27&28

388 29 4
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    27&28

            Da mamaki ƙarara afuskar Alhaji Kabeer ya kalli matashin saurayin yana faɗin, " Kai Khalifa lafiya me yake faruwa ne? bangane ni na kashe Mahaifinku ba?? " kafin Kaleefa yayi magana ɗaya daga cikin police ɗin ya ce, " Alh bamu da time ɗin amsa tambayoyin ka yanxu amma idan muka je office zaka samu damar amsa su yanda ya kamata " yana rufe baki yaran sa suka fara ƙoƙarin kamo hannunsa da sauri ya fisge cikin ɓacin rai yana faɗin, " Dakata ku dakata idan wata magana kuke san yi da ni basai kun biyo mun ta wannan sigar ba, badai office bane muje " Hajiya Kaleesat dake zaune jin maganganun da tayi sama-sama yasa ta fitowa, ganin abinda ke faruwa ne ya bata mamaki a matuƙa aruɗe ta fara tambayar Alhaji halin da ake ciki, bayani yayi mata sannan yayi wa Driver gidan sa magana tare da wasu police biyu suka shiga, motar police ɗin ce agaba sai ta Alhaji Kabeer sai kuma ɗayar motar tasu, jiki a sanyaye Hajiya Khaleesat ta shiga cikin gida maganganun Alhaji na mata yawo azuci, wani tunani tayi da sauri ta ɗauki wayarta ta kira Hajiya Uwani, kira biyu tayi mata ba'a ɗauka ba sai ana uku sannan aka ɗauka, tun kafin Hajiya Kaleesat tayi magana Hajiya Uwani ta fara balbaleta da ruwan masifa, " kiran me kike mun mai zaki ce mun Kaleesat dama Amintaka na juyewa ta zama ƙiyayya? Wallahi ko amafarki akace mun Alhaji Kabeer zai iya kashe Daddyn Khaleefa zan ƙaryata saboda irin shaƙuwarsu da Amintarsu, to wallahi-wallahi kinji na rantse idan kuɗi da ƙarfin iko na magani jinin Maigida na bazai tafi a banza ba, idan yana taƙama da kuɗi da faɗa aji muma muna dashi babu abinda zai numa mana, ni Uwani bazan bar jinin Uban ƴaƴana ya salwanta abanza ba " tana gama faɗar haka ko jiran abinda Hjy Kaleesat zata faɗa batayi ba ta katse wayarta hawayen rashin mijinta na gangarowa daga idanunta, jikin Hajiya Kaleesat har wani irin tsuma yake saboda tsananin tashin hankali musamman da ta tabbatar da maganar daga bakin Uwar gida agurin Alhaji Abdurrahman, wasu irin siraran hawaye baƙin ciki masu zafi ne ke gangarowa daga idanunta, kaiwa da komowa ta shiga yi daga farkon falonta zuwa ƙarshensa afili take furta, " kai anya kuwa Daddyn Aseela zai iya kashe aboki kuma amininsa, anya babu sharrin abokan gaba kuwa?? To idan ma haka ne wane abu ya haɗa su da har zai hafar da kisa atsakaninsu?? yaushe ma muka dawo ƙasar kuma mai yasa da ya shigo ɗazu banga alamun damuwa a tattare da shi ba??? anya wannan lamarin babu lauje acikin naɗi kuwa?? " ita kaɗai take ta surutan ta kamar zautacciya, tana cikin wannan halin Hajara ta kirata awaya, hannnunta har rawa yake tasa hannun ta ɗauka murya asanyaye, " Salamu alaikum " daga cen ɓangaren aka bata amsa da, " Mummyn Aseela dan Allah mai yake faruwa ne wai abinda na gani yanxu a News da gaske wai Yaya ya kashe Alhaji Abdurrahman??? dan Allah meye gaskiya lamarin wallahi na shiga ruɗani da tashin hankali " sai ayanzu Hajiya Kaleesat ta samu damar yin kuka saboda da zuciyarta suya da raɗaɗi take mata, jin irin gursheƙen kukan da Hajiya Kaleesat ta ke yi yasa jikin Hajara yayi sanyi, itama hawaye ne ke zuba daga idanunta ta kuma jefo wa Hajiya Kaleesat tamabaya, " dama sunyi wata hatsaniya ne, ba shekaran jiya waccen kuka dawo daga India ba " goge hawayen ta tayi sannan ta ce, " wallahi Hajara ni kaina bansan me haɗa su ba, nifa ina ganin kamar da sharri acikin awannan al'amarin amma taya Daddyn Aseela zai kashe Aboki kuma amini agurinsa da kowa yasan yanda alaƙarsu ta ke, Hajara ke kina ganin hakan zai faru wallahi ba shi bane Allah sharri suke masa " Hajiya Kaleesat ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya, Jikin Hajara kuma sanyi yayi cikin kuka ta fara furta, " Innalillahi........ " saboda yanda ta ke ji katse wayar tayi itama Hajiya Kaleesat ajiye ta ta wayar tayi tana dafe kanta tana wani irin matsanancin kuka, Aseela dake gefen kujera a kwance sai ɗan wasannin ta ta ke tana ciccilla-ciccilla ƙafafu, wata wayar ce ta kuma shigo mata tana dubawa taga number ɗan uwanta ne Alhaji Abubakar, ɗagawa tayi amma saboda yanda kuka yaci ƙarfinta kasa magana tayi, daga cen ɓangaren Alhaji Abubakar najin haka jikinsa ya kuma sanyi dama kiran da yayi mata dan ya tabbatar da abinda ya gani a labarai ne, cikin tashin hankali ya cewa ƴar uwar tasa, " Bari nazo gidan ganin nan zuwa yanxu" ko kashe wayar baiyi ba sai ta kashe, Lokaci-lokaci ta ke furta kalmar, " Innalillahiwa'inna'ilahirraji'un " gaba ɗaya gidan tsit yayi kamar waɗanda akayiwa mutuwa, jikin ma'aikatan gidan da ƴan aikin gidan gaba ɗaya yayi sanyi kowa ji yake ba daɗi a zuciyarsa, musamman da Alhaji yake mutum ne da bashi da mugunta ko kaɗan ga wanda yake ƙarƙashin sa, baya nuna ƙyama ko cin zarafi ga kowa har su Inna Furaira, shiyasa suke jin daɗin aiki agidan saboda sunyi dace da iyayen gida.

        Kai tsaye cen Bompai aka wuce da Alhaji Kabeer ɓangaren kula manyan lafuka da ya harda da Fashi da makami, Masu garkuwa da mutane, Masu Fyaɗe da masu laifuffukan kisan kai, kafin su ƙarasa tuni wasu daga cikin abokansu da ƴan uwan mammacin sun hallarci Headquater, musamman da case ɗin ya zama na manyan mutane ne lokaci ɗaya garin Kano da sauran garuruwa da ke cikin Kasar Nigeria har ma da  maƙwabtanta suka ɗauka, haka nan kafofin yaɗa labarai da gidajen talabijin zance ya karaɗe ko'ina, uwa uba Kafofin sada zumunta irinsu Facebook, Whatsapp, Twitter, Instagram da dai sauransu, harabar gurin cike ta ke da ƴan jaridu na sassan ɓangararo daban-daban, Alhaji Kabeer abun ba ƙaramin girgiza shi yayi ba musamman yanda yaga ƴan jarida na dafifi wajen ganin sun naɗi sautin muryarsa, da sauri suka wuce ciki danma ma'aikata sunyi ƙoƙari matuƙa wajen dakatar da ƴan jaridu da basu samu damar wucewa ba.

        Alhaji Kabeer na zaune wani Police ya ƙaraso gurinsa ya zauna akan wata kujera suna fuskantar juna, kallan Alhaji Kabeer yayi ya ce, " Alhaji munasan ka gaya mana gaskiyar abinda ka sani bamasan ka wahalar damu kaima ka wahalar da kanka, idan ka bamu haɗin kai Case ɗin nan zai xo mana da sauƙi tsakanin mu da kai,  amma idan ka wahalar damu kaima zaka wahalar da kanka " jinjina kai Alhaji Kabeer yayi shi har lokacin abin mamaki yake bashi ace yanda yake da abokinsa kuma Amininsa ace wai ya kashe shi, katse shirun police ɗin yayi da, " ka gaya mana dalilin da ya sa ka kashe Abokinka kuma Amininka Alhaji Abdurrahaman, ko kana da wata hujja akan kisan?? mece ce hujjarka? Wani abu ya haɗaku ne kafin ka kashe shi?? Idan ya faru mai yasa bakayi report ba har ka ɗauki doka a hannunka " Alhaji Kabeer jin tambayoyin yayi kamar saukar aradu saboda baisan ma mai zaice musu ba, shi fa har zuwa lokacin gani yake kamar duk faɗa suke yi Alhaji Abdurrahman na raye, jin shirun yayi yawa yasa Police ɗin ya buga masa tsawa yana faɗin, " Muna tambayarka kayi shiru karka ɓata mana lokaci " da idanu Alhaji Kabeer yabi Police ɗin yana masa kallon mamaki har baisan lokacin da ya ce, " yau ni Ƙaramin ma'aikaci ke bugawa tsaya a gabana?? " Murmushi Police ɗin yayi ya ce, " kana mamaki ko? ay tunda ana zarginka da kisan kai kisan ma na mutum Kamar Alhaji Abdurrahman zaka ga abinda yafi haka ma, naga ka harzuƙa ko nima zaka kashe ni ne kaga sai ka tabbatar da hujja batare da wahalar bincike ba " dafe kansa Alhaji Kabeer yayi ransa na masa suya duk inda ɓacin rai ya kai ya kaishi, shiru yayi bai tankawa Police ɗin ba yana firzar da iska mai huci, Kwankwasa Table ɗin da dake gabansu Police ɗin yayi ya ce, " Har yanxu baka bamu amsar tambayarmu ba ko sai mun turaka wancen sashen sun tamabaye ka ne " ya ƙarasa faɗa yana nunawa Alhaji Kabeer wani ɗan ɗaki dake kallon gurin da suke, Idanun Alhaji Kabeer sum kaɗa jawur saboda ɓacin rai cikin ƙunan rai ya ce, " Ni ban kashe shi ba hasalima ni ban gasgata maganar ku ba taya zan kashe abokina kuma Aminina da hannuna?? " murmushi Police ɗin yayi sannan ya zura kansa ƙasan table ɗin yasa wani farin ƙyalle  ya ɗauko wata zabgegiyar wuƙa irin ta maharba da jini ajikinta, daga jikin hannunta anyi waɗansu irin gwamammnun rubutu, agefen farko na  wuƙar kuma zanen fuskar ƙwarangwal ne garesu guda uku ☠️☠️☠️ a ɗayan ɓangaren kuma anrubuta, " FARTAF KINBAS GUR " ( RUHIN FANSA NE ) Kallan Alhaji Kabeer yayi ya ce, " kana nufin baka san wannan wuƙar ba?? " Alhaji Kabeer na kallan wuƙar yaga wata irin walƙiya sannan daga gurun fuskar ƙwarangwal din yaga wasu fuskoki sun bayyana sai dai hasken walƙiyar shi ya hana shi gane ainihin fuskar mutanen, da sauri yasa hannu ya kare fuskar sa saboda hasken jinsa yake har tsakiyar kansa, wannan karan murmushin rainin hankali  Police ɗin yayi musamman yanda yaga Alhaji ya tsorata da ganin wuƙar, mai da wuƙar yayi yana cigaba da murmushi yace, " wato kana nufin tsoron wuƙar ma kake ji ko?? Kana tunanin zaka iya raina mana hankali ne ka kashe shi da hannunka sannan kazo kana mana basaja, kai Emmenual zo ku wuce dashi ku tambaye shi "  yana rufe baki wasu police biyu dake bakin ƙofa suka shigo suka wuce da shi, cen cikin wani Cell suka kaishi babu kowa aciki kasancewar nan aka ware ake  ajiye masu laifi masu kuɗi ko mulki ko wasu madafun iko, ɗakin baƙiƙƙirin yake ba haske sosai suna turashi ciki suka fito, tsaye Alhaji Kabeer yayi abun duniya na damunsa, daga cen bayansa alamun tafiya ya ji yana waigawa yayi arba da Muneera tana tafe tana goge hawaye, a tsorace ya ja baya jikinsa ya hau karkarwa, cikin wani irin sautin muryarta mai amo mara daɗin saurare ta ce, " Har gobe ina cikin bakin ciki bazan daina baƙin ciki da zubda ba har sai RUHIN FANSA ya cika burinsa " tana ƙarasa faɗa tabi ta jikin kofar Cell ɗin ta wuce.

     *TURƘASHI*🤭

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now