55&56

319 26 5
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    55&56

           Alhaji Kabeer cikin wani irin yanayi ya koma cikin ɗakinsa nadama da dana sani cike da zuciyarsa, wani ɓarin na daga cikin zuciyarsa ne ya ce, " Ka bayyana duk wani abu da kasan kun aikata shi kai da abokan yinka ko kwa samu ku samu kwanciyar hankali " ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin irin tsangwamar da zai fuskanta muddin duniya taji irin taɓargazar da suka aikata, ɗayan ɓarin zuciyarsa ne ya ce, " Taya zaka tona asirin kanka da kanka wannan ma aya kamar ka ɗauko wuƙa da hannunka ka daɓawa cikinka ne, karka manta kaifa babban mutum ne a ƙasarnan kana da tarin masoya haka nan kana da tarin maƙiya, idan kayi haka ka bawa maƙiyanka damar cin karensu babu babbaka akanka dan haka kaja bakinka kayi shiru tunda ba kai kaɗai ka aikata ba " shi kaɗai yake ta saƙa da warwara acikin zuciyarsa har ya samu yayi ruƙo da shawara ɗaya wacce yaga itace mafi dacewa agareshi.

*WASHE GARI*

        Kamar yanda yake a rubuce litinin ne ya kama ranar da Za'a ƙara sauraren ƙarar Alhaji Kabeer da Iyalan marigayi Alhaji Abdurrahman suka shigar da ƙara, kamar kullin kotun cike take da mutane Alƙali da lauyoyi kowanne yana mazauninsa daga cen wajen kotun mutane ne daga ko'ina na sassan cikin birnin kano, ƴan jarida da mujallu zagaye suke kowa na shirin kota kwana na samun damar naɗar muryar wanda ake ƙara zuwa waɗanda suke ƙarar.

         Magatakarda ne ya miƙe tsaye yana karanto ƙunshin ƙarar su Alhaji Kabeer bayan ya gama ya miƙawa Alƙali file ɗin ya koma mazauninsa, Alƙalin buɗewa yayi ya ɗan duba headlines ɗin sannnan ya rufe ya juyo ga Lauyoyin masu ƙara da lauyan wanda ake ƙara ya ce, " Zamu fara da Lauyan masu ƙara Br Ahmad ko ka shirya? "

     Miƙewa tsaye Br Ahmad yayi cikin girmamawa ya ce, " Ashirye nake ya mai shari'a " kotu tana saurarenka " cewar Alƙali.

     Gyara tsayuwarsa yayi ya fara magana, " Kamar yanda aka sani nine lauyan marigayi Alhaji Abdurrahman dan haka zan fara gabatar da hujja ta farko a yau, idan Malam Saminu yana kusa kotu tana san ganinsa " Dattijon na shirin tashi yaji jikinsa ya sandare wani irin sanyi na shigarsa daga nan bai sake sanin mai yake faruwa ba, wani dattijo ne ya taso mai siffar Malam Saminu ya je ya shiga cikin gurin da ake tsayawa domin bada shaida.

     Lauyan ne yace masa, " Mlm Saminu  munaso muji cikakken sunanka da kuma matsayinka agidan wannan marigayin " gyara tsayuwa Dattijon yayi yace, " nidai Sunana Malam Saminu kuma ni mai gadi ne agidan Alhaji Abdurrahman na shafe shekara goma ina gadi a gidansa "

      " Ranar da aka kashe mai gidanka kana ina ranar? kuma waye yazo kuma da wane irin yanayi ya shigo? " Br Ahmad ya tambaye shi, Malam Saminu ya cigaba da bayani, " Ina zaune a mazaunina wato bakin ƙofa sai naji anata knocking, ina buɗe ƙofa a hassale naga ya shigo yana huci ni da sauran ma'aikata muna masa sannu da zuwa bai tanka mana ba kawai ya shige ciki bayan wani lokaci naga ya fito da hanzari sai muka ji ihun kuka da kururu, nida sauran masu aikin muna shiga muka samu marigayi kwance ba rai cikin jini " Br Ahmad yace, " Malam Saminu baka gaya mana waye ya shige ka a bakin gate ba duba da kotu tana amfani ne da hujjoji " Malam saminu juyawa yayi gurun Alhaji Habibu yace, " Gashi cen Alhaji Habibu " gaba ɗaya idanu ne suka koma kan Alhaji Habibu, Alhaji Habibu najin haka sai da hanatar cikinsa ta kaɗa ya haɗiye wani irin yawu mai ɗaci, hatta Alƙali sai da ya ɗago da kai ya kalli gurin da yaga Malam Saminu ya nuna zame glass ɗin idanunsa yayi yace, " Malam Saminu Kotu ba gurin wasa bace ka kiyaye " shi kansa Br Ahmad mamaki ne ƙarara akan fuskarsa saboda yasan ba haka sukayi da Malam Saminu ba kafin zaman kotun yana cikin tunani karaf yaji Mlm Saminu ya cigaba da cewa, " Ya mai shari'a ba wasa nake ba da gaske nake idan ma ana tantama za'a iya kiran shi Alhaji Habibun ya faɗa da bakinsa " Alƙali da kansa ya ce Alhaji Habibu ya fito, jiki ba ƙwari Alhaji Habibu ya yunƙura ya fito Malam Saminu ya fito daga ciki shi ya shiga, Alhaji Habibu tunda Malam Saminu ya fito jikinsa ya bashi akwai wata a ƙasa, cikin karyewar zuciya ya ce, " Assalamu alaikum nidai sunana Alhaji Habibu kuma ni Abokin marigayi ne da shi Alhaji Kabeer wanda ake zargi " Alƙali ya ce masa, " Shin kaji mai wancen bawan Allah ya faɗa game da kai muna san jin ƙarin bayani daga bakinka "

ASEELA COMPLETEOn viuen les histories. Descobreix ara