NINE

274 20 6
                                    

Washe gari shiryawa tayi cikin latest Sheraton super embellished da aka yiwa dinkin doguwar riga bubu wacce tadan kamata.

Kamar jira baki keyi Sha biyu tayi suka fara ruda dowa a gidan daga kan yan uwanta har nashi

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Kamar jira baki keyi Sha biyu tayi suka fara ruda dowa a gidan daga kan yan uwanta har nashi.

Saida magrib tayi sannan suka samu sararawa. Kamin isha Rukayya da Noor suka sake gyara gidan tsab dukada cewa ba wani lala cewa yayi ba.

Suna yin sallar isha suka ware sai gida. Sati daya ta share kullum sai mutane sunzo gidan ganin amarya.

Tana zaune a palor tana kallan zee world bayan isha intercom dinta yafara kara. Picking tayi danta dauka daga gate ne.

Jin dakakkiyar muryarsa tayi yana fadin ki sameni a part dina. Kamin tayi magana aka katse kiran.

Ajiyeshi tayi ta shiga bedroom dinta ta dauko gyalenta ta yafa sannan ta fito bayan tayi pausing kallon.

Rufe kofar tayi ba tareda tasa key ba. This is the first time data tsaya ta karewa gidan kallo tun shigowar ta cikinsa.

Kallan parts din guda ukku tayi kamin taga part dinda ke kusada nata wutace a kunne. Tafiya tayi side din ta tsaya bakin kofa tayi knocking.

Bude kofar akayi ta tura hadeda sallama ta shiga ciki. Takalminta ta cire ta rufe kofar daga kanta tayi taga ya koma cikin palorn.

Tsarin part din nasa exactly irin nata ne well from the living room and doors haka take tinani.

Palorn nashi shima dai royal ne shigen nata saidai sunfi natan girama and nashi palon komai white and gold ne.

Ganin yana zaune a kan carpet din yasata neman guri nesa dashi kadan ta zauna tace mishi Ina wuni?

Lafiya ya amsa mata batareda ya kalla gefenta ba. Kallan news yake a katuwar TV din tasa. Ganin ba magana zaiyi ba yasa ta kalla center table din dake cikeda ledoji kala kala.

Mikewa tayi ta kwashesu ta nufi dinning dinsa wanda shima set ne da kujerunsa. Nan ma ganin plates tayi dayaci abinci.

Straight kitchen dinsa ta shiga and baiyi haduwar nata ba cause dagani kasan siyayyar namiji ce Amma shima ya hadu sosai.

Bude ledoji tayi ta duba abubuwa da alamu tun ranarda tazo gidan abincin restaurant yakeci. Rufe komai tayi ta bude back door dinsa tasasu a shara including wadanda ke a dinning.

Time ta duba taga ten har tayi. Cupboards din ta duba ta fidda set din kitchen pots ta ajiye sannan ta shiga store dan ganin me yake dashi.

Deciding to work with what she has kawai ta fidda kayan macaroni. Saifa taci neman blender bata gani ba.

Fitowa tayi taga har yanzu idanshi nakan TV. Fita tayi taje part dinta ta duba cikin store ta fito extra blender dinda take dashi.

Freezer ta bude ta fidda wata yar karamar roba ta koma part dinsa. Harta koma kitchen baisan tayi ba.

Rufe kofar kitchen din tayi ta wanke blender din sannan ta zuba kayan miyar tayi blending. Tana gamawa ta dora macaroni din.

Ashe robar data dauko ruwan tafasar namane data dafa dazu da kuma naman.

Lafiyayar macaroni ta dafa masa in thirty minutes sannan ta fidda daya daga cikin warmers dinda ke cikin cabinets ta zuba.

Wanke duk abinda ta bata tayi sannan ta maidasu inda ya dace. Setting din dinning din tayi mishi sannan ta koma ta zauna.

Ashe nakun wani program ne yake kallo tun kamin ta shigo shiya dauke hankalinsa. Batayi ten minutes ba aka gama ya kashe TV din.

Juyowa yayi ya kalleta kamin kuma ya dauke kai ya cire glasses dinsa. Ba karya tun lokacinda ta zauna kamshin tirarenta ya cika mishi hanci.

Dama na kiraki ne in fada miki dokokin gidana. A tsarina ba'a kawo min yar aiki a gida idan zaki iya aikin gidanki kiyi idan bazaki iyaba wannan keta shafa.

Na biyu banda kawo mun tarkacen kawaye a gida I won't tolerate that. Na ukku at all times idan na kira gidanki ki daga waya unless salah kike.

Lastly yafada ya juya ya dauka wani key holder mai makulli guda ukku a jiki ya jefa daidai gefenta.

Those are the keys to this house you can have access to it any time.

Sannan karki kuskura Ina bacci ki tasheni ko duniya zata nade ta nade amma karki tasheni. My sleep is very important to me that's all for now. Yafada yana yin tafiyarsa.

Me hakan yake nufi? Zama zanyi ko tafiya zanyi? Haba Fatima bakiji furucinsa ba? That's all fa yace. To me kuma zaki tsayayi a gidansa?

Fita tayi ta koma part dinta jiki a sanyaye. Rufe kofar tayi sannan ta cire makulli ta ajiye kan console dinta dake hallway din zuwa second palorn ta.

Chanja kaya tayi ta fada kan gadonta tayi adduar bacci ta rufe ido. Tafi hour ukku a farke tana tinani kamin bacci ya dauketa.

Washegari kuwa tana gama sallar subahin ta koma bacci bata jima ba aka dauke wuta zafi ya fada ita.

Lokaci ta duba taga shidda da rabi. Tsaki tayi ta mike. Kitchen ta shiga tafara kokarin hada breakfast.

Pancakes tayi sannan tayi topping dinsu da fruits kamin ta rufe glass container din. Ganin tayi tagama everything in just thirty minutes.

Ruwan tea data tafasa ta juye a cikin wani flask nata mai azabar kyau. A basket tasa kayan kawai ta sanya fara jallabiya mai light blue stones.

Fita tayi ta nufi part dinsa Allah Allah kawai take karsu hadu lokacinda ta maida kayan jiya cikin kitchen sink.

Harga Allah taji dadi a ranta lokacinda taga yaci macaroni din saidai bada yawa yacita ba. A ranta tana murna tace kila bayason macaroni.

Komawa tayi zata fita taji sassanyar muryarsa yana fadin Ina zaki? Since you made it you should serve it.

Dawowa tayi tace mishi Ina kwana?

Lafiya yace mata kamin ya zauna kan dinning din. Dinner set dinsa ta dauka tayi serving nashi breakfast sannan ta dauka cup da niyyar hada mishi tea. 

Hadawa tayi ta ajiye a nan gefensa sannan ta koma kitchen din ta wanke kular data sa mishi abinci a jiya da kuma plate, spoon and serving spoon dinda yayi anfani dashi a jiya.

Komawa dinning din tayi taga wayam babushi babu alamunsa. Tabe baki tayi tace toh ma'ana ya fita ko sallama babu.

Bedroom dinsa takesa ran cewa main bedroom dinsa ne ta shiga and true she found it like she expected.

Cire zanen gadon tayi ta bude drawer ta nema ga sunan kala kala. Wanda ya kwanta mata a rai ta dauka ta shinfida kan royal bed din da da alama kamar set ne har kujerun palor.

Kayan laundry dinsa sun cika basket shara tayi tai moping kamin ta koma part dinta ta debo tiraren wuta.

Bade gidan tayi da tirare sannan ta kwashi kayan zata koma part dinta. Ganin five thousand tayi aje a saman wayarta.

FATIMAWhere stories live. Discover now