TWENTY

310 28 7
                                    

Kallan Abdallah tayi yana cin abinci kamin ta mike ta dauka intercom ta kira part din farida. Picking tayi tace lafiya?

Dama maigidan yace kizo. Tana gama isar da sakonta ta ajiye wayar. Komawa tayi ta zauna kan kujerar tana wasa da kwalliyar laffayarta.

Yana saukowa daga dinning din kofar shigowar na budewa. Zaunawa yayi kusada Fatima kan two seater din datake zaune.

Guri farida ta nema ta zauna hadeda daure fuska. Kallanta yayi yace idan attitude kikazo gwadi tashi ki bani guri.

Sakin fuskarta tayi sannan tace Ina wuni. Batareda ya amsata ba yace sanin kankune magana mai yawa bata dameni ba and banason maimaita magana.

Taraku nayi dan in gaya muku zan qara aure. Yau akaje kai kudin sadaki.

Harararsa farida tayi kaga malam kanka kalau kuwa? Ko sanyi ya shigo hauka ta kama ka? Aure fa kace?

Wallahi baka isa ba yaushe mukayi aure da har zaka tsiro wani maganar aure? Wallahi Abdallah baka isa ba. Ni zaka chuta? Wannan chin amanar damea tayi kama?

Kallan cikin idonta yayi yace kwarai kuwa aure zan kara nan da wata daya.

Ihu tafara sannan tafara hargitsa palorn gabadaya. TV dinsa taje zata kashe yace kul karki kuskura hannunki yakai kan TV na.

Fita tayi daga part din tana fada da masifa. Wallahi baka isa ba. Nida kai ne shege kafasa. Yanzu haka wannan munafukar matar takace ta zugaka.

Ita dai fatima ikon Allah ta tsaya kallo chan ta mike ta gyara palorn. In thirty minutes ta maidashi yadda yake ada except for glass decors dinda farida ta fasa.

Tunda tafara aikin harta gama kallanta yake. Ya dauka duk kanwar jace itada farida Amma sai yaga akasin hakan. Kitchen ta shiga ta dafa mishi tea ta fito.

Bedroom takai ta ajiye sannan ta dawo palor tace mishi idan auren ba alkhairi bane Allah ya watse shi. Idan kuma alkhairi ne garemu gabaki daya Allah ya kara sanya alkhairi a ciki kuma yasa ayi damu.

Fita tayi daga part din dakyar da boni ta isa part dinta jiri na neman halakata. Sauri tayi ta bude part din ta shiga ta kulle.

Kuka ta sanya mai chin rai. Kuka tayi har hawayenta suka kare. Kwantawa tayi dan tayi bacci amma ta kasa.

Tana kwance taji ihun farida.

"Ni zaka cewa bakin aurena Abdallah? Nidin? Ka manta wacece ni?"

Kallanta Abdallah yayi yace bismillah farida nuna min wacece ke na manta.

Juyawa yayi ya koma part dinshi ya dafe kanshi. Dama yasan farida batada hankali amma baisan haukar tata har takai chan ba.

Har daya na dare idon fatima biyu ta kasa bacci. Mikewa tayi tana dafa bango ta shiga bathroom ta doro alwala ta fara sallah.

Tun tanayi a tsaye har tagaza tafara a zaune. Ba'a jima ba tafara ganin duhu yana gilmamata.

Bayan ta sallame ta kwanta kan carpet din tana addua. Nasan Abdallah baya sona kuma bazai soni ba Allah ka chire min shi a raina.

Allah ka bani ikon daina son wannan bawan naka. Har aka kira subahin idonta biyu a haka nan tana ganin duhu ta shiga bathroom ta fito tayi sallah.

Tana gamawa ta mike tana tangadi ta shiga bathroom again ta sakarwa kanta ruwan sanyi suka ratsata.

Fitowa tayi ta kwanta kan gadon tana jin wani sanyi sanyi a ranta. Hijab ta sanya tafara karatun Qur'an tafi two hours tanayi bata kula da time ba.

Saida taji fitar Abdallah daga gidan sannan ta duba time taga eight thirty. Cigaba tayi da karatun ta dan jin ta samu natsuwa sosai.

Abinda ya tada ita daga kan gadon was sallar azahar. Lafiya kalau babu juwa babu komai tayi sallah. La'asar tayi sannan ta kunna AC din dinning.

Jollof rice tayi da pepper soup din catfish. Koda six tayi ta gama. Part dinsa takai abincin ta ajiye.

Tana fitowa sukayi karo da farida wacce dawowarta kenan tace

Sannu wahalarliya duk wannan bautar da ake masa bai hanashi ya auroni ba kuma gashi yanzu zai karo wata.

Murmushi Fatima tayi kamin tace na dauka a iya zaman da kikayi da Abdallah zaki karanci halayensa sai aka samu akasin hakan.

Wai shin baki san cewa abinda zaman lafiya bai kawo ba tashin hankali bazai kawo shi ba? Abdallah ya rigada yayi niyyar sake aure ihunki da tashin hankalinki bazai hanashi abinda yayi niyya ba.

And malama please wake up from your delusion. Kishiya bani za'a yiwa ba ke zaa iya dan haka duk abinda zakiyi kije chan ku karata ni bakwa gabana.

Tafiyarta tayi tabar farida tsaye tana budar baki tana kullewa.

Saida tayi isha sannan ta sake shiga wanka ta sakarwa kanta shower tayi kusan thirty minutes sannan ta fito.

Tana fitowa ta chanja kaya zuwa wata farar gown simple marar nauyi. Hanyar fita ta nufa unfortunately zubewa tayi a tsakiyar carpet din.

============

Abdallah kuwa as usual ya fito on time Amma yaji baiji motsin mutum ba. Ganin dinning wayam yasashi duba freezer ya fidda yogurt yasha.

Zaunawa yayi kan dinning din yace nayi tinanin itace mai hankalin amma sai ya zama ba tada ban banci da waccan mahaukaciyar.

Fita gidan yayi yaje office. Harya tashi dawowa gida hankalin shi na kan meyasa batazo ba? For more than nine months Fatima never failed to make him breakfast and dinner. Why?

Komawa gidan yayi yana isa part din yaji kamshi na tashi. Shiga yayi and kamshin ya dabai bayeshi.

Kulle kofar yayi a ransa yace tazo kenan. Alwala yayi yaje masallaci saida yayi isha'i sannan ya koma gidan.

Kiranta yayi a intercom taki picking yayi kira yafi sau biyar. Ganin taki dagawa yasashi daukar makullan part dinta yasa takalmasa yayi waje.

Bude part din yayi ya shiga. Sanyi da kamshin tiraren wuta suka bugoshi hakan yasa ya rufe idansa yaja numfashi.

Rufe kofar yayi ya shiga chan ciki. Kitchen ya duba bata nan sannan ya nufi dakinta bayan ya kashe AC din dinning.

Yana bude kofar ya hangota sheme a kasa. Sauri yayi ya karasa inda take ya dagota. Tana numfashi Amma sama sama.

Ajiyeta yayi ya kira Bala yace ya fito masa da mota sannan ya dauka gyalenta.

Mota yakai ta yasata a back seat. Zaunawa yayi tareda ita yace. Sky Memorial Hospital Bala ya kaisu.

Sake daukarta yayi ya shiga assibitin da ita. Emergency room din ya shiga already ya kira doctor Hauwa tana gurin and she is an ER physician.

Bayan ya ajiyeta Dr Hauwa ta kalleshi tace ya akayi?

Girgiza kansa yayi yace I don't know kawai na dawo daga masallaci naganta a kasa.

FATIMAWhere stories live. Discover now