END

381 36 10
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*
   

                    99&100
     🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

       Hajiya Khaleesat gudu take kamar zata tashi sama har ya ƙasara ƙofar gidan Iyayenta, lokacin da taje a bakin gate ta tsaida motarta ta kifa kan akan sitiyarin motar tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, su Aseela shiru sukayi suna kallanta da mamaki Aseela ce ta ce, " Mommy meyasa kike yin kuka bayan idan nida Aseem muna kuka faɗa kike mana? " ajiyar zuciya ta sauke jikinta na rawa ta fara goge hawayenta ta ce, " Kaina ne yake ciwo kinji babu abinda ya faru " Kamar mai nazari Aseela ta kalli  mahaifiyarta ta ce, " Amma Daddy ba shi yake kaiki asibiti ba kuma yace kar mu tafi kika janyo mu muka taho " ɗan tsuke fuska Hajiya Kaleesat tayi ta ce, " Aseela ba na hanaki surutu ba kina san na yanke bakinki ko?" shiru tayi daga haka bata ƙara magana ba.

     Hajiya Khaleesat tunani ta shiga yi na abinda zata sanarwa dasu Hajiya Yaya idan ta shiga gidan, ta jima a haka amma ta kasa samarwa da kanta mafita, horn ta fara yi a hankali ba'a ɗauki lolaci baTukur ya buɗe mata ƙofar, kai tsaye parking space ta wuce tana ajiye motarta suka fito ita da su Aseem da jakar kayansu, Tukur ne ya karasa da ya ɗauki jakar kayan ya wuce musu da ita falon Hajiya Yaya, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka take takawa fuskarta babu walwala abinka da farar mace fuskar tayi jawur  saboda kukan da tasha, lokaciin ada ta shiga falon Hajiya Yaya a zaune ta sameta tana cin abinci, tunda Hajiya  Yaya ta ga Hajiya Khaleesat take binta da kallo, guri  ta samu ta gaida mahaifiyarta sannan ta ja baki tayi shiru, Hajiya Yaya kallan tsaf tayi mata ta ce, " Khaleesat lafiya me yake faruwa na ganki da jaka? "
     Hajiya Khaleesat kamar jira take ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, Hajiya Yaya shiru tayi  tana kallanta sai da ta barta tayi mai isarta sannan ta ce, " Lalla lamarin babba ne yau sama da shekara Ashirin da aurenki baki taɓa zuwarmun da wannan  yanayin ba ki sanar dani me yake faruwa " Hajiya Khaleesat goge hawayen  idonta tayi ta rasa abinda zata sanarwa da mahaifiyarta, dabara ce ta faɗo mata tayi maza ta ce, " Hajiya Yaya wai Daddyn Aseela aure zaiyi " Kallan tsaf Hajiya Yaya tayi mata tana nazartarta  sannan ta ce, " Khaleesat ni ba yarinya ba karki manta nina haifeki dan haka babu wata dabara da zakiyi mun, tunda baki kai haka ba mijinki ya taɓa aure ko alokacin babu wani abu da kika nuna na sakarci sai yanzu da girma yazo yaranku suka fara girma, akwai dai wata a ƙasa amma ba wannan dalilin bane ya dawo dake " suna cikin haka Mahaifinta ya shigo cikin ɗakin ya riski hirarsu, sai da ya zauna suka gaisa da Khaleesat yanayinta ya ƙarewa kallo ya tabbatar masa da akwai matsala, cikin halin dattako ya ce, " Khaleesat lafiya na ganki a daren nan? " Hajiya Yaya najin haka tayi karaf ta ce, " A faɗarta  wai mijinta ne zaiyi aure " murmushi yayi ya ce, " Saboda zaiyi aure zaki taho gida Khaleesat ko shi yace ki taho? " girgiza musu kai tayi ta ce, " A'a ni na taho "

     Ajiyar  zuciya ya sauke yace, " Idan wani abun ne ki sanar da muu sai mu shawo kan matsalar saboda dake da Kabiru duk ɗaya ne agurunmu " girgiza kai tayi tana hawaye ta ce, " Ba komai Abba " har cikin zuciyarsa yanajin kukanta dakewa yayi ya ce, " To idan kin tabbata babu komai ki tashi ki koma gidan mijinki " ɗagowa tayi ta bishi da idanu har zuwa lokacin hawaye ne ke bin fuskarta, jiki  ba ƙwari ta yinƙura ta riƙe hanun su Aseem ta juya tana share waye, Hajiya Yaya ce ta ce, " Alhaji barinta zakayi ta tafi? " murmushi yayi ya ce, " Idan ban barta ta tafi ba kina nufin barinta zanyi tunda dalilin da gayamun ba wani gamsashen bayani bane " shiru Hajiya Yaya shiru tayi bata ƙara magana ba, har sun kusa zuwa ƙofa Aseela ta juyo ta ce, " Abba kuma wallahi sai Daddy yace Mommy tayi haƙuri karta tafi amma ta janyo mu muka taho, kuma kullin Daddy sai ya bamu chocolate "

      Hajiya Khaleesat cikin takaici ta kalli Aseela zata doke Abba yace, " Kyaleta karki daketa, Aseelan Abba kyale Mommynki yanzu zaku koma gurin Daddynku " Gyaɗa masa kai tayi sannan suka wuce suka tafi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 03, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now