FIVEE

299 23 5
                                    

Yau sati daya da sallamar Fatima da akayi daga assibiti. Kwance take a daki maganar da sukayi da yaya Amina na dawo mata.

Hakika tabbas babu karya a maganar anti. Allah shike bayarwa kuma shike kwacewa. Komai yayi tsanani to maganinsa Allah.

Ba abinda zata iyayi face ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Yana daya daga cikin qualities na Muslim yadda da kaddara mai kyau da marar kyau.

Ba abinda zatayi inba tayi addua Allah ya bata ikon chinye wannan jarabawar ba. Har ila yau duk bayan yan dakiku sai tinanin abubakar yazo mata a rai.

Tana zaune tana karatun Al Quran aka turo kofar dakin nata aka shigo. Bata katse karatun ba sannan kuma bata waiga taga waye ya shigo ba har saida takai aya.

Juyawa tayi taga ya Aisha tsaye da alama daga office ta fito. Murmushi tayi sannan ta mike tace yaya kin shigo Ina wuni?

Lafiya kalau Zarah ya jiki? Alhamdulillah anti naji sauki sosai. Kinji wai next week official graduation ceremony namu ba?

Eh haka naji. Kinyi calculating GP dinki?

Eh anti nayi and it's a first class. Murmushi anti tayi tace Masha Allah gurin ki ya cika sai a daina stressing.

Dariya tayi taja dankwalinta ta daura a ka.

===============

Aisha!

Na'am Alhaji?

Na jima ina tinani ya za'ayi mu ciwo kan matsalar nan ta Abdallah. To jiya Ina zaune a kasuwa wani tinani yazo min a rai.

Toh namefa?

Abdallah ko auransa na farko saida akayi tamkar anayi sannan yace ga wacce zai aura. Sanin kanki ne Safiya badan inaso Abdallah ya aureta ba.

Akazo daga baya sukayi sukayi wannan rabuwar rashin albarka. Tun lokacin mata suka kara fita ranshi.

Yanzun ma dan na tirsasashi nace saiya kawo wacce zai aura shine yaje ya nemo wannan ya kawo.

Da ita, da tsohuwar matar tasa ban bancin kadan ne. And jira kawai yake nace wannan batayi ba ya cigaba da harkokin gabansa.

Next time idan an dauko maganar aure yace ai nine na kushe wacce ya kawo.

Eh Alhaji na fahimceka. Dama na jima da sanin ko wannan matar auren kawai yayi bawai dan yana sonta ba.

Tun Abdallah yana yaro Alhaji akan gane abinda yafiso da abinda kuwa yana ra'ayinsa ne kawai.

To yauwa kin gane inda na dosa. Shine nace na yadda zan aura masa wannan din daya kawo Amma da sharadin cewa saiya auri yarinyar dana zaba masa.

Nodding tayi kamin tace toh kai Alhaji hala akwai wacce kake sa ran hadasu? Kasan yaran yanzu basa son zama da kishiya ko kadan.

Murmushi yayi yace kwarai ma kuwa sannan har nayi magana da iyayenta kuma sun amince. Abinda ya rage muku shine lefe.

Alhaji yar waye? Na santa?

Kwarai kuwa hajiya Sa'adatu kin santa farin sani ma kuwa. Dan Yar gidan Alhaji Yusuf Bulama ce.

Badai kana nufin Fatima ba?

Eh ita.

Murmushi mommy tayi tace Masha Allah idan hakan ta faru ai kuwa Abdallah yayi sa'ar mata.

Hakane abba yafada yana jijjiga kansa. Suna zaune hakan saiga Abdallah ya shigo sanyeda bakar suit wannan karon.

Dukawa yayi ya gaishe dasu sannan ya zauna a kan carpet din ya kalla abba yace abba kace inzo.

Eh hakane nace kazo. Dama shawara mukayi da mommyn yara muka tsaida magana.

Na yadda na amince zaka aura ita farida amma sai idan ka yadda ka amince zaka aura yarinyar dana zaba ma sabida dukkanin alamu sun nuna cewa bakada ido wajen zaben matar arziki.

Daga kansa yayi ya kalla abba chan kuma ya soke kan nasa. Shikenan abba Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi.

Ganin yana shirin mikewa yasa abba cewa kaga dawo ka zauna bamu gama maganar ba. Akwai maganar lefe ka ishi kanka sabida haka idan kai zaka har hado ka har hado akai gidansu.

Bayan wannan ka shirya gobe jumua kaje gidansu ka gaida iyayenta sannan daga nan ka ganta dan abin ba da nisa zaa kaishi ba.

Ita kuma waccan ka gaya mata tafada a gida iyayenka zasuzo nema maka aurenta. Kallo dubu zaka iyayi masa amma bazaka gane meke a ransa ba.

Dadi ne? Takaici ne? Haushi ne? Batamasa rai maganar tayi ko akasin haka?

Jikinshi yayi wani pink pink red red ko ina. Insha Allah yace kamin yayi musu sallama ya fita.

Baya ya shiga yacewa driver dinsa ya kaishi driver. Harya isa gida ya shiga wanka ba abinda yakeyi inba kallan gina ba.

Tsaye yake ruwan shower din na dukan shi amma ba abinda ke replaying a kansa irin maganarshi da abba.

Ba idon zabar matar arziki ne dakai ba. Scoffing yayi kamin ya kashe shower din ya fita.

Yana fitowa wayarsa na fara ringing. Kallan sunan yayi ya daga.

Eh ya akayi? Ya tambaya cike da isa da gadara.

Dan karamin tsaki yayi a lokacin da ya tuna maganar abba. Kinaji?

Ki fada a gida su abba zasuzo neman auranki! Yayi maganar cikin halin ko in kula......

==================

Kwance take kan gadon anti Amina tana rusar kuka ba iyaka. Kallanta anti tayi tace Fatima bani Aron hankalinki nan.

Kallan anti tayi tana mai share hawayenta.

Bake da wannan bakin naki kika gaya min cewa baki expecting ki aure shi ba?

Eh!

To yanzu zaunawa zakiyi bakiyi aure ba? Shiru fatima tayi bata tanka ba. Murmushi anti tayi sannan tace to bude kunne ki kiji.

Meye sunan aminin abba?

Kallan anti tayi tace me kuma ya kawo wannan?

Ki amsani mana.

Umar Zaki. Masha Allah to meye sunan wanda abba yace zaki aura?

Abdallah.

To yanzu ki zauna ki gaya min meye sunan wanda kikeso?

Abdallah Umar Zaki! Kallanta anti tayi batareda tace mata komai ba.

Shiru itama Fatima tayi sai chan abun ya bigeta zare ido tayi "anti kar dai kice...eh shi dinne nima jiya nayi finding out cewa babban dan baba umar shine Abdallah.

But anti kinji fa tareda wata za'ayi.....kul Fatima karki soma wannan tinani. Nasan inda kwakwalwarki keso takai ki.

Karki kuskura so what Dan zai auri wata? Ko tazo a kanki zata zauna? Sannan kedin ba macce bace?

Bakisan yadda zakiyi ki janyo hankalinshi zuwa gareki bane? Duk mulkin namiji duk kyawonsa duk nasabarsa duk dukiyarsa Fatima to akwai macce a bayansa. Be that woman earn that place.

Allah ya baki kyau? Addini da uwa uba qira mai kyau. Fatima ko macce ta kalleki wallahi sai taso dama ace wannan jikin nata ne.

Use that shape to your advantage use that body and most importantly use the brain upstairs to your advantage.

Karki kuskura kishiya ta tsorata ki and mind you duk son da kike mishi karki kuskura ki furta mishi wannan kalmar taso har saiya buda baki ya furta miki ita.

Ki rike ajinki da matsayin ki. Na tabbata mata dubu sun gayawa Abdallah cewa suna sonshi and hakan baisa yaso su koya auresu ba kema idan kika furta ba shakka kinbi layin su bakida banbanci dasu.

FATIMAWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu