TWENTY FOUR

322 27 6
                                    

Kallan umma rukayya tayi tace umma meye na damuwa.

Girgiza kanta umma tayi tace bazaki gane ba. Dole in damu da Fatima tana zaune da kishiya har biyu a cikin gida rukayya.

Wannan zamane dani kaina uwarta ban yi shi ba.

To umma kin manta cewa ya Aisha kishiya ukku ne da ita kuma tana zaune kalau? Ya Fatima tafi ya Aisha fada idan an tabota.

Sannan nice shaida ya Abdallah yana son ya Fatima. Umma ranarda aka kai amarya shida kansa yaje ya jata sukaje part dinsa.

Sannan Washe gari tunda safe a palorn ta muka ganshi. Umma ki daina saka damuwa a ranki.

Ita din ma wacce aka yiwa kishiya bata damu ba saike.

============

Farida ta gama cika koda akayi kwana bakwai da kawo amarya. Kullum sai taje part din Abdallah kuma kullum da bakin ciki take komawa nata part din.

Ita harta mamakin Fatima takeyi da bata shiga part din sai ranar girkinta. Batasan Fatima is a firm believer na cewa abinda baka gani ba baya batama rai.

Sai taje tagani sannan zata wuni ta kwana da bakin ciki. Hakama Alhamdulillah ai. Da harta fara adduar Allah ya raba aurenta da Abdallah ta samu wanda ke sonta ta aura Amma yanzu ta chanja kala addua take Allah ya barsu tare.

Eight daidai ta shiga part din sai zuba kamshi take ta dauki wanka cikin boyel baki mai yellow designs.

As usual ture kaga tsiya tayi ta saka yan kunnen zinari masu dan tsayi sannan ta sanya zoben yan kunnen hannunta daure da agogo tamkar wacce zata gidan biki.

Setting din dinning din tayi ta shiga kitchen take ranta ya baci ganin kaya ko ina a aje har wari kitchen din ya fara.

Rufeshi tayi sannan ta koma palorn ta zauna. Kallan carpet tayi taga ba wacce tasani bace an chanja ta.

Bude kofar third palor akayi safiya ta fito sanyeda abaya brown mai kyau. Sai hamma take tamkar zata hadiye mutane.

Kama kanta tayi ganin Fatima zaune tana Kallan tv. Take wani tinani ya shigo ta taje ta zauna tana Kallan Fatima.

Sannu uwargida.

Kallanta fatima tayi fuska a sake tace sannu amarya.

Nace ba daga yau ki dinga anfani da third palor din da kuma bedroom ni zan dinga anfani da master bedroom da master palor.

Murmushi Fatima tayi tace hakan bazata yuwu ba saidai idan maigidan ne yabada umurnin nayi hakan.

Hade rai safiya tayi magana ta daidai take data baby.

Dauke kanta Fatima tayi bata karabi ta kanta ba taci gaba da kallo. Farida data shigo sanyeda wata blue atampha super exclusive anci ubanta wajen dinkin daya matseta harya gani ta kallesu.

Zage extension din dake lake da socket safiya tayi hakan yaja hankalin Fatima. Dan daga murya safiya tayi Ya Ina miki magana zaki shareni ki koma Kallan tv.

Mikewa Fatima tayi ta kalleta cikin ido tace kul wannan ya zama na farko ya zama na karshe da zaki shiga gonata batareda izinina ba.

Karki kuskura kuma ki sake daga min murya dan koshi mijin da kike taqama kike tinkaho sabida shi baya daga mun murya sabida haka ke din baki isa ki daga mun murya ba.

Bana shiga harkar ko wacce daga cikin ku sabida haka ki kama kanki karki shiga harkata domin yin hakan babban matsala ne a wajen ki.

Farida dake bayanki shaidace bata shiga harkana bana shiga tata. Idan zama lafiya kikazo kiyi a gidannan zamu zauna lafiya Amma idan tsiya kikazo nafiki iyata.

Tsit kake jin palorn a fusace safiya tayi waje hanyar barin part din while ita kuma farida ta nemi guri ta zauna a ranta tana gulmar dama wannan matar haka takeda balai?

Fatima tace dakata malama wanke wanken da kika tara a kitchen yana jiranki kije kiyi nan part din ba'a tara wanke wanke ko shara a area dinda ake sharing.

Na tabbata ba haka kika isko kitchen dinba sabida haka ba a haka zaki barshi ba. Fitowa Abdallah yayi sanyeda farar maroon shirt da kuma black trousers.

Kallansu yayi yadda sukayi cirko cirko a palan da kuma fatima dake zaune fuska a hade tana danna waya.

Lafiya?

Juyawa tayi ta kallesa ta saki fuska tace dashi Ina kwana?

Lafiya kalau tambaya nake.

Murmushi farida tayi tace dear ka tambayi amaryarka magana tafi dadi a bakin mai ita.

Wani kallo safiya ta watsawa farida kamin ta kalla abdallah zatayi magana yace Fatima Ina jinki.

Safiya kuwa jin tayi tamkar ta saki kuka ganin yadda yayi ignoring existence dinta ya zauna yana dauko remote.

Dear bafa zata kawo ba.

Kallanta yayi yace akan me?

Murmushi tayi tace amaryarka gurin neman fada ta zage kan extension din. Kallan Fatima yayi ba zakiyi bayani ba?

Abinda ya faru daga farko har karshe tagaya mishi. Juyawa yayi yaga babu safiya babu mai kama da ita.

Kallan farida yayi yace meya kawoki?

Ita harga Allah ta manta abinda yazo da ita tun farko. Dama inaso zanje gida ganin mama batada lafiya tun jiya da dare suka kirani.

Karki kai magrib kawai yace sannan yaje gurin intercom dinsa ya kira part din safiya. Picking tayi yace minti ukku kacal na baki kizo Ina neman ki.

Dinning yaje fatima ta bishi ta zuba mishi abinci. Kallan abincin yayi weirdly kamin ya kalleta.

Ganin yana kallanta wani iri yasa tace dumplings ne da dipping sauce sai kuma noodles.

Ajiye fork din yayi sanna yace yau bazan samu ko sausage din ba?

Yadda yayi maganar yaso ya bata dariya because kamar yaron da aka hanawa sweets haka maganar ta fito.

Bafa vegetable stuffing kawai ne a ciki ba beef yafi vegetables din yawa.

Shigowar safiya yayi daidai da karar da timer dinsa tayi. Bata hau stairs in dinning ba tace gani.

Kije kitchen kiyi clearing mess dinki.

Haba baby kamar ni zakasa wanke wanke? Ko a gidan mu banyi wanke wanke ba sabida haka bazan yishi a nan ba.

Sannu princess aikin da wahala ko? Yafada sarcastically yana kallanta.

Eh wallahi ni kazantar wanke wanke nakeyi. Yaushe umma zata turo masu yimin aiki?

Nodding yayi kamin yace a gidana babu mai aiki idan bazaki iya aikin kiba to saidai ki bari. Kije wanke wanken ki yana jiranki.

Kallansa tayi speechless kamin tace bafa zanyi wanke wanke ba.

Ajiye fork din tayi ya sake kallanta. Allah ko?

Eh tafada a shagwabe.

Dan murmushi yayi Eh fah hakane babu dole safiya. Amma fa idan bakiyi wanke wanken da kika tara ba to saidai kije gida kinga a chan gida babu dole kiyi.

Take murmushin dake kan fuskarta ya gushe. Me kake nufi baby? Saki na zakayi kan wanke wanke? Bayan kanada mata biyu da zasu iyayi tunda sun saba especially wannan.

Da murmushin akan fuskar sa yace.

Aa bance zan sakeki ba princess safiya cewa nayi saidai kije gida chan din da wanke wanken bai zama dole ba.

And regarding matana especially Fatima tako fiki jin dadi a gida and she knows to clean up after herself.

Princess safiya idan farida zata iya sauke girman kai tayi wanke wanke kema zaki iya ai. Sabida haka

murmushin dake kan fuskar da ya gushe ya hade rai ya karasa kije wanke wanke na jiranki.

Kama hanyar kitchen tayi yace one last thing. Juyowa tayi ta kalleshi.

Kallan cikin idanta yayi yace matana ba bayin ki bane. Sannan fatima ta wuce raini a gurinku.

FATIMAWhere stories live. Discover now