THIRTY TWO

285 26 6
                                    

Abincin yafara ci kamin yace she slept with another man.

Fuskarta went pale and ta zuba mishi ido like seizing tayi tamkar dasata akayi a gurin.

Jin batace komai ba yasashi dagowa ya kalleta. Dage gira yayi chan yace you should breathe I don't want to go to the hospital tonight.

Blinking tayi sannan tafara breathing. Chan tace yaushe?

Four nights ago ranar sunan latifa data fita.

Bawai inama shishigi ba Amma are you sure? Ka tabbata?

Kallanta yayi kamin yayi murmushi ya cigaba dacin abincin sa.

Wannan ne karon farko dataga murmushinsa Amma kuma he shouldn't be in a place to smile. Matarshi tana ganin wani qato kuma yayi murmushi.

Mikewa yayi bayan ya gama ya shiga bedroom dinta. Shiga tayi itama taji karar shower. Komawa tayi palor ta dauka hijab dinta tayi part dinshi.

Kayansa ta dauko na bacci ta ajiye kan gadon sannan ta koma part din ta kwashe kayan dayaci abinci shida abdul.

Wanke wanke tayi sannan ta fito tana fitowa ta hango safiya ta fito part dinta da akwati a hannu.

Tana ganin Fatima ta saki akwatin tayi cikinta da kokuwa. Fitowa farida tayi daga part dinta tana dariya.

Tureta Fatima tayi sannan ta cire hijab dinta tace zo. Ki sake shigoni ki gani idan ban miki illa ba.

Abdallah daya fito daidai lokacinda safiya tayi cikinta ya tsaya kallan ikon Allah. Kallan Fatima yakeyi wani kallo na musammam kamar bai taba ganinta ba.

Fati! Ya kira sunanta ta juya ta kalleshi. Alama yayi mata da hannu tazo.

Tafiya tayi gurinshi yayi mata alama na ta shiga cikin gida. Shiga tayi yabi bayanta bada jimawa ba.

Kulle kofar yayi yabar key a jiki kamin ya zauna palor ya fara kallo. Ita dai ikon Allah kawai ta tsaya kallo.

Abdallah baiyi kamada mutumin dayayi finding out matarshi tayi cheating on him ba because kamar yadda take ganinshi a koda yaushe yauma haka ta ganshi.

Idan kikaci gaba da kallona zan fara narkewa ya fada batareda ya kalleta ba. Dauke kanta tayi kamin ta mike tayi bedroom.

Binta yayi da ido kamin shima ya mike yayi dakin. Koda ya shiga tana bathroom tana wanka.

Kwantawa yayi kan gadon ya cire glasses dinshi ya ajiye kan bedside drawer sannan ya rufe idanshi.

Kallon farko zaka dauka bacci yakeyi dan itama Fatima haka ta zata. Kwantawa tayi a dayan gefen ta juyo tana kallanshi.

Wai wannan kyakyawan mutumin mijina ne? Ta fada tana kallan fuskarsa.

Hannunta ta sanya ta shafa gashin girarshi kamin tace to shi kuma yau meya kawoshi bacci a dakina? Lafiyar shi kalau kuwa? Ko kuwa ce mishi likitanshi yayi mutuwa zaiyi cikin dare shine yazo nan? 

Lips dinshi ta shafa chan tace dama ni Allah ya bawa wannan kyan da Kallan kaina zanyi tayi Ina murmushi a mirror.

Ba kamar wannan mutumin ba kullum with a resting bitch face waini fuskarsa bata ciwo ne? To top it all baka gane jin da dinshi baka gane fushinsa. Gama gulmarta tayi ta fara tossing and turning tana kokarin tayi bacci.

Ganin baccin yaki daukarta yasata mikewa ta fidda wata bottle din magani ta ajiye kan bedside drawer tayi waje dan dauko ruwa.

Dawowa tayi tasha maganin sannan ta rufe ta mayar. Kashe wutar dakin tayi sannan ta rufe idonta. Inji Allah bacci tayi Amma three nayi ta bude idanta.

Tsaki tayi sannan ta shiga bathroom tayi alwala ta fito. Palor ta koma gudun karta tasheshi daga bacci ta kabbarta.

Nafila tayi har zuwa three thirty sannan ta zauna kan carpet tana addua kasa kasa bakajin me take fada Amma hadda hawaye takeyi.

Chan ta mike ta nade carpet dinta ta cire hijab ta koma dakin. Turus tayi ganin wanda taji tsoron tayarwa a tsaye yana sallah.

Kayanda ta sayan ta cire ta nadesu ta mayar a drawer sannan ta maida kayan baccinta. Komawa tayi kan gado ta kwanta and bacci ya sake daukarta.

Batasan lokacinda ya gama sallar ba kawai ta tashi tunda safe taga yana bacci a gefenta. Mikewa tayi ta shiga wanka.

Fitowa tayi daure da towel and har zuwa sannan yana kwance tana bacci. Harkar gabanta tayi sannan ta bude wardrobe ta fidda leshi dinkin fitted gown ta sanya.

Fita tayi daga dakin ta shiga kitchen tafara hada breakfast. Sanin yau weekend's ba office zashi ba yasata yin something simple.

Ruwan tea ta zuba a flask sannan ta soya mishi dankalin turawa da kwai. Tana juye kwan cikin kula takai dinning.

Ganinshi tayi zaune yana dannar wayarshi. Plate ta koma ta dauko sannan tayi serving nashi ta tura mishi ketchup.

Zubawa kanta tayi itama kamin taci abincin ta sauka daga dinning din tayi bedroom dinta cause fitsari ya korota.

Bayan tagama abinda take ta kalla sink dinta taga extra toothbrush duba dustbin tayi taga packaging nashi a ciki.

Shi wannan mutumin saiya zauna yiwa mutum bincike a daki?

Wanke hannuwanta tayi sannan ta koma dinning din ta zauna. Tea ta hada mishi sannan taja kayan hada tea ta hadawa kanta sabanin shi da sugar kawai tasa mishi a cikin ruwan tea din data tafara (don't come for me not white water but tea water)

Kallanta yayi yace nifa?

Kallanshi tayi bangane ba?

Ke kadai kikeda bakin shan madara da ovaltin ne?

Murmushi tayi kamin ta janye tea dinsa data hada mishi ta bashi nata. Nashin kuma ta zuba mishi madara da ovaltin tayi sipping.

Jin sugar wasn't enough yasata karawa. Knocking akayi mata ta duba wayarta taga first day of the month.

Yau ake clearing stores dinsu. Mikewa tayi ta sanya hijab dinta ta nufi kofar kitchen ta baya ta bude.

Ina kwana malam Shuaib?

Lafiya kalau hajiya nazo chanja kayan store dinne.

Bismillah tace tana komawa ciki tana shigowa ta rufe kofar kitchen din ta zauna ta karasa breakfast.

Budar bakin Abdallah sai cewa yayi bana hanaki saka fitted gown ba?

Dukarda kanta tayi tace eh.

Meyasa kika sanya?

Allah Ina San fitted how a gida umma bata bari ayi mun but nan I can wear my stuff tunda ba fita nakeyi ba kuma ba zuwa mutane suka cikayi ba.

FATIMAWhere stories live. Discover now