SIXTEEN

244 20 8
                                    

Fatima kuwa fira sukayi da anti Hadiza da yan matan biyu suhaima da kuma afra duka kannen mijin anti Hadiza ne.

Ina zan kai wannan? Afra data gama cin masa ta tambaya.

Nuna mata kitchen Fatima tayi sannan ta maida hankali ga anti dake cewa ai itama afra NYSC takeyi saidai ba taje camp ba kamar itama fatima.

Nan fa fira ta koma ta NYSC. Ai saura two weeks a fito camp sai mujira Jin inda akayi posting namu.

Bayan sunyi azahar suka wuce Fatima har mota ta rakasu sannan ta koma cikin gidanta. Nade sallayar datayi sallah tayi sannan ta cire hijab ta shiga kitchen.

Baked chicken tayi da jollof rice sai creamy spinach salad data hada. Zuba mishi coconut juice tayi a cikin jug tabar sauran cikin fridge.

Shiga tayi dakinta ta dauko blue shantli veil dinta ta fesa tiraren once again sannan ta dauka wayarta ta nufi part dinsa.

Sa'a akaci cause tana ajiye gyalenta kan kujerar palor yana shigowa gidan. Setting dinning din tayi sannan ta shiga kitchen.

Kayan dazu da safe tagani cikin basket a kitchen din. Ruwan datazo dauka ta dauka ta fita. Ganinsa tayi zaune kan dinning.

Dukawa tayi ta gaidashi. Wannan karon ya amsata yace lafiya kamar yadda yakeyi. Zuba mishi abincin tayi.

Hala tailor dinki bata iya dinka dankwali bane? Ya tambaya yana kallanta kasa kasa idan ba kalla kayi dakyau ba wallahi zakayi tunanin kitchen yake kallo.

Kallan baby blue lace dinda akayiwa kaftan gown yake. Dinkin ya bala'in yi mata kyau kamar a jikinta aka dinka.

Sorry mantawa nayi dashi Amma ai na sanya gyale.

Dagowa yayi ya kalleta wani bahagon kallo yayi mata wanda yasa ta sauka ta dauko gyalenta batareda ta shirya ba.

Suna zaune farida ta shigo tana sallama tamkar wacce aka tilastawa. Amsawa sukayi a tare ta nemi guri ta zauna kusa dashi.

Baby sannu da zuwa ka wahala ko?

Bai kalleta ba yace baki iya gaisuwa bane?

Dan tari tayi sannan tace haba baby ai gaisuwar na zuwa ko. Ina wuni?

Shareta yayi taje zata kama hannunsa yace karki tabani.

Kama kanta tayi harya gama cin abincin ya mike. Kallan Fatima yayi yace five minutes ki fito Ina jira.

Fita yayi ya barsu su biyu Fatima kam mikewa tayi taja wayarta tayi hanyar fita. Kamin takai kofa taji an bangajeta an wuce.

Kallan ikon Allah tayi tace lallai wannan kanta na hayaki. Rufe part din tayi taje nata ta fidda dankwali ta daura daurin ture kaga tsiya.

Yafa gyalenta tayi sannan ta sanya black Alex evening heels dinta from Saint Laurent. Matching tayi da black Chanel classic purse dinta.

Coconut juice din data hada ta dauko ta fita ta rufe part din nata tayi inda taganshi tsaye bakin mota.

Harararta farida tayi Amma ta share tayi kamar bata ganta ba why? Ko hauka take bazata taba fada da kishiya a gaban abdallah ba.

Shiga back seat tayi sannan suka gaisa da Bala dake a drivers seat. Shiga motar yayi yacewa Bala. Assibitin vintage.

Suna parking a gaban assibitin yace mata one hour highest. Daukar juice din tayi ta fita. Tana shiga dakin taga umma tazo.

Ajiye juice din tayi ta rungume umma tana yan hawaye. Dazu sukayi magana Amma still ganinta yafi waya.

One hour na cika wayarta tafara ringing saidai tana toilet tana yiwa Abdulshakur wanka dayake tun safe ya lake ala dole mami zatayi mishi wanka.

Ganin an sake kira kuma silent take yasa umma dauka tayi sallama.

Daga chan a nutse Abdallah ya amsa sallamar yace umma Ina wuni? An wuni lafiya?

Lafiya kalau Abdallah ya gida?

Lafiya kalau umma.

Masha Allah bari a kai mata.

Ke Aisha ungo wayar nan ki kaiwa fatima.

Koda anti takai wayar an katse kiran. Knocking kawai su umma dake palor sukaji. Anti Amina dake nan tareda umma ta mike ta bude.

To my surprise Abdallah ne. Gaisawa sukayi sannan ya shigo ya duka har kasa ya gaida umma.

Ashema kazo shine kake kira?

Inno je ki duba idan taga yiwa baban naku wanka tazo su tafi.

Chan ta fito tana fadin gobe in Allah yace karka jira sai nazo ayima wanka kaji dirty boy. Ganin Abdallah yasa gabanta faduwa.

Anti Amina tace Ina umma?

Kina shiga ta wuce ya bawa ya Amina amsa. Girgiza kai ya Amina tayi tace umma daga ganin suruki an gudu.

Sallama sukayi bayan yaga abdulshakur sannan suka fita.

Yi hakuri na tsaya yiwa abdul wanka ne. Tafada lokacinda suka sauka stairs din.

Shareta yayi kawai yayi gaba.

Har suka koma gida motar tsit take bamai magana a cikinsu. Sai karar typing dinda takeyi.

===============

Khadija kikace ko jiya tare sukazo?

Eh anti jiyan ma war haka sukazo tare sukayi kusan one hour suka koma.

Murmushi ya Amina tayi tace kice diyar abba an zama matar kulle.

Wallahi kuwa anti dan tun safe na kira na gaya mata Amma sai bayan isha sukazo tare suka koma.

Jijjiga kai ya Amina tayi tace to ai gwara haka dan wallahi da yabar fatima da idan tazo sai dare zata koma kuma auren sabon aure ne.

Time ta duba tace nima zan wuce morning shift ne dani gobe in Allah yakai mu I cannot stay late.

Kallan abdulshakur tayi tace Andyn mama to ummi zata wuce ko?

Kallanta yayi yace Andyn mami zakice ummi kinyi mistake.

Dariya tayi tace lallai Andy an samu sauki. Allah ya kara baka lafiya ya kuma nuna mana aurenka dakai da sauran yan uwanka.

===============

Binshi tayi part dinshi ta hada mishi night tea dinshi sannan takai mishi. Koda takai mishi twelve ta kusa.

Farida da tun dawowarsu take tsaye bakin window taga meke going har tagaji da tsayi ta koma dakinta.

Bacci tayi har taso ta makara sallar subahin dan tana tashi ana sallame sallah. Sallar tayi sannan tayi azkar dinta.

Sai six ta shiga kitchen ta hada mishi breakfast. Arish da kwai tayi sai plantain rolls masu yawa sunyi ashirin.

Shiryawa tayi cikin pencil jeans wanda ya bala'in kamata ta sanya wata baby pink too mai spaghetti hands.

Sannan ta dauko wata baby pink tasha white embroidery dan stones here and there. Wannan karon flat pink Prada shoes ta sanya sannan ta fesa tirare.

Part dinsa taje ta jera abincin sannan ta zauna a living room tana jiran shi as she was thirty minutes early.

This two months din da sukayi tare tasan karfe nawa yake fitowa and karfe nawa yake fita.

Shigowar farida ta bata mamaki ba kadan ba. Kallanta tayi ta wani sha toka sai hawa take tana karawa.

Banza Fatima ta bawa ajiyarta ta cigaba da Kallan tv.

Ganin ta zauna kan dinning zata dauka plantain rolls din yasa fatima mikewa.

Dakata malama me kike shirin yi haka?

Kallanta tayi tace abincin zanci mana.

Wani dan banzan murmushi fatima tayi tace babu rabonki a ciki dan ban dafa dake ba.

Me kike nufi? Nida baby kullum a tare muke breakfast sabida haka wannan abincin sai naci.

Look malama kamin mu samu matsala kija jikinki kikai wani guri dan wannan abincin badonki na dafa ba.

FATIMAWhere stories live. Discover now