ELEVEN

321 24 4
                                    

A yaune aka bude part dinda ke kallan na Abdallah ba wani jimawa sosai mata suka zo a cikin wata golf baka.

Zaune take tana waya da anti khadija. Har take mata fada wai ba'a zama hakanan batayi komai ba.

List din kalolin abincinda za'ayi suka fara bayan ya Amina tayi joining kiran. Murmushin takaici Fatima tayi tace yau suka fara jere ai.

Toh babu ruwanki da abinda bai shafeki ba Fatima. Karki shiga shagalinsu baki San dame sukazo ba.

Sun jima suna wayar kamin su ajiye ta kira umma suka fara yar fira. Nan take shaida mata ai sunanta ya fito a batch A na NYSC this year.

Masha Allah Fatima Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a.

Ameen umma saidai ki gayawa abba batun camp!

Zan mishi magana da yaddar Allah diyar babanta. Murmushi tayi sannan suka ajiye wayar.

Tana Jin suna magana Amma ta share. Goge goge daya rage mata batayi ba tayi dan kashe lokaci.

Ta fara Kallan wani series a Star Plus aka fara kiran magrib. Pausing tayi sannan ta tafi daki tayi alwala ta kabbarta sallah.

Bayan ta gama azkar ta dauka remote din TV dinta ta kunna ta. Palor ta koma ta danna play sannan ta kashe TV din palor.

Tana kwance a daki tana kallo taji knocking kamar za'a balla kofar side din. Mikewa tayi sanyeda hijab dinta ta nufi kofar tana kiran waye?

Bude ki gani mana. Bude kofar tayi ta kalla matar fara da ita dagani an kara dana kanti. Tambayar ta tayi lafiya?

Cikeda gadara tace kawata farida ce kishiyarki dama zuwa nayi naga da wacece kawar tawa zatayi kishi?

Toh tunda kin gani saiki kama gaban ki ko? Fatima tafada kamin ta rufe kofar a fuskar ita matar.

Tsaki tayi ta koma daki ta cigaba da kallonta. Sallar isha tayi tana gamawa. Ta shirya cikin wata fitted gown wacce tabi shape din jikinta ta kwanta.

Atamphar daya daga cikin na lefenta ce. Tana shafa powder taji intercom dinta ya fara tsuwa kamar ba gobe.

Dagawa tayi hadeda sallama. Jin tayi an amsa an kashe. Murmushi tayi tace Abdallah na dan gata.

Ita wallahi komai yayi birgeta yake. Ba abinda ke sata rikicewa irin yayi magana cikin sassanyar muryarsa.

Shantli veil dinta ta dauka ta yafa sannan ta sanya purple fendi flat shoes ta fito. Yau kam ta rufe kofar ta da key sannan ta tafi.

Tana kallan matan dake waje ta gefen idonta kuma tasan ita suke kallo Amma tayi banza dasu.

Tsayawa tayi ganin wata dattijuwar mata tasha gabanta. Ki kama kanki ki tashi tsaye saida uwar farida da ita kanta farida suka shirya sannan zata shigo gidannan.

Murmushi fatima tayi ko digon tsoro bataji a ranta ba tace wallahi ta Allah ba tasu ba. Duk tashi tsayen da zasuyi basu isa suyi abinda Allah baiyi ba. Amma nagode inna.

Ta gefenta tabi ta wuce.

Kallo matar tabi Fatima dashi tace lallai akwai aiki a gaban farida wannan babu yadda ta iya da ita.

Knocking tayi tana shirin bude kofar aka budeta. Kallanshi tayi tadan rage tsayinta tace Ina wuni?

Bai amsa ba yadai Qura mata ido.

Ganin tamkar yayi freezing yasa tace Maigida? Snapping out of it yayi ya kalleta cikin ido. Akwai baqo a ciki.

Juyawa tayi da niyyar komawa ta sanya hijab yace tsaya mika mata purple hijab dinta data bari a palorn yayi.

Tayita tinanin ina tabar hijab din ashe nan tabarshi. San yashi tayi sannan ya bata hanya ta wuce shi kuma yabi bayanta.

A nan main palorn taga wani mutum zaune yana kallan ball. Gaisawa sukayi sannan taje tayi serving din Abdallah daya wani hade rai.

Kallansa tayi bayan ta zuba taga yana a palorn ba alamar cewa zaizo dinning din. Daukar abincin tayi takai masa inda yake.

Ta koma da niyyar daukar wani plate tayi serving abokin shi yace baci zaiyi ba. Kitchen ta wuce ta dauko ruwa da lemo da cup ta ajiye a gaban baqon.

Tana ajiyewa ta nufi second living room dinsa ta shiga tayi zamanta. Ganin zaman zai gundureta saita fara chatting a WhatsApp.

Tana zaune tana chatting aka bude kofar aka shigo. Kallan Abdallah tayi ya zauna kan daya daga cikin English chairs dinda ke palorn.

Nawa kike buqata?

Sanin inda ya dosa yasa ta girgiza kanta kawai zan bada list sai kasa a siyo.

Abinda za'a siya na tambayeki? Tambayar ki nayi nawa kike buqata?

Ganin nayi koda ka bada kudin it's the same thing zanyi and since I will be giving you a list there's no need for me in karba kudinka.

Mikewa yayi zai fita tace inada magana!

Komawa yayi ya zauna baice komai ba.

Suna na ya fito a cikin first batch din NYSC. Ance sai naje karbar coppers uniform and daganan abba zaiyi processing for me to stay out of camp.

So?

Gobe nakeso naje in amsa idan ka bada izini.

Ki turo min size dinki zaa kawo miki a gida.

With an aching heart tace I don't have your number.

Duba wayarki kawai yace ya mike ya fita. Ba jimawa tabi bayanshi. Mamaki tayi ganin wayam ba kayan dayaci abinci a palor. Kitchen ta shiga ta gansu a sink.

A mamakance take Kallan kitchen din because tunda suke bai taba cin abinci ya dauke plate ba.

Share batun tayi ta wanke kwanukan tas ta fita tayi part dinta.

A waje kuwa gayen kallan Abdallah yayi yanzu AA zaki wannan matarce zaka yiwa kishiya?

A hangame ya kalleshi me kake nufi?

Murmushi yayi da har zance ka shiryawa balai a gidan sai na tuna mutum biyu ke fada ba daya ba.

Juyawa Abdallah yayi ya nufi part din nasa.

Kwana hudu yan gidansu farida sukayi suna zuwa jere kamin su gama. Gidan amarya kam idan comparing zamuyi saidai muce Allah ya sauwaka.

Ko banza karfi ba daya ba. Itama dai iyayenta sunyi iya bakin kokarinsu wajen ganin sunyi mata abinda zasu iya.

Daki biyu suka gyara mata da palor daya. Forty five inches LG plasma suka sanya mata a main palorn ta.

Kujerun kuwa dukda sunada girma Amma girman part din sai yayi overwhelming nasu suka koma yan kanana dasu.

A gefen amarya kuwa rikici ya kaure lokacinda wata distant cousin din Abdallah datake friend dinta ta gaya mata wallahi ko qurar Fatima bata kai ba a gurin kayan daki bale biki.

Nan farida ta tayadda hankalinta ta tayarwa babanta hankali kan wallahi ita bata yadda ba.

ATM dinda Abdallah ya bata ta wurgawa ummanta. Ga wannan kuje ku sake siyayyar kayan daki.

A daren wankin amaryar motar Abdallah tayi parking a cikin gidan ya fito daga gidan baya. Kallan nazir driver dinsa yayi yace gobe da sassafe dan Allah karka bata lokaci.

Jin kawai yayi message na shigowa. Fidda wayar yayi ya kalla message din alert ne na five million.

Rufe wayar yayi ya shiga cikin gida.

FATIMAWhere stories live. Discover now