TWELVE

264 21 4
                                    

Kallan dinning dinsa yayi bayan ya dawo daga isha yaga wayam. Tabe baki yayi ya koma dakinsa ya dauka wasu makullai sannan ya dawo ya dauka jakkar yayi waje.

Mamaki sosai nayi ganin ya nufi side din Fatima. Ba kara mamaki ba saida naga ya sanya makulli ya bude side din.

Yana shiga kamshin tiraren wuta hadeda kamshin da takeyi a ko wanne lokaci ya bigi hancinsa.

Shiga palorn yayi ko Ina tsab tsab dashi Jin wani mahaukacin kamshi yayi yana tashi a kitchen wanda yasashi kallan gurin.

Maida idanshi yayi kan television sai alert dinda ya gani dazu ya fado masa a rai. There's a total of ten million in that account.

She will definitely use it for events and maybe some house renovations. Am I wrong? Amma na bata itace batayi anfani dashi ba.

Ko duka ta qona a part dinta bazasu siya set din palorn nan ba. Seventeen million on dinning set and four chairs.

Fitowa tayi da wata glass bowl sai sauri take. Ajiyewa tayi a dinning ta kalla kayan.

Kallanta yayi ya dauke kai. Sanye takeda wani matsatsen pencil trousers ya bala'in kamata exposing her a** and hips.

Farar baggy T-shirt ce a jikinta sai kanta dake sake. Komawa kitchen din tayi ta dauko basket red color ta fito.

Shan kasa tayi lokacinda ta ganshi zaune yana Kallan TV. Cije lips dinta tayi ta rike waist dinta tana mikewa.

Kallanta yayi ita kuma wannan haka Allah yayita da tsoro. Ina wuni?

Lafiya yace yanaci gaba da Kallan tv. A nan zakaci dinner?

Nodding kawai yayi hakan yaso ya qona mata rai amma ganin Abdallah nefa yasata komawa still rikeda kunkurunta ta dauko plate din ta ajiye glass dome din.

Well cooked steak ta ajiye a gabansa gefe Kuma mashed potatoes ne da vegetables. Komawa tayi kitchen ta dauko zobo data hada dazu da safe.

Cikin farin glass jug yake ta ajiye bayan ta zuba mishi cup daya. Ganin yafara cin abincin yasata shiga kitchen ta dafa indomie.

Bayan ta gama ta dawo ta ganshi yana cin abincin. Nesa dashi from the dinning taje ta zauna tafara cin indomie dinta.

Kallanta yayi ya kuma dauke kai ya karasa nashi abincin ya koma palo. Yana Kallan tv din tafara playing dayake tanada sensor.

Sauri tayi tayi pausing tv din da remote hakan yasa ya kalleta. Gyaran murya tayi tace na dauka you are not interested in star plus ne.

Bai dauke idansa ba kuma baiyi magana ba hakan yasa tayi playing hadeda cewa yi hakuri.

Nuna mata bag din yayi yace kayanki ne. ATM dinda ta ajiye kan dinning the second day da tayi mishi abinci ya ajiye mata.

Use this to get yourself what you want. Banga bukatar sake siyan kaya ba bayan na lefenki na nan instead of kayan fadar kishiya I will leave you with the money.

Take taji ranta ya bala'in baci amma kawai tace Allah ya saka da alkhairi and ya bamu zaman lafiya.

Ameen yace ya mike yayi tafiyarsa. Binshi tayi da kallo harya fita ya kulle kofar. Hawaye suka fara zubo mata masu zafi.

Daren ranar batayi bacci ba sallah ta kwana tanayi tana rokon Allah. Kukanta takaiwa Allah sannan hankalinta ya kwanta.

Ranar daurin auren part dinta cike yake da yan uwanta, danashi yan uwan ma da suke zuwa suyi mata jaje.

Tun safe take tsaye bata zauna ba har yanzu bayan azahar. Jin parking din motoci ya shaida mata cewa angon da tashi tawagar sun iso.

Ba wani tazara da isowarsu Rukayya ta kawo mata wayarta wai ya Abdallah ya kira. Sawa tayi a kunne tayi sallama.

Tana Jin yayar mutane a dayan gefen lokacinda yace Aisha na gidan?

Eh sunzo tun safe turo ta za'ayi?

Eh kice tazo kawai yace ya kashe wayar.

Neman aisha kanwarsa tayi ta kuwa ganta a palor na ukku tace kije yayanki na nemanki. Jan Rukayya tayi sukayi part dinshi.

Knocking sukayi suka shiga ciki. Kamshin tiraren wutar da part din Fatima keyi nashi part din keyi.

Tun kamin suzo Fatima ta sake tiraren part din sannan tayi setting abincin da komai tare dasu Aisha da Rukayya.

Zo nan yace batare daya kalla bayanshi ba.

Aa Abdallah na dauka uwargidance kamata yayi muyi mata jaje da Allah ya sanya Alkhairi.

Wani cikinsu yace kaji munafikin Allah idan tazo kalleku zatayi tace kune sanadin yi mata abokiyar zama.

Kallansu yayi akan me zaku ganta? Ganin matanka nakeyi ne?

Kallan Aisha yayi ya bata wata katuwar jakka ki mika mata kice ajiya ce saina tambayeta. Dakyar su biyu suka kama jakkar sukayi part din Fatima.

A jigace suka isa suna maida numfashi ya Hadiza da shigowar ta kenan tace ku kuma daga Ina?

Wallahi ya Hadiza ya Abdallah ne yace waimu kawowa anti Fatima wai ta ajiye mishi har ranarda ya bukata.

Neman Fatima sukayi tace suzo a bedroom dinta ta bude wardrobe dinta ta fidda suitcases dinda ke kasan abayas dinta dake hange tace susa a nan.

Rufe kofar tayi sannan ta rufe dakin. Kusan la'asar duka wanda ba close yake da gida ba suka watse.

A lokacin su rukayya, Aisha, latifa, ya khadija da sauran suka kama aka gyara gidan inda aka bata.

Gabadaya toilets dinta saida aka wanke na dakinta dayake a rufe wanda baa shiga ba shine kawai basu wanke ba.

Ana kusan magrib suka wuce gidajensu. Tana sallame sallar isha tayi shafai da wutiri sannan ta mike ta nade carpet dinta.

Tana cikin nade hijab taji dirar motoci da hayaniyar mata. Ba abinda suke inba habaice habaice ba.

Murmushi tayi lokacinda ta tuna maganar anti aisha ki bita a yadda tazo. Idan tazo da zaman lafiya a zauna lafiya idan kuma da tsiya tazo a tafka tsiyar.

Wannan dagani bada niyyar zaman lafiya tazo ba. TV ta kunna tafara Kallan wani film a studio universal.

Har yan kawo amaryar suka wuce bata daga daga inda take ba. Sai shadaya da rabi maigidan ya dawo shikadai.

Tun bayan magrib wani kololon bakin ciki yayi mata zaune a zuciya ta rasa meyasa. After twenty minutes taji wayarta na ringing.

Picking tayi tace hello! Kizo Ina jiranki.

Mikewa tayi ta kalla kanta a mirror. Wani farin HKG lace ne a jikinta a kalla zaiyi seven hundred thousand naira.

Anyi mishi dan uban sun dinkin doguwar riga wacce taji stones. Yanada touches of peach a jiki hakan yasa ta dauka peach luxury veil dinta ta yafa ta sake fesa tirare.

Wayarta ta dauka ta nufi part dinsa. Wannan karon sanye takeda fararen designer takalmanta na Yves Saint Laurent(YSL)

Sallama tayi ta shiga. Is koshi tayi zaune kan kujera sanyeda cream shaddar sa. Babbar rigar na ajiye a gefe.

Gaidashi tayi sannan ta zauna kan one seater dinda ke kallanshi. Jin motsi tayi a kitchen tana daga kai taga watar farar mata sanyeda wani farin material hannunta yasha bakin lalle.

Dauke idanta tayi ta dora kan center table din dake palorn. Farida kuwa zaunawa tayi kusada Abdallah ta wani shige mishi sai harare harare take.

Kallanta fatima tayi tace amarya sannu!

Yauwa farida ta amsa hadeda wani kwantawa Abdallah dake danna wayarshi.

Tsaki fatima tayi a ranta tace wai iskancin banza.

FATIMAWhere stories live. Discover now