THIRTY FOUR

292 30 9
                                    

Da kikaje malamin naki bai gaya miki cewa zan rufe miki kofa ba?

Saurin sakinshi tayi kamin tace bangane ba me kake nufi? Juyowa yayi ya kalleta with same resting face.

Eh mana wannan malamin dayayi miki alqawarin zai fitar da Fatima daga gidan nan. Bai gaya miki ba?

Take jikinta ya a fara rawa ta zame a kasa. Dan Allah kayi hakuri baby sharrin shedan ne da kuma sharrin qawa.

Kallanta yayi kinyi shirka kuma kike tinanin in zauna dake?

Kneel down tayi wallahi ba halina bane baby ban taba ba sai yau kayi hakuri kamin rai.

Kallanta yayi tana hawaye kamin yace kin gama?

A mamakance ta kalleshi waiko wannan mutumin kalau yake kuwa?

Kin manta? Ranarda nace miki to hell with you cewa kikayi saikin maidani mijin tace kin manta?

Bama wannan ba tafiya kikayi bidda gurin wani Anas ya baki tirare shi kika sanya ranarda aka kawoki gidannan.

Sannan idan har ban manta ba yayar mamanki da tazo jere tareda yan uwanta sun bar miki sako a cikin flowers din bayan gidanki.

Sakonda kika tona kika qona kwana hudu da zuwanki gidan nan. Sannan kuma duk abinci wanda kikayi a gidannan saida kika zuba mishi magani da aka baki koba haka ba?

Innalillahi wainna illaihir rajiun dan Allah Abdallah kamin rai.

Kallanta yayi batareda emotions ko daya a ransa ba.

Meye na innalillahi? Bayan kin daina sallar asuba sabida neman duniya? Dama kinsan Allah?

Farida ni zakiyi kokarin yiwa asiri? Ni? Ce miki akayi bansan kaina bane?

Da Allah kika rike tamkar yadda kika rike wadannan bokayen farida da tuni Allah ya baki abinda kike nema saidai kash hankali ba isarki yayi ba.

Dan Allah Abdallah kayi hakuri idan gidanka zan barma zan barshi Amma kamin rai.

Tsayawa yayi kallanta kamin ya cire glasses dinsa ya dage girarsa.

Abinda ya tsorataki yadda akayi na sani ko?

Nodding tayi

Wani malalacin murmushi ya saki kamin yace karki damu nidin mutum ne ba abinda ranki yake raya miki ba Allah na rike kema ki rikeshi.

Ba zan sakeki ba at least not now farida kinsan meyasa?

Kallansa tayi jiki na mazari tace aa.

Sabida nasan dama ba son tsakani da Allah kike min ba and kallo daya na miki na gane hakan tun haduwar farko da mukayi.

Saidai nima I used you for my own selfish interests abba ya matsa sai nayi aure shiyasa na aureki.

Dama Abdallah baka sona? Ta tambaya hawaye na mata zuba.

Eh bana sonki yafada mata kirikiri ba wani corner corner. Time ya kalla sannan yace ki komawa Allah wata qila in soki.

A guje tabar part din akayi daidai da Fatima ta dawo daga karbar sakon mommy. Ido hudu sukayi da farida wacce ta wuce a guje.

Trouble in paradise tafada tana tabe baki chan wata zuciya tace anayi muna jin dadi.

Washegari baqi tayi sisters dinta sukazo suda yaransu gabadaya. Take gidan ya cika da hayaniyar wasan yara dan garden tajasu sukaje and kuma garden din yanada playground.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abinci sukaci suka hau fira. Fatima yaushe zaki fara aiki? Ya Amina ta tambaya.

Sai next month wai research lab dinmu is not completed shine suke karasa kawo kayan da zamu bukata amma dai confirm confirm next month zamu fara.

Nawane salary dinki? Ya Aisha ta tambaya.

Kallanta Fatima tayi tace five hundred and twelve thousand naira after an cire tax and all that.

Masha Allah mami allah ya sanya musu albarka kuma ya kawo muna babies da zasu chinye kudin.

Ameen duka suka fada sannan suka cigaba da fira. Wai nikam Fatima naji magana a gari wai Abdallah ya saki matarshi ta ukku hakane? Ya khadija ta tambaya

Eh hakane shekaran jiya abin ya faru da dare bayan isha.

Meyasa? Ya Amina ta tambaya.

Nima anti ban sani ba kinsan ba yawan magana bawan Allah keyi ba.

Kawai naji hayaniya na fito naga ya bata takadda na koma gidana nayi zamana. Shine daya shigo nace dashi lafiya?

Sai cewa yayi wai she's cheating that's all I know. And sai jiya gashi yan gidansu sunzo kwasar kaya.

Jimami sukayi kamin anti Amina tace to Allah ya kyauta yasa hakan shiyafi zama alkhairi.

Dawowa rukayya tayi da drinks suka sha suka karasa firarsu nan take jin ashe amaryar su mommy qawar rukayyace.

Sai bayan isha anti Aisha taje gida itace last ga wucewa rakota Fatima tayi tana rikeda iman dake bacci ta sanyata a mota.

Dagowa tayi sannan ta rufe kofar sukayi saida safe sannan taga wucewarta. Komawa tayi zata part dinta tayi ido hudu da Abdallah dake tsaye bakin window sanyeda farar jallabiya.

Saida tayi ihu danya bala'in bata tsoro kallansa tayi sannan tai murmushi tace mai house an dawo?

Kallanta kawai yayi baice komai ba ita kuma ta tabe baki dan taji haushi. Kabe kanta tayi ta isa gidanta ta rufe kofar ta shiga bedroom.

Jin kamshin freshener yasata murmushi Allah dai yayiwa rukayya albarka kamin taje ashe gyara mata daki tayi ta wanke toilets dinta guda biyu da aka shiga.

Kallo tayi har kusan ukku na dare sannan bacci ya dauketa dama tana a daki kwance saman gado TV din kuwa sai four ta kashe kanta.

Kiran faro ta mike tayi bathroom ta doro alwala ta fito ta shinfida sallaya ta shiga ta zauna zaman jiran ayi kira.

Tana sallame sallah tafara azkar bacci na cinta amma saida ta kare azkar sannan tayi baccin akan carpet.

Tana cikin bacci taji maganar mutum hakan yasa ta bude idanta. Ido hudu sukayi da Abdallah dake sanyeda farar shadda tayi mishi kyau harta gaji.

Kyaftawa ta sakeyi kamin chan tace ba gaskiya bane mezai kawoshi nan yana chan tareda matarshi.

Juyawa tayi dan ta karasa bacci amma ya dagota ya zaunarda ita. Kallanshi tayi ta taba kuncinsa jin mutum yasata tayi baya tace Ina kwana?

Lafiya! Plantain rolls nakeso yafada yana kallanta.

Amma ba girkina bane.

Tsareta yayi da ido ta mike ta shiga bathroom ta wanke fuskarta tayi brush ta fito. Ganinshi zaune kan gadon yasa tace zai dauka one hour zan aikama dashi office.

Mikewa yayi ya fita batareda yace mata komai ba. Binshi tayi da ido tace lallai ma Abdallah ka raina min hankali.

Jiya inma magana ka shareni yau ka wani tadani daga bacci wai plantain rolls. Kaci sa'a nima inaso inci da wallahi kyaleka zanyi kayita zuba ido kaga wayam dan rainin wayo.

FATIMAWhere stories live. Discover now