THIRTY FIVE

315 33 10
                                    

Kitchen ta shiga ta zage ta hada mishi plantain rolls masu rai da Lafiya sannan ta hada mishi da masar datayi ta semo.

Saida ta gama ta kula batayi miyar chin masar ba. Tsaki tayi tayi sauri ta hada pepper soup din kayan cikin rago.

Bata bari yayi kauri ba kuma baiyi ruwa tamkar an wanke kai ba. Kiran Bala tayi ta tambayeshi yana office?

Eh hajiya gani office na ajiye Oga tun dazu.

Kazo gida ka karbi abincin sa nan inda nake.

Wanka ta shiga tayi tana fitowa taji karar doorbell dinta. Hijab mai kauri ta sanya kan towel din taje ta bude kofar.

Ganin Bala yasa ta koma ta dauko kwandon data sanya abincin a ciki. Bashi tayi sannan ta rufe kofar ta.

Tana shiga daki taji wayarta na ringing ta daga kiran.

Wallahi anti khaddy yanzu nakeda niyyar kiranki.

Fatima please kizo Abdulshakur ba lafiya gashi anyi rushing dinsa a assibiti ba abinda yake sai kiran mami.

Okay anti gani zuwa wacce Hospital?

Sky Memorial ko vintage memorial?

Sky Memorial!

Sai nazo.

Kira ta dannawa Abdallah tana hawaye and ya daga da sauri. Sallama yayi ta amsa.

Dan Allah inaso inje assibiti duba Abdul yanzu aka kaishi assibiti ba lafiya sosai.

Ki jira idan na dawo zan kaiki I will be back early yau.

Amma fa bashida lafiya sosai I can't wait har five o'clock.

Nace ki jira zan kaiki ki ganshi!

Yana gama magana ya kashe waya. Kallan wayar tayi takaici na ciyota. Take wani kololon bakin ciki yayi sama ya tsaya mata a zuciya.

Kuka tayi harta godewa Allah. Qarar wayarta yasata duba wanda ya kira. Rukayya ce hakan yasa ta daga.

Anti kina ina?

Ya akayi?

Anti please idan kinada time kizo Abdul yanata kuka sai kinzo gurin kuka har cannula dinshi ta fita kuma yaki bari oxygen din ya tsaya.

Gani zuwa dama na tsaya hada mishi coconut juice ne.

Sauri tayi ta bude wardrobe dinta ta fidda blue atamph mai bala'in kyau anyi mata dinkin kaftan gown.

Luxury veil ta dauka taja car key tayi waje. Saurin rufe gidanta tayi da gudu ta nufi motocin.

Saida ta isa sannan ta kula ashe makullin perfection ne ta dauko. Bata taba fita da motar ba.

Share zancen tayi ta shiga motar datake brand new ta kunna ta sannan ta sanya drive tayi gate.

Bude mata gate din sukayi ta fita a guje. Tukin gan gan ci ta dingayi harta isa assibitin. Ganin ya Amina tayi zata shiga suka shiga tare.

Tana isa ta rungumeshi tace dan mami ba lafiya ko?

Kallanta yayi da idansa da suka kumbura baice komai ba sai damqe hannunta dayayi. Ita ta rikeshi aka sake sanya mishi cannula aka karasa sanya mishi drip dinshi.

Suna zaune su ukku kasancewar sauran Sun koma aiki dan they are on duty ya Muhammad kuma kotu yaje.

Ringing wayarta tayi ta kalla mai kira saida zuciyarta ta halba ganin sunan Abdullah. Batasan sadda tace innalillahi ba.

Lafiya? Ya Aisha ta tambaya.

Wallahi anti Abdallah ne yake kira kuma sai yanzu na tina bada izini na fito ba.

Lallai Fatima kin kai. Sake kira yayi bayan wayar ta katse. Picking tayi hadeda sallama.

Jin kawai tayi yace ki shirya nanda thirty minutes zan iso.

Okay kawai ta samu fada taji ya kashe wayar. Ajiye Abdulshakur tayi tace anti zan tafi. Nanda one hour zan dawo.

Da sauri ta koma kasa ta shiga motarta. A tsiyace ta shiga kwanar gidan. Horn tayi bakin gida suka bude.

Shiga tayi tayi parking motar a inda ta dauketa. Fitowa tayi jiki na rawa tayi part dinta. Zaunawa tayi tana tinani batayi two minutes da zama ba ya dawo gidan.

Shigowa part din yayi ya rufe kofar. Mikewa tayi ta juya ta kalleshi with a shaky voice tace sannu da dawowa.

Ki shirya zan shiga bathroom kawai sai muje yace mata yanayi hanyar bedroom dinta. Bin bayanshi tayi taga ya shiga bathroom.

Don rashin ta ido kin rufe kofa yayi yana ciki. Kallan key dinta tayi kan mirror and tana sa ran ya ganshi.

Tsaki tayi ta dauka dankwalinta data manta dazu ta daura. Yan kunne fashion ta sanya sannan ta shafa mai.

Fitowa yayi yace muje inada abinyi. Binshi tayi ta dauka gyalenta a palor ta yafa. Kallanta yayi yace fita kikayi?

Diriricewa tayi ta rikice kamin tace aa meka gani?

Gyalen kayan nagani a palor.

Tinani tayi chan tace ajiyewa nayi idan ka dawo muje kamar yadda ka fada.

Nodding yayi sannan ya wuce tabi bayanshi tana ajiyar zuciya. A waje kuwa kallan Lexus din tayi tace tab sabuwar mota wannan mutumin ya chanja.

Shima back seat ya shiga suka wuce. Parking sukayi ya fito suka shiga tare. Allah Allah kawai take kar suce tazo dazu.

Sa'a akaci umma na dakin koda suka shiga. Dukawa yayi har kasa ya gaida ita.

Kaima tasoka sukayi Abdallah?

Dukarda kanshi yayi yace ba haka bane umma.

Kallan Abdul tayi taga still bacci yakeyi. Sallama yayi dasu kamin ya wuce tayi mishi rakiya.

Wuni Fatima tayi tana saka da warwara har dare yayi Abdallah yazo daukarta. Komawa gida sukayi a tare.

Mamaki tayi ganin farida tsaye tana murmushi tana kallansu. Takawa tayi taje ta kalla Abdullah.

Baby dan Allah meye haka? Hadda ranar girkin nawa yanzu wannan matar zaka bawa?

Kallanta fatima tayi kamin tace mishi nagode saida safe.

Ta gaban farida tabi ta wuce tayi hanyar gidanta. Wani haushi taji Abdallah din yana bata.

Tsaki tayi ta cire kayan jikinta ta sanya kayan bacci tayi palor tafara kallo. Bayan movie din ya kare ta chanja channel.

Sai two taje ta kwanta bacci amma kuma bacci yaki yazo tayi shi. Drawer dinta ta bude ta dauka magani tasha.

It seems this insomnia is getting worse. Why won't it? I've been stressed and worried since I got married. Tunda ba kanwar ubana bace dole ta karu ai.

Tsaki tayi kamin tace dole gobe inje ganin doctor. Samu tayi bacci ya dauketa tayi bacci har safe.

Shigowar Abdallah dakin shine ya sanyata ta tashi daga bacci.

FATIMAWhere stories live. Discover now