Bintu tayi dariya sosai harda rufe baki tace " duk kyauna na kaiki ne?

"Ah wallahi kin fini, sai dai idan tsokanata zakiyi, ni dai ki bani labarin dan Allah, meya rabo ki da gidanku, garinku da k'asarku?

Gwauran numfashi Bintu tayi had'i da cewa " ke meya raboki da gidanku?

"K'addara...

Maryama tace tana k'ok'arin mayar da hawayenta kana ta d'ora da gidanmu babban gida ne iyaye,  'ya'ya da jikoki duk gidanmu d'aya..

"K'addara ta rabo ni da gidanmu da iyayena.

"Wacce irin k'addara..?

Cewar Bintu tana gyara zama...

"Bak'ar k'addarar so da makauniyar soyayya suka rabo ni da gida, daga nan Maryama ta kwashe labarinta tsaf ta fad'awa Bintu, daga Bintu har Maryama kuka sukeyi wiwi...

Cikin kuka Bintu tace " lalle kam kinsha gwagwarmayar duniya kema, kusan shigen k'addarar mu d'aya ce, ni k'addarar aure ce ta rabo ni da gida..

"Babana ya dad'e da mutuwa tun ina yarinya, wan mahaifinmu ya tattare gaba d'aya dukiyar ya cinye ya barmu a wahala nida mahaifiyata da k'anina,
ina da shekara goma sha hud'u ya kawo abokinshi yace dole saina aura, kuma matanshi uku 'ya'yanshi sun kai 30,
kowa a garin Marad'i yasan gidan da rashin tarbiyya da rashin zaman lafiya, kamar gidan karuwai kowa zaman kanshi yakeyi a gidan,
koshi me gidan bai isa a gidan ba, babu wanda zayyiwa magana ya saurareshi, dan baya iya ci da gidan,
kowa shiyake fafutuka ya ciyar da kanshi, idan kina da manyan 'ya'ya suyi talla,
'Ya'ya mata subi maza, 'ya'ya maza sun zama 'yan daba, ke in tak'aice miki labari duk inda kike neman gidan rashin tarbiyya gidan Lado yakai, amma kawu na ya kawo min shi a matsayin mijin aure bayan shima yana da 'ya'yan mata harda wad'anda suka kusa haihuwata basu da aure a lokacin...

Koda yazo da maganar da farko Mamana tayi kara, amma dataga abun bana k'are bane, saita aje k'ara a gefe ta zage zata kwatar min 'yanci amma a banza,
duk yadda Mamana taso ta hana auren Kawu na ya bugi k'asa yace bata isa ba ayya fita iko dani,
shawara Mamana ta yanke ta shigar dashi k'ara kotu amma dayake sun fimu farcen susa babu inda shara'ar takai,
dole muna ji muna gani kawu na ya karb'i kud'in auren da kud'ad'en lefe ya turmushe su ya d'aura min aure da Lado..

Ranar Kawu na yayi tsaye saida na tare a gidan Lado k'arfe d'aya na dare na tare a d'aki na da babu komai sai yaloluwar taburmar kaba shinfid'e ita kad'ai..

A ranar Lado ya rabani da budurcina, nasha bak'ar wahala duk da kasancewata yarinya k'arama Lado bai saurara min ba, ya zage iya k'arfinshi harda mugunta ma ya had'a..

Da buk'atarshi ta biya bai k'ara bi takaina ba, ya saka k'afa ya tsallake ni ya fice, nakai kwana uku a d'aki bana iya tashi, amma babu wanda ya kulani, balle a kawumin agaji,
harna fara wari saboda ban samu ruwan zafi ba, ga ciwo da azaba sun addabeni, hankalin Mamana yak'i kwanciya tunda aka kawo ni gidan Lado..

Gashi babu wanda zata tambaya taji yadda nake, dan haka ta shirya da kanta ta tafi gidan, ta shiga mummunan tashin hankali dataga halin danake ciki, bata tsaya bi takan kowa ba, ta d'auke ni sai asibiti, nasha jinya sosai wajen wata shida kafin na samu sauk'i,
tunda aka kwantar dani asibiti Lado baizo kosau d'aya ba, amma dan rashin kunya ranar da aka sallamoni yazo k'ofar gidan mu yayi tsaye wai yazo tafiya da matarshi.

Ba yadda Mamana ta iya dan anfi k'arfinta dole tabarni na tafi, ina kuka kamar raina zai fita..

Bazan iya fad'a miki irin rayuwar k'unci da rashin 'yancin danayi a gidan Lado ba, bai tab'a sauke hakk'i na dake kanshi ko guda d'aya ba,
kwanciyar aure kawai ya sani, duk sanda yake buk'atata yazo ya danne ni yayi abunda zayyi ya tashi, har na samu ciki, anan na gane Allah yana girma...

"Ba ci, ba sha, ga laulayin ciki, ga duk gidan babu me ce min ci kanki, da farko Mamana ke aiko min abinci kullum, Lado yayi tijara da tawatsimar nasi dole tasa Mamana ta dena aiko min abincin badan taso ba,
da naga zan mutu a d'aki  wuya ta sakani fitowa na fara kama musu aiki, ina yi musu aikatau d'in abincin da suke siyarwa,
inayi musu wanke-wanke da sauran ayyuka, basa biyana da ruwan kud'i, sai dai kullum zasu bani abinci sau uku a rana..

"A haka har cikina ya tsufa ya isa haihuwa, ko sau d'aya magana bata tab'a shiga tsakanina da Lado ba, tunda akayi aurenmu har yanzu,
iyakaci idan yana da buk'atata ya hayeni kamar dabbobi, koda cikina ya tsufa Lado bai dena kwanciya dani ba,
ya haye ni d'erere ya zage babu tunanin ina da ciki balle ya tausaya min..

Dayake yarinya ce ni akwai k'arancin shekaru yasa na fara nak'uda ban sani ba, sai da ciwo yaci k'arfi harya kwantar dani bana iya tashi,
kwanana takwas a d'aki ina nak'uda amma ba sauk'i ga Lado ya hana a kaini asibiti, a b'oye d'aya daga cikin matan Lado ta aika aka sanar da Mamana,
aiko ta bazamo kallo d'aya tai min, ta kawar da kanta had'i da fashewa da kuka ta rungume ni.

Jikinta na rawa ta kinkime ni, ta fito dani, a bakin k'ofar d'akin taga Lado ya raba k'afa ya kama k'ugu, cikin isa yace " ina zaki kai min mata?

"Ko kin manta tana da aure na akanta?

Cewar Lado yana turo hula gaban goshi zayyi rashin mutunci, Mama bata kulashi ba ta rab'a ta gefenshi zata wuce, yayi caraf ya rik'e hannun Bintu, Mama taja shima yaja,
ganin haka yasa Mama had'a hannayenta tana zubar da hawaye ta shiga rok'onshi had'i dayi mishi magiya, amma Lado ya bugi k'asa yace Allan fur baza'a fitar mishi da mata ko'ina ba, shi gidanshi ba'a zuwa asibiti haihuwa a gida ake haihuwa...

Mama na kuka kamar ranta zai fita ta zame ta durk'usa gaban Lado had'i da dafa k'afarshi ta shiga had'ashi da girman Allah, duk da Bintu tana cikin matsanancin zafin nak'uda sai da taji abin har cikin ranta,
ganin abinda Lado yayi yasa 'ya'yanshi da matanshi sukayi cali-cali dashi suka d'aga shi sama sukacewa Mama tayi sauri ta d'auki Bintu su wuce,
jikin Mama na tsuma ta tallafe Bintu suka fita, Lado nata wutsil-wutsil d'in kwacewa ya kasa yana zundumawa matanshi da yaran ashar..

Kwana d'aya a asibiti na haihu bayan nayi jijjiga na haifi 'yar ba rai, ta mutu tun a ciki, ni kuma na kamu da cutar yoyon fitsari....

***********************

*To masu karatu labarin Bintu labari ne me zaman kanshi, idan baku manta ba na tab'a fad'a muku shi a cikin littafina, wanda nace mace d'aya tana auren Maza bakwai kuma kowanne da k'addarar da take raba su, wasu daga cikinsu ma rayuwarta suke nema sunan littafin*
'''NISAN KWANA..'''
*ku biyoni bashinshi in Allahu zan rubuta muku shi wata rana*

*To kada aji na fad'i d'an gutsuren labarin Bintu (NISAN KWANA) wata ta d'auka ta juya min labari, dan an saba d'aukar min labari ana juyawa ko sunan labari, duk ina kallanku ina kuma sane daku*

Bayan Bintu ta gama bawa Maryama labarinta tsaf, Maryama d'auke wuta tayi dan taji abinda yafi nata, taji k'addarar data girmewa tata, taji HALIN MAZA, taji RASHI TAUSAYI DA IMANI na wasu mazan, ita kukan ma yafi k'arfinta, ashe k'aramin abu akewa kuka, lallai labarin Bintu yana cike da abubuwan da suka girmi tunani ya iya tunanowa..

"Lallai Bintu kin jigatu a hannun maza, kuma kinga rayuwa, babu irin k'addarar da baki gani ba, haka maza suka rink'a yin cali-cali da rayuwarki?

"Babu wanda yaja miki sai kawonki, Allah ya had'a shi da masifar datafi wacce ya jefaki a cikinta, murmushi Bintu tayi me kyau had'i da cewa " Allah ma ya riga ya had'ashi da ita.

"Ban gane ba..?

Cewar Maryama, basarwa Bintu tayi tare da mik'ewa tana cewa " tun d'azu Mania ta turo muje kin san idan bamuje ba akwai matsala, kafin Maryama tayi magana Bintu ta fice..

Maryama tabi bayanta da kallo tasan akwai abubuwa da dama data b'oye mata a labarinta, tasan ba komai da komai ta fad'a mata ba..


*JIDDARH...* ✍🏻

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now