TWENTY THREE

315 21 15
                                    

Wish you a blessed and pleasant Jummah. May this valuable day bring satisfaction in your heart and fill your life with the endowments of Allah!

From this chapter we will go on RAMADAN break. Da yaddar Allah bazan sake publishing ba sai bayan Ramadan.

Banko kofar akayi aka shigo and Kallan kofar sukayi sukaga farida. Dauke kanta Fatima tayi ta mayar kan kafafuwanta.

Zaunawa tayi kan two seater tace dear shine ni zaka kira ita kuma matar so har gidanta zakaje daukota?

Allah yace kayi adalci a tsakanin matanka idan ba haka ba ranar lahira zaka tashi rabin jikinka a shanye.

Kallanta yayi kamin yace toh imamu Malik kin gama? Jan bakinta tayi tai shiru sanin cewa karamin aikin sane yayi mata talala a cikin kishiyoyi.

Addua yayi sannan yace zuwan safiya bazai chanja wani abu a gidan nan ba. Nafada tun baya bana san tashin hankali and Ina alfahri da Jin dadin yadda Fatima kika zauna lafiya da farida for a long time baku taba tashin hankali ba.

Yanzu ma I would like for you and farida to do the same.

Kallansa tayi taji wani sanyi a ranta wani farin ciki ya lullubeta. Abdallanta ya kira sunanta sannan a gaban abokan zamanta ya yaba mata.

Dama yana kule da zamansu da farida?

Insha Allah za'a kiyaye da yaddar Allah baza'a sami matsala daga wajena ba.

Kallan farida yayi yana jiran yaji daga bakinta. Dage kanta tayi tace nima haka. Sannan ya kalla safiya dake kallansa tin dazu.

Haba baby ai kafi kowa sanin cewa baza'a samu problem daga gareni ba. Mash Allah yace sannan ya nunawa safiya third palor and bedroom da yatsansa.

Ranar girkin ki, zaki iya anfani da wanchan daki da palor. Kallan Fatima yayi zaku cigaba da kwana biyu biyu or zaki chanja wani abun?

Yanzu kam shock more than happiness ya lullubeta. Anya wannan Abdallah ne ba chanja shi akayi ba?

Abdallah da baya neman shawararki a abinda zaiyi saidai ya fada miki yau shine ke tambayarta that too a gaban matan sa?

Aa a barshi a kwana biyu biyun dai. Tsayar da idanshi yayi kan Fatima kamin yace shikenan. Addua yayi yana gamawa Fatima tace mishi saida safe sannan tayi gaba.

Yau kwana hudu da kawo amarya safiya kuma tun daren kawota suka samu sabani da Abdallah.

THROWBACK

Haba dan Allah yanzu wannan karamin daki da palor zakace dasu zanyi anfani ranar danake dakai?

Akan me bazaka bani main palor da bedroom ba? Ai naga furnitures dinsu are more expensive and sunfi girma.

Kallanta yayi safiya sau daya kawai zan gaya miki wannan maganar ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau.

Main living room da main bedroom na Fatima ne kedin da kikazo yau baki isa ki amshe su ba. Second bedroom da farida ke using is same size as this banga tayi complain ba.

Yau kikazo so karki nemi ki batamun tsarin gidana.

Baby ka tsaya ka fahimci abinda nake nema in gayama. Baby nice amaryarka yar gaban goshi ya za'ayi ace nice mai karamin guri.

Janye hannunta yayi daga jikinsa sai me dan kina amarya? Idan a tinaninki na auro kine dan bana son mata ta to tun wuri ki chanja tunani dan ba zane kika fisu ba.

Abdallah meya kawo wannan maganar kuma? Maganar daki muke bafa wani abuba. Dan kawai nace bazai yuwu in zauna da English furniture ita tanada royal furniture ba?

Idan abinda nafada ya bata ranka baby kayi hakuri baza'a sake be kaji? Lallashi tayi tayi har takai kusan two hours kamin ya sauko.

Washe garin ranar kuwa zaune yake a living room din third room din which was a maroon and black color living room.

Safiya ce gurfane a kasa tamkar mai neman gafara sai kuka take.

Allah Abdallah ka yadda dani wallahi nidin ba yar iska bace wallahi kanen babanmu ne yayi mun fyade ina primary.

Murmushi yayi for the first time naga murmushin Abdallah a rayuwa ta. Makin murmushin yayi mishi kyau saiya maidashi scary.

Dariya yafara kamin ya jingina jikin kujerar. Safiya ni zaki maida karamin yaro? Fyade yayi miki sau nawa? How many years ago?

What's lost is lost but you would never be like this had it been years ago. Ina tinanin jiya kike a primary ko?

Kamin kimin karya ki tsaya ki tsarata da kyau dan yimin karya in kasa ganewa abune mai wahalar gaske.

Mikewa yayi yabar palorn ya shiga main palor. Kallan one sitter dinda Fatima ta zauna jiya yayi kamin ya shiga bedroom dinta.

Wanka yayi ya sanya farar jallabiya ya fito ya shiga side din Fatima. Kwantawa yayi kan three seater dinta ya rufe idansa.

Fatima kuwa bacci suka sha itada rukayya tama riga rukayya tashi. Brush tayi ta fito gashinta a sake ya sauko harya dan wuce kafada kadan.

Bude kofar bedroom din tayi ta fito ta maida kofar ta rufe. Kamshin tiraren Abdallah taji ta wani saki murmushi. Yau kuma da wannan mafarkin kika tashi? Ta tambaya kanta.

Walking across living room din tazo yi taga mutum kwance kan three seater idansa a rufe. Dagani Abdallah ne.

Right then ya bude idansa ya kalleta. Sanye takeda kayan bacci riga mai guntun hannu sai wando three quarter.

•••••••••••••••••••••••••••••••

A gefen safiya kuwa yana barin part din ta dannawa mamanta kira. Tana dagawa tace amarya amarya wannan kira tunda safe haka.

Umma ke kikace bazai gane ba. Umma wallahi ya gane hadda karya nayi masa nace kanen baba yayi kun fyade.

Umma ya zanyi ko saurarena yaki yayi umma wallahi Ina sanshi. Kefa kikace bazai ganeba koda kuwa yafi kowa.

Kuka take tana sabbatu kala kala ta jima a waya kamin tayi shiru ta saurari me ake gaya mata a wayar.

================
END

Kallanshi tayi yadda yake juya spoon dinshi cikin lunch dinda ta hada mish. Itafa wannan mutumin yafara bata haushi.

Kallan hannunta tayi taga bandage dinda ke daure a kai. Dan murmushi tayi tunowa da abinda ya faru kwanaki da suka wuce.

Abdallah idan baka yafe min ba kashe kaina zanyi a gidannan. Tafada tana kallansa hadeda sanya wuka akan wrist dinta.

Kallanta yayi ya kalla wukar hannunta kamin ya dauke kansa yace bismillah ya shige master bedroom dinsa.

Saida taji alamun fitowarsa sannan ta rufe ido ta dage ta yanka hannun kadan jini yafara zuba sosai.

Jinin dake zuba yabi ya bata farar carpet dinda ke palorn. Fitowa yayi ya kalleta ya kalla hannunta sannan yace good enough.

Nan ya tsallaketa yayi tafiyarsa.

FATIMAWhere stories live. Discover now