49&50

353 19 8
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    49&50

          Motsa bakinta take niyyar yi domin karanta addu'a amma wani irin nauyi taji yayi mata wata dabara ce ta faɗo mata cikin zuciyarta ta fara karantar Ayatulkursiyyu, jitai bakinta na motsi aykuwa ta cigaba da karantawa bakinta na biyawa, da ƙarfin gaske ta samu ta hamɓare mutanen da ke riƙe da ita cikin ikon Allah ta samu ta fisge ɗan gajeren mutumin dake riƙe da wuyanta, cikin ɗaukaka murya ta cigaba da karanta Addu'ar da duk tazo bakinta, da sauri taga suna ja da baya tana kuma tunkararsu suna matsawa ganin haka yasa ta cigaba da binsu da suka ga zata cimmusu take suka fara tashi sama kamar wasu tsintsaye suna komawa kan wata bishiyar kuka dake cikin maƙabartar, firgigit Inna Furaira ta tashi  bakinta ɗauke da Addu'a da take biyawa acikin mafarki, tana buɗe ido su Rakiya tayi tozali dasu agefenta sunyi carko-carko, gaba ɗaya jikin Inna Furaira jiƙe yake da gumi ta ko'ina goge zufar goshinta takeyi sannan ta fara tunano mafarkin da tayi da irin artabun da sukayi, kallan su Binta tayi gaba ɗaya a tsorace suke dob ta kauda tsoron dake garesu ta kalle su ta ce, "  Ku kuma lafiya naga duk kunyi zuru-zuru a cikin tsohon daren nan ? " Binta ce ta fara magana, " Wallahi Inna kece kika tashe mu jin kina faɗan wasu irin maganganu ƙasa-ƙasa sai kuma mukaji kina ta Addu'o'i da ƙarfi ga jikinki sai wata irin karkarwa yake " Ajiyar zuciya Inna Furaira ta sauke ta ce, " wallahi wani mummunan mafarki nayi amma insha Allah alkairi ne ku koma ku kwanta " aɗan ɗarare suka bi gefenta suka kwanta amma da alama babu wanda ya koma bacci, Inna Furaira tashi tayi ta faɗa banɗakin su dake cikin ɗakin ta ɗauro Alwala ta gabatar da sallah tana kai kukanta gurin Ubangiji.

         Kaleesat tun bayan da ta goya Aseela cikin zuciyarta banda saƙe-saƙe ba abinda take yi, fargaba da tsoro babu wanda bai mamaye ta ba musamman da ta tsaida tunaninta ta tuno duk abubuwan da ke faruwa, ganin haka ne yasa ta ɗaura Alwala ta gabatar da sallah tana miƙa lamarinta gurun Ubangiji bawa Allah mafita akan abubuwan dake faruwa cikin rayuwarsu.

        Bayan tashin Aseela daga bacci tsoro ne ya hanata sake bata Nono saboda har zuwa lokacin bai daina mata zugi ba, madara ta haɗa ta bata nan da nan kuwa ta karɓe ta zuƙe ta, abunda ya bawa Kaleesat mamaki lokaci guda Aseela ta shanye madarar wacce ada sai dai tayi mata sha uku ko biyu, amma sai bata kawo komai ba saboda taga wuni guda bata wani sha nono sosai ba, sake haɗa mata wata madarar tayi rabin fida🍼nan ma baije ko'ina ba ta  zuƙe shi ta shanye, Kaleesat idanu ta zurawa Aseela tana mamakin irin wannan ci nata dan bata taɓa cika cikinta irin na wannan ranar ba.

          Cikin dare bayan Kaleesat ta kwantar da Aseela akan gadonta itama komawa kan nata gadon tayi ta kwanta, bayan ƙafa ta ɗauke Aseela wata irin girgiza tayi lokaci guda ta koma wani zandareren ƙwarangwal, juyawa yayi ya kalli Aseela da ke baccinta hankali kwance, zaƙwa-zaƙwan hannu ya miƙa cikin gwamammiyar murya ya ce, " ZAN CIGABA DA ZUƘAR JININ FANSA TA RUHINKI KAFIN TABBATAR DA ƊAUKAN FANSA A TSAKANINKU " hannunsa ya kai jikinta ta niyyar ƙara zuƙar jininta kamar yanda ya fara, wani irin hucin wuta yaji saboda addu'ar data tofe jikinta dasu kafin kwanciyarta, cikin takaici ya janye jikinsa ya fice daga ɗakin sannan ya sauko ƙasan gidan, kai tsaye store ɗin gidan ya wuce, yana kallan kayan Abincin ciki ya fara furta, " DURGU DARGIN GINSAR " lokaci guda gaba ɗaya kayan abincin suka zuƙe shinkafa, taliya, macaroni, indomie, cus-cus, mai, maggi, da dai sauransu gaba ɗaya komai ya ɗauke sai buhunna da kwalaye mayuka kuma sai jarkokin danginsu kayan Tea kuwa sai gwangwanaye, wasu Food Flasks ya hango masu launin Ja take suma ya ƙarasa gurin ya wartosu ya hau taunawa lokaci guda ya cinye su, haka ya dinga bin duk wasu kayayyaki na kitchen ɗin danginsu kofuna, plate, robobi da cokula masu launin Ja yana cinyewa tass, sai da ya gama cinye su lokacin kitchen  ɗin gaba ɗaya ya zama shara-shara babu wasu kayan kirki aciki sai burbuɗin kayan abinci dana kwanuka aƙasan tiles ɗin.

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now