9&10

457 36 2
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/L7dj60ptcAV3Oe1X6hAyBT

   

                    9&10

          Tafiya suke amma Alh Kabeer banda masifa ba abinda yakewa Driver cikin tsananin tashin hankali yake mata sannu yana kuma maida hankalinsa ga Driver yana azalzalar sa har suka ƙarasa asibitin da ke kan titin Alu avanue road, da sauri nurses ɗin suka tarbi Hjy khaleesat da ke cikin mawuyacin hali, DR Khaleel da sauran Doctors haka suka rufu akanta domin ganin sun ceto rayuwarta musamman yanda suka ga jini na zuba daga jikinta abun ya matuƙar ɗaga musu hankali, allura suka yi mata sannan suka ɗaura mata ruwa haka suka dinga zuba mata ruwan allurai dan ganin jinin da yake zuba ya tsagaita, sun shafe sama da minti talatin akanta sannan Allah ya taimakesu suka shawo kan matsalar, Alh Kabeer dake bakin corido banda safa da marwa ba abinda yake, abun duniya gaba ɗaya ya tattaru ya sashi a gaba, tunanin halin da ta ke ciki yake, gashi yaje shiga yafi a irga sun hanashi shiga, yana nan yana kaiwa da komowa DR. Khaleel ya fito agajiye fuskarsa sharkaf da gumi, ragowar ma'aikane suka biyo bayansa daka kallesu ka san sunsha aiki kafin su fito, axabure Alh Kabeer ya tambayi Dr. " Dr. ya jikin matata awane halin take ciki??? yaya cikin jikinta hope there is no any problem, pls Dr say something ko inshiga inganta ne? " murmushi Dr Khaleel yayi sannan ya ce, " jikinta da sauki amma inasan ganin ka, mu ƙarasa office ur Exellency " yana gama faɗa ya sa kai ya wuce, gaba ɗaya jikin Alh Kabeer yayi sanyi fargabar sa abunda Dr zai gaya masa, jiki ba ƙwari yake ɗaga ƙafafunsa ahankali har ya ƙarasa cikin office ɗin Dr.Khaleel.

       Zame glass ɗin idanunsa Dr yayi yana goge fuskarsa, Alh Kabeer zama yayi ya zuba masa idanu yana sauraron abinda zai fito daga bakinsa, kallansa Dr Khaleel yayi ya fara magana, " Alhamdulillah  Ur Excellency mun samu nasarar shawo kan matsalar amma mai ya faru da ita haka har yasa ta shiga cikin irin wannan condition ɗin??? " ya ƙarasa maganar yana zubawa Alh Kabeer idanu, daɗi yaji har cikin zuciyarsa sai dai kuma mai zai gayawa Dr? jim yayi yana nazari sai cen ya ɗago fuskarsa cikin damuwa ya ce, " dawowa ta daga offfice ba jimawa sai aka kirata awaya ake sanar da ita rasuwar wata aminiyarta, to shi ne fa ta tsinci kanta acikin wannan halin " jinjina kai Dr yayi ya ce, " gaskiya jininta ya hau sosai sannan tana buƙatar karin jini, kuma baza mu bari ta haihu da kanta ba sai dai muyi mata CS saboda gudun afkuwar wani problems ɗin " bakin Alh kabeer har rawa yake yana faɗin, " duk abinda ya dace ayi Dr nidai fatana karna rasa matata da abinda yake cikinta, dan Allah Dr ka taimaka mun dan Allah karka bari na rasa su " ya ƙarasa maganar yana riƙo hannun Dr Khaleel kamar zai yi kuka " tausayinsa ne ya kama Dr ganin  Babban mutum kamar Alh Kabeer ya na irin wannan magiyar, cikin nuna ƙwarin gwiwa ya ce masa, " Alh Insha Allah zamuyi iya bakin ƙoƙarinmu wajen ganin munyi komai yanda ya kamata, amma Alh rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah " jikin Alh kabeer ne ya ƙara sanyi jiki ba ƙwari ya ce, " shikenan Allah sa ayi komai cikin nasara " Dr Khaleel ya amsa da,, " Aameen " Alh Kabeer tashi yayi ya fito gaba ɗaya zuciyarsa ba daɗi, kai tsaye ɗakin da take ya shiga tana kwance fuskarta tai fayau sai sauke numfashi ta ke ahankali, kujera yaja ya zauna agurunta yana ƙare mata kallo cikin tausayi, azuciyarsa yana dana sanin sanar da ita maganar da janyo musu wannan tashin hankali.

       Wayarsa ya ɗaga ya kira Inna furaira ya sanar mata halin da ake ciki sannan ya bata umarnin tahowa, yana gama waya da ita ya kira Alh Abubakar Yayan Hjy Khaleesat cikin girmamawa ya ɗauka da sallama yana faɗin, " lalala Ur Excellency da kansa Barka da wannan lokacin " gajeren murmushi Alh Kabeer yayi sannan ya ce, " barka dai, dama Khaleesat ce muke asibiti ba lafiya amma karka sanar da su Hjy Yaya " cikin tashin hankali ya ce, " Subhanallah gani nan zuwa " daga haka katse wayar yayi, shima Alh Kabeer ya cire wayar daga kunnensa yana maida kallansa kan Hjy Khaleesat dake kwance bata san abinda yake faruwa ba.

       Bayan wasu mintuna Inna Furaira da Alh Abubakar kusan lokaci guda suka ƙaraso jin bayanin da Alh Kabeer yayi musu yasa duk jikinsu yayi sanyi, sai dai bai bayyana musu dalilin faruwar ciwon nata ba, cikin damuwa Alh Abubakar ya ce, " ikon Allah shi yasa mai rai ba abakin komai yake ba, ɗazun nan fa muka rabu da ita lafiya ƙalau amma kaga yanda Ubangiji ya nuna ikonsa, Allah ya bata lafiya Ubangiji yasa ayi aikin cikin nasara " gaba ɗaya suka Amsa da Ameen.

      Suna nan zaune bayan wasu awanni har ta farko sai dai Alhamdulillah jikin nata yayi kyau sosai, ba abinda yake damunta sai ɗan ciwon kai duba ta nurses suka shigo suka ƙarayi bayan wasu mintuna shima Dr ya shigo yayi mata gwaje-gwaje da dube-duba, acikin duk abinda yake buƙata ya ga komai succecfully.

          Kwanan Hjy Kaleesat biyar a hospital akayi mata aiki ranar Talata aka ciro mata yarinyarta kyakykyawa gwanin sha'awa, murna gurin Exellency abun sai wanda ya gani saboda bakin sa gaba ɗaya yaki rufuwa, Jaririya da mamanta suna cikin ƙoshin lafiya, sai alokacin ur EX ya dinga kiran mutane yana musu albishir aykuwa murna gurin ƴan uwa da abokan arziki baya faɗuwa, kafin kace kwabo hospital ɗin ya zama kamar gidan biki daga harabar hospital ɗin jerin gwanon galla-gallan motoci na alfarma ne suke ta parking, ta ko'ina mutane shigowa suke ana taya ur Ex munar samun ƴar da aka daɗe ana jiran isowarta ƴa ɗaya tilo agurin tsohon Gwamnan jihar Adamawa DR.KABEER MUHAMMAD LAMIƊO.

           Tun lokacin da aka ciro jaririyar ko kaɗan batayi kuka ba Abinda ya sanya su cikin damuwa, shiyasa ma basu bayar da babyn ba suka wuce da ita danyi gwaje-gwajen da ya kamata, sai dai duk binciken su babu wata matsala da suka ci karo da ita hasalima sai hannu take sawa a baki ta na neman abinci, dawo musu da ita wata nurse tayi aykuwa nan aka shiga ɗaukanta hotuna kala-kala, masu posting ta Whatsapp nayi masu yi a Instagram suma suna yi haka ƴan uwa da abokan arziki suka nuna farin cikinsu akan wannan kyakykyawae jaririya.

       ALH ABDURRAHMAN UBA abokin Alh Kabeer ne yama fi ƙarfin aboki sai dai mu kira shi da amini, bayan kowa ya watse suna zaune su biyu ya kalli abokin nasa ya ce, " Nifa ina cikin damuwa mutumina wallahi jiya a airport na ci karo da Inna Larai karka ga yanda hankali na ya tashi abun mamakin ma kuma jirgin dana sauko itama acikinsa ta fito, maganar gaskiya jiya ko baccin kirki banyi ba dama dan kana ji da fargabar Hjy Kaleesat shi yasa tun jiyan ban sanar da kai ba " tunda Alh Abdurrahman ya fara magana jikin Alh Kabeer yayi sanyi wata zufa ta fara keto masa, yana shirin bashi amsa Inna Furaira ta loƙo gurunsu cikin girmamawa ta na kiransa ta shi yayi ya ƙarasa ciki, idanu ya zubawa jaririyar cikin tashin hankali ya ce, " meye wannan nake gani kamar jini a idanunta me ya faru da ita? ke me kika yiwa gudan jini na?? " ya ƙarasa maganar yana watsawa Inna Furaira manyan idanunsa, jikinta sai ɓa ri yake kamar ta saki futsari agurin ta fara magana, " Allah ya taimake ka wlh ba abinda nai mata kuma ka tmby Hjy......... " katse su Hjy Kaleesat tayi cikin damuwa, " Ur Ex ba abinda Inna Furaira ta mata hasalima ahannuna take tana shan Mama sai kawai sai ji nai ta fashe da matsanancin kuka amadadin  naga hawaye sai gani nai jini na gangarowa daga idanunta " zaro idanu waje yayi ya na furta, " Serious??? " gyaɗa kai Khaleesat tayi hawaye na gangarowa daga idanunta.

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now