agun Ramlat ma hakanne koba komi sun yi gado gun iyayensu (mussamman hajiya Saude🤣)tsaki kawai suke ja,ji suke da suna dama ko kofar gidan nasu wani mai alaka da Kabeer baza zai tsaya ba balle har ya shigo cikin gidan.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now