"Ni fa bance ban san Yaya Yuraam ba, ina dai kuje mana gaba ne.

"Kinji nace miki wani abu ne?

"Ko kinji nayi miki magana?

"Zab'i ya rage naki, kowa abinda yaga zai fishsheshi yake yi, nima iyaye na basuyi min auren dole ba, akan me ke zanyi miki?

K'ofa Mama ta nufa zata fita Maryama tayi saurin fad'awa jikinta had'i da fashewa da kuka tana cewa "dan Allah kiyi hak'uri ki yafe min Mama kada wannan fishin naki yayiwa rayuwata illa.

Sosai zuciyar Mama tayi sanyi, jikinta ya saki.

"Kiyi hak'uri Mama zan aure shi, ai d'an uwana ne.

A hankali Mama ta kamata suka zauna saman kujera ta tallafo fuskar Maryama cike da tausaya tace " bakiyi min komai ba Maryama,
laifinki d'aya dana hanaki yin magana gaban mutane kikayi, meyasa ni ina matsayin mahaifiyarki kika kasa zuwa ki sanar dani damuwarki?

"Me yasa baki fara shawartata ko Ummanki da sauran 'yan uwanki kafin ki zartar da komai ba?

Cikin muryar kuka tace " nayi kuskure kiyi hak'uri Mama ban k'arawa, kuma zan auri Yaya Yuraam, zanyi duk yadda kuke so.

Hawayen dake zubowa saman fuskarta Mama ta goge mata tana fad'in " a'a nima ba'ayi min auren dole ba, kema bazan matsa miki ba.

"Wallahi Allah ban tab'a jin k'in Yaya Yuraam ba.

"Ban tab'a jin bana sanshi ko wani abu cikin raina game dashi ba.

"Ina yi mishi alk'alanci ne bisa halayyarshi, nasan babu wani namiji dazan samu sama dashi a fad'in duniya tunda shine zab'inku.

"Kin tabbatar idan kika aure shi baki matsa kanki ba, baki saka rayuwarki cikin k'unci ba?

"Kai ta d'agawa Mama tana murmushi.

"Ni inbanda abun Maryama ina abun k'i ga kwallon k'afa?

"Ni banga ta inda hakan zai shafi zaman aurenku ba, Umma ta fad'a tana shafa kanta, ta d'ora da " kina ganin d'ana kyakkyawa san kowa k'in wanda ya rasa namijin duniya, abun nema ga kowacce mace.

Gaba d'aya aka saka dariya, Maryama ta rufe fuskarta da tafin hannayenta tana dariya, ta tashi zata ruga Faji ta rik'ota tana gad'in " zo nan munafuka ina zaki?

"Ana so ana kaiwa kasuwa, ta turo baki tana fad'in " gwara ni bamai tsoron mace zan aura ba, wanda yake in ina a gaban matarshi, Baakura ya jefeta da filo had'i da mik'ewa yayi kanta yana cewa " zanci gidanku Maryama tayi waje da gudu tana dariya.

Tana jinta wasai amma ba sakayau ba, tayi farin ciki sosai da shiryawarta da mahaifiyarta da kuma ran mahaifinta da zata faranta,
amma ta rasa dalilin dayasa zuciyarta keyi mata nauyi, ta rasa dalilin yasa take jin wani abu a zuciyarta data rasa menene ta kuma kasa fassarashi.

Juyi tayi saman bed tana fad'in Ubangiji ka samamin mafita ka kuma yi min zab'in alkhairi, dan har yanzu tak'i yarda da abunda mutane ke cewa na tana san Yuraam.

Zuciyarta tak'i gaskatawa da hakan, tak'i yarda da amincewa kan da gaske tana san shi, ita dai tasan bata k'inshi.

Juyawa ta kuma a karo na biyu karaf idonta ya sark'e cikin nashi, rolling idonta tayi danta tuna da bata rufe k'afa, da sauri ya k'araso inda take yana fad'in " meke damunki Maryama naga duk kin rame?

Ya fad'a yana bin jikinta da kallo.

"Bakomai. tace a tak'aice.

"Maryama...!

Ya kira sunanta a kasalance kana ya d'ora da fad'in.

"Bazanyi miki dole ba, bazan tilaski aure na ba, bazan matsa ki ba, nasan dai ina sanki, kuma so na gaskiya nake yi miki, so na tsakani da Allah wanda ba algus a cikinshi.

"Zan iya hak'ura dake matuk'ar hakan zai  samar miki farin ciki.

Idan har aurena zai zama takura da cutarwa ga rayuwarki na hak'ura dake Maryama, zan iya sadaukar da soyayya dan samun salamarki Maryama.

"So da yawa muna rasa abunda muke so, haka muna samun abinda muke k'i, na hak'ura Maryama, na hak'ura da aurenki, ya k'arasa maganar muryarshi na shak'ewa.

Bai jira abinda zatace ba yayi hanyar fita, cikin nutsuwa ta mik'e zaune.

"Yaya Yuraam.

Ta kirashi cikin sanyi a nutse.

A sanyaye ya juyo yana fuskantarta fuskarshi d'auke da sassanyan murmushi, bayyi magana ba illa ido daya kafe ta dashi.

Ido itama ta zuba mishi tana kallan kwayar idonshi tana san gano wani abu amma ta kasa, cikin ranta tana fad'in " YAUSHE ZAN SAN SO?

"YAUSHE NE ZAN FARA SO?

"WAZAN FARA SO?

"WAZAN BAWA SOYAYYATA TA FARKO?

Azahiri kuwa murmushi ta k'ak'aro tana cigaba da kallan kwayar idonshi dake sark'afe da abubuwa da dama tace.

"Kayi hak'uri da duk abinda ya faru Yaya.

"Ban rik'eki da komai ba, ya fad'a yana murmushi.

Sai da ta d'anyi jimmm! kana ta sauke numfashi tace " Yaya Yuraam na yarda da aurenka.

"Na yarda na amince zan aureka.

Baki ya bud'e yana kallanta while yana murmushi, idonshi kanta yama rasa abinda zayyi, juya mata baya yayi had'i cusa duka hannayenshi cikin sumar kanshi.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah nagode maka.

Abinda Yuraam keta maimaitawa kenan.

"Ina zuwa!, yace yana fita harya kai bakin k'ofar fita ya juya ya dawo daf da ita yana sakar mata shu'umin murmushi daya shan banban dana koyaushe.

"Thank you so so much.

"Nagode miki sosai Allah saka miki da alkhairi.

Guntun murmushi tayi mishi batare datace mishi komai ba.

"Bari naje yiwa Abba babban albishirin.

Kanta kawai ta iya d'aga mishi, ya juya ya fice tabi bayanshi da kallo.

"San kai, bai tambayeni komai akaina ko zuciyata ba, ta kanshi kawai yake.

"Mafita da samawa kanshi salama kawai yake k'ok'arin yi banda ni.

Rana bata k'arya haka sannu bata hana zuwa duk abinda aka sakawa lokaci zaizo kamai daren dad'ewa.

Ana ta shirye-shiryen biki, kowa yayi busy a family musamman da yau Alhamis gobe juma'a d'aurin auren yara goma a family maza biyar mata biyar.

Wasu na cikin matsanancin farin ciki, yayinda wasu ke cikin bak'in ciki wasu kam 'yan i don't care ne, to Kellu tana cikin jerin masu matsanancin bak'in ciki dan sai da akasha gwagwarmaya da ita, dan dai ba yadda ta iya da Bugaje's ne yasa dole ta shanye wasu abubuwan.

Su Maryama kam 'yan  tsaka-tsaki ne, bata farin ciki haka bata bak'in ciki bata tattare da damuwar komai, amma bata mugun farin cikin nan da fara'a irin ta amare, an sha k'unshi ja da bak'i, an yarfa k'ananun k'itso yadda kasan da allura aka tsaga kun san Kanuri da ado da kamshi ba sai an fad'a muku ba.

Haka kun san Maryama nada Natural Virgin hair, gashinta irin me cukus d'innan ne, wanda ba'ayiwa shamfo, ga bak'i ga tsayi ga cika da yawa.

Washe gari juma'a bayan an idar da sallar juma'a mutane da dama wanda bazasu lissafuba suka shaida d'aurin auren Baakura da Faji, Kolo da Aisata, Fanne da Gambo, Fanna da aji, Yuraam da Maryama Bukar Bugaje.

Me shela yana kwala sanarwar an d'aura auren  Maryama dake zaune ta lumshe ido tana jin wani nauyi na baibayeta.


*JIDDARH* ✍🏻

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now