THIRTEEN

294 30 14
                                    

For those asking about the HKG I will attach a picture next time and if you are interested in buying you can go to Exclusive wears or exclusive fabrics same for the luxury veils.

Yanzu wannan abar ce zabin Abdallah? Ikon Allah. Farida irin matan nan ne da she's not thin and she's not curvy.

Ba wani shape bane da ita ba amma kuma bazaka kirata shapeless ba. Farace sosai tanada hanci mai kyau Amma kananan ido ne da ita and doguwace sosai.

Saidai duk tsawonta bata kamo Abdallah ba. Ba laifi tanada kyau Amma ko rabin kyan Fatima batayi ba.

Fatima najin idanta suna yawo a kanta amma tayi kamar batasan tanayi ba. Ajiye wayar yayi gefe.

Addua yayi sannan ya kallesu yace magana zan fada hadeda wasu dokoki bazan kuma sake mai mai tasu ba.

Kallan farida dake magana tayi.

Haba baby ya zakace ba masu aiki to wa zaiyi aikin part dina? Bazan iya ba wallahi saidai kayi hakuri.

Haka kawai kace bazan dauka masu yimin aiki ba. Wannan bazai yuwu ba.

Kallanta yayi a gadare yace da kina gidanku wake miki aikin?

A mama kance ta kallesa babe a kasuwa zakazo ka kunce mun zanina?

Kallan Fatima tayi kamin ta dauke kanta ta mayar gefe.

Zaki iya anfani da main bedroom din da main seating room yafada idansa kan Fatima. Nodding tayi still kanta na gefe.

Didn't I tell you idan Ina magana ki kalla idona ba?

Kallansa tayi tace yi hakuri Insha Allah baza'a sake ba.

Kallan farida yayi yace ke kuma ranar girkin ki you can use second bedroom and seating room. And you both can do two days each starting from Friday.

Addua yayi yana kaiwa karshe ta mike tayi part dinta bayan tace mishi saida safe.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Rufe kofar tayi ta sanya mata key sannan ta zauna kan kujera. Tinani ta komayi ranarda aka kawota gidan.

FLASHBACK

Tsaye yayi bakin gadon yana kallanta kanta a duke cikin alkyabbarta. Ajiye ledoji dake hannunsa yayi sannan ya zauna kusa da ita.

Janye mata hular alkyabbar yayi ya tsaya kallan fuskarta. Ya jima yana kallanta kamin yace kije kiyi alwala.

Mikewa tayi jiki a sanyaye ta shiga bathroom tayo alwala ta fito. Gefe ta tsaya kanta a kasa.

Nizan dauko miki carpet ne?

Kallansa tayi a ranta tana mamakin halin wannan bawan Allah. Wardrobe ta bude tagansu guda ukku ta dauka guda biyu ta shinfida.

Sallah sukayi suka gama tamkar malamin dake yiwa student oral exam a islamiyya haka ya koma mata tako Ina wurgo tambaya yakeyi.

Fatima kuwa zagewa tayi ta dinga bashi amsa. Tambayarsa ta karshe ce ta bata kunya tayi shiru ta dauke kanta.

Dauke idonsa yayi daga kanta sannan ya ajiye mata kayan dayazo dasu a dazu yace gashi nan na kine. And if you believe nine zanzo gurinki toh tun wuri ki chanja tinani tun kamin lokaci ya kure miki.

Tana kallo ya juya yabar dakin.

FLASH BACK ENDS

To yanzun itace ta bishi ko kuwa shi yaje gidanta ya janyo ta? Anya kuwa lokaci bai kure min ba? Me kunya da ajin nawa ya janyo min?

Yau a gaban idona wata ta kwanta jikin Abdallah. A gabana ta kira mijina baby. Kaiiiiiiio! Na fado. Faduwa ba Karama ba. Dole ta chanja zani.

Mikewa tayi da sauri ta shiga bedroom ta wuce toilet ta doro alwala. Fitowa tayi ta sanya hijab ta kabbarta sallah.

FATIMAWhere stories live. Discover now