FIFTEEN

261 22 7
                                    

Isa yayi ya zauna tafara serving dinsa. Previously kamshin tiraren tane ya bade part din Amma zamansa da few seconds tirarensa yayi dominating gurin.

Mixing kamshin turarukansu sukayi sai suka bada wani sassanyan kamshin daya bade gidan once again.

Kallan masar yayi data sanya a plate daya miya a cikin bowl kuma. Tana gama serving dinsa taja kujera ta zauna.

Kallanta yayi a lokacin yayi arba da kwalliyar data zuba. Haka kawai ya tsareta da ido yana kallo.

Gashinta daya fito ya kalla kamin ya dauke kansa yafara cin masar. Kanana kanana ne shi yasa ta zuba mishi guda hudu.

Cinyesu yayi sannan ya bude kular ya sake daukar wasu hudu ya cinyesu kamin yasha tea dinsa data hada mishi.

Hannunsa ya wanke sannan ya dauka tissue yayi drying nashi. Fatima kuwa ganin haka yasa tayi yunkurin yi mishi magana Amma ya rigata.

Bazaki ba kawai yace sannan ya fidda hundred dollars ya ajiye kan dinning din. Kallan flask din yayi ya daukeshi yayi tafiyarsa.

Binsa tayi da kallo without saying anything. Ita ji takema tamkar ta makeshi. Wato wannan ne ikon da namiji ba?

Knocking taji a bakin kofa hakan yasata isa tadan leka kanta taga waye. Ganin Bala driver dinshi tayi.

Hajiya Ina kwana?

Lafiya kalau.

Hajiya wai Alhaji yace a bada abinci akai mishi.

To bari Ina zuwa tace mishi sannan ta koma ciki ta buda kular taga masa hudu kawai ta rage. Maida masar tayi da miyar a cikin basket ta fito.

Bala alhajin yana ina?

Ya wuce dan yayi latti shine yace in kai mishi office.

To jeki idan na hada zan kira kazo ka karba.

Bayan ya wuce ta rufe part din ta koma nata. Masar data sanya a cikin medium kula ta bude ta zuba mishi guda ashirin a ciki ta rufe kular.

Bude miyar tayi ta kara mata yawa sannan ta kara nama ta rufe. Plates da bowls sai serving spoon ta sanya a cikin wani basket daban.

Farin hijab dinda take sallah dashi ta dauka ta sanya sannan ta sake fita tana isa part dinsa ta hango bala a gate.

Kiranshi tayi yazo ta mika mishi sannan ta shiga cikin part din. Kitchen dinda yadan baci ta gyara tayi wanke wanke sannan ta nufi store.

Cleaning supplies ta dauka tayi bedroom dan tana sa ran cewa yayi kura. Turus tayi ganin bedsheets din ya janye da alama an kwana a dakin.

Tsaye tayi tana tinani chan tayi shrugging shoulders dinta ta chanja bedsheets din zuwa wani all navy blue colored on da white touches chan ba'a rasa ba.

Bathroom ta shiga taga laundry basket dinsa cikeda singlets da boxers hadeda jallabiya guda ukku.

Hadawa tayi da zanen gadon ta nufi laundry room dake kusada store. Setting machine din tayi to ten minutes ya wanke underwear's dinshi sannan ta koma gyaran dakin.

Washing machine din nafara kara ta gane cewa ya gama aikinsa. Fidda kayan tayi ta sanya jallabiya din guda ukku ta sake setting dinsa for fifteen minutes.

Rinsing sauran tayi a cikin dayan compartment din tayi drying dinsu a cikin dryer sannan ta ajiyesu kan laundry table din.

She did the same ma sauran sannan ta koma ta karasa aikinta. Kallan ko ina tayi taga clean sannan ta koma laundry room.

Goge kayan tayi except zanen gadon data sanya cikin basket din kayan guga. Daukar kayan tayi ta nufi bedroom dinsa ta jerasu a wardrobe tareda sauran kayansa.

Sake duba bathroom dinsa tayi taga lallai ta wanke ko ina sannan ta rufe gidan tayi part dinta.

Tana shiga part dinta taji karar horn a cikin gidan. Lekawa tayi cause tasan maigidan baya horn idan ya dawo kuma ba lokacin dawowarsa bane.

Kallon gogaggar yar duniyar data fito cikin Honda civic din tayi. Matar farace ta nunawa a jarida amma kallo daya zakayi mata kasan bleaching ne.

Saukarda curtain dinta tayi ta koma ta zauna. Hollandia milk tasha tafara muraji'ar haddarta.

Tana cikin haka taji knocking. Mikewa tayi taje bakin kofar ta duba ta peephole taga anty Hadiza ce.

Bude kofar tayi tana murmushi tace anti sannu da zuwa. Shigowa anti tayi tareda yan mata biyu dake bayanta.

Drinks ta kawo musu hadeda snacks sannan ta zauna. Alhamdulillah tafara a ranta sabida jiya da dare ta gyara part dinta tsab sanin koda zata gama da part dinsa rana tayi.

==============

Zaune farida take da bakuwarta suna labari.

Ke wallahi kin bani mamaki yaza'ayi ki kyale kishiya tana yawo. Na dauka kina shigowa zakiyi waje da ita.

Kallanta farida tayi tace duka duka fa satina daya a gidan hafsat ai kya tsaya ko? Me kikeci na baka na zuba?

Batayi haramar barin gidan ba sai bayan la'asar zamanta a gidan akayi azahar har akayi la'asar Amma cikinsu babu wadda ta mike da niyyar tayi sallah.

Karki tsaya jiran komai farida wallahi ki azalzaleta da masifa karki yadda a zauna lafiya a cikin wannan gidan.

Naji mana hafsat sai kace bakisan wacece farida ba? Shiga motar hafsat tayi sukayi sai anjima sannan farida ta koma part dinta.

Tana shiga tayi kwance tana chatting a wayarta. Bata motsa daga gurin ba saida akayi magrib.

Bathroom dinta ta shiga tayo alwala ta kabbarta sallah. Nidai naga sai zuba sallah take ashe wai rankawa tayi daga azahar har magrib.

Second living room dinta ta shiga Amma naga guri wayam red carpet kawai ce a gurin sai shoe rack.

Bedroom din ta shiga shima dai duk shegiyar darin ce. Akwatunan lefenta ne a watse ko wace a bude.

Green din jallabiya ta dauka ta juya tabar dakin ta shiga nata. Bathroom ta shiga tayi wanka ta fito ta tsantsara kwalliya iya kwalliya.

Ba laifi ta kware a gurin makeup dan tayi kyau sosai. Abayar ta sanya da kyar ta bala'in kamata.

Murmushi tayi tace saidai ki nuna min shape badai iya kwalliya ba. Yau ranar girkin kice Amma Abdallah zai kwana da tinani na.

Gyalen abayar ta dauka da niyyar taje part dinshi ta tuna cewa ko taje ba'ayi isha ba so bai dawo daga masallaci na.

Komawa tayi ta zauna tana jiran tsammani.

Hello guys how have you been? It's me I'm back Hamdullah feeling better thank you for all your prayers. I've seen a lot of comments. praying for my health and a lot of messages as well. Thank you so much. I really really really appreciate it. I love you guys. Dahlia the new book, will the premiering in a while In Sha Allah. check it out. I'm sure you guys will be surprised to see this as today is not a Boston day, but I'll send it to give you a bonus as it has been a while since I posted and to show you how happy I am how grateful I am how thankful I am for your prayers.

FATIMAWhere stories live. Discover now