37&38

320 29 9
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    37&38

    _SHIMA BAN TACE SHI BA_

           Ranar da Amarya ta tare Alhaji Kabeer ƙin shiga ɗakin yayi gani yake kamar ya ci fuskar Kaleesat ne dan yana gudun abunda zai sosa mata zuciya musamman da yasan halinta yanda take da tsananin kishinsa, Washegari ma sai da ta matsa masa da gaske sannan ya amince mata ita tayi masa rakiya har part ɗin kishiyarta mai suna Surayya, tunda suka nufi hanyar Part ɗin gabanta ke matsanancin faɗuwa wani irin abu mai ɗaci take ji ya tsaya mata aƙahon zuci, ahankali take ɗan sauke ajiyar zuciya tana fidda iska mai huci daga bakinta, Suna zuwa part ɗin abakin ƙofarta Alhaji Kabeer ya tsaya Kaleesat ce tayi ƙarfin halin ƙwanƙasa ƙofar, duk yanda take ƙoƙarin kaucewa dan karya fahimci halin da take ciki sarai ya ganota, cikin zuciyarsa shima ji yake ba daɗi gani yake kamar yayi mata wani babban laifi mai yawa, daga ciki suka ji anzare sakata ƙofar wani sihirtaccen ƙamshi ne ya doki hancinsu, atake gaban Kaleesat ya yanke ya faɗi amma sai ta basar ta ƙaƙalo murmushin dole ta ɗora akan bakinta tace, " Barka da dare Amaryar mu ga Angonki na kawo miki shi " Sanye take da ƙananan kaya riga da siket kanta da hula sai dai ta baya ta watso gashinta baya, ƙas ƙas ƙas ke tashi daga cikin bakinta tana taunar cingam, wani malalacin murmushi ta sauke sannan ta kalli Kaleesat tace, " Ay na ɗauka Angon sai ya gama African time zai ƙaraso, koda yaushe wataƙila Auntyna bata gama sallamar sa bane " Kaleesat murmushi tayi ta ce, " Habeebee nifa daga nan zan wuce, Amaryarmu ga Angonan amana asha amarci lafiya "

       Gaba ɗaya fuskar Alhaji Kabeer ba annuri sai cika yake yana batsewa, Surayya na jin haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta ce, " to mu kwana lafiya Aunty, My Dear mu wuce ciki ko " Khaleesat najin haka ta janye hannunta daga na Alhaji Kabeer ta wuce gaba zuciyarta na ƙuna, tana fita daga part ɗin Surayya ta wuce tana Part ɗin kai tsaye Bedroom ta shiga ta faɗa kan gadonta tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

       Sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta faɗa toilet taje ta watsa ruwa ta koma kan gado ta kwanta har zuwa lokacin zuciyarta zafi take mata, tana cikin wannan yanayin har bacci yayi awon gaba da ita.

        Washe gari tun duku-duku Alhaji Kabeer ya taho sashen Kaleeasat sai dai fir ta hana shi zama dan dole haka ya janye ƙafarsa ya koma ɓangaren Surayya.

         A daddafe Alhaji Kabeer ya kammala kwanakin sa agurin Surayya har kwana ya zagayo kan Kaleesat, a kallon da yayi mata iya kwana ukun da yayi a ɗakin Surayya harta ɗan faɗa daga fuskarta zuwa wuyanta, sai dai ga wanda bai ƙare mata kallo ba bazai taɓa fahimtar halin da take ciki, Suna zaune suna hira Hajara ce ta kira shi a waya bayan sun gaisa ya miƙawa Kaleesat itama suka gaisa, bayan sun gama gaisawa Kaleesat take mata ciwon bakin bata zo Auren Alhaji Kabeer da Surayya ba, ita ɗinma maida mata da martani tayi saboda ita ƴar amanar Kaleesat ce kowa yasan da haka, sun jima suna hira sannan sukayi sallama.

         *BAYAN WATA ƊAYA DA SATI BIYU*

         Surayya ce kwance babu lafiya banda Amai babu abinda take kwarawa ko ruwa ta sha sai ta dawo dashi, wannan ciwo da take yi sai ya ɗaga hankalin Alhaji Kabeer ba shiri ya kira Family Doctor ɗinsu yazo ya duba ta, tashin farko a gwaje-gwajen da yayi mata ya nuna Surayya na da ciki,  Alhaji Kabeer jin maganar yayi wani banbarakwai har cikin zuciyarsa bai Aminta da maganar likita ba, saboda ko kaɗan bai kawo ciki agurin Surayya ba shiyasa ma yaja bakinsa ya tsuke ba wanda ya gayawa har Kaleesat bai sanar da ita ba, Surayya banda fankama da hura hanci ba abinda takeyi sai kuma sabon iyayi da yauƙi ya tashi, tun daga wannan ranar sai ta tsiri shiga sashen Kaleesat da sunan taje suyi hira, kwananta uku da fara zuwa suna zaune suna hira kawai sai gani tayi Surayya ta tashi da gudu ta fita tana kakarin amai, Kaleesat sai da gabanta ya faɗi cikin zuciyarta take ayyana zargin ciki agun Surayya musamman da ta lura da yanda Surayya ta ɗashe ta yi wani haske, alokacin bata dawo Part ɗin Kaleesat ba sai ita ta bita taje tana mata sannu da jiki, lokacin tana kwance akan doguwar Kujera Alhaji Kabeer ne ya shigi ya samesu ahaka, cikin yatsina ta ce, " jiki da sauƙi kinsan irin wannan larurar sai ranar da aka rabu jiki yake daɗi, yauwa Dear ka tahomun ta Mangwaro da Agwalumar da nace maka? " Daskarewa Alhaji Kabeer yayi saboda tsananin kunyar da ta kama shi, ganin haka yasa Kaleesat tace, " To sannu Amaryar mu Allah ya raba lafiya ni bari naje na ɗan kwanta na huta dan bacci nake ji " Surayya ɗago da kanta tayi ta watsawa bayan Kaleesat harara cikin zuciyarta tana jin haushinta, Hajiya Kaleesat ta gefen Alhaji Kabeer ta wuce uffan bata ce masa ba cikin zuciyarta take ayyana ashe akwai lokacin da zai ɓoye mata wani abu nashi, Shekararsu kusan goma sha huɗu da aure bata taɓa ko da ɓatan wata amma matarsa ta samu ciki shi ne ya ɓoye mata irin wannan abun farin cikin da aka daɗe ana nema, Shafa nata cikin tayi afili ta furta, " Allah nasan kana sane dani Allah ka bamu haihuwa mai albarka kamar yanda kake bawa sauran mata " hawaye ne ya gangaro mata afuska ta goge sannan ta haye kan doguwar kujerarta ta kwanta.

       Alhaji Kabeer na shiga faɗa rufe Surayya dashi gani yake kamar wannan cin fuska ne tayiwa Kaleesat, aykuwa kamar jira itama take ta fara zazzaga masa ruwan rashin mutumci, baibi ta kanta ba yasa kai ya wuce abinsa, tana ganin wucewarsa ta dafe ciki tana kuruwa da ihun cikinta na ciwo, abinka da farin shiga cikin tashin hankali ya kira likita cikin gaggawa yace yana buƙatar ganinsa, tun fitar Kaleesat yaso yabi bayanta domin yaje ya wanke kansa, saboda lurar da yayi ranta kamar aɗan ɓace yake ita kuwa Surayya tunda ta lura da haka take ƙara langwaɓewa san ranta.

         *BAYAN WATA BIYU*

         Tafiya ce ta kama Alhaji Kabeer zuwa Kano yaje tattaunawa ga Gwamnan Kano, bayan ya gabatar da abinda ya kaishe gidan Abokinsa Alhaji Yakubu ya leƙa saboda Alhaji Yakubu ya azuzuta masa akan dole sai yaje gidansa sun gaisa, katafaren falon gidan suka shiga alokacin dattijuwar na zaune tana jan carbi, da sallama suka shiga cikin falon fuskarta ɗauke da fara'a ta kalleshi tana faɗin, " Barka da zuwa Yau mutanen Adamawa ne agidan namu? " cikin girmamawa Alhaji Kabeer yaje ya tsugunna gabanta ya ce, " Barka da Hutawa INNA LARAI da fatan mun same ku lafiya? " Carbin hannunta ta ajiye agefe sannan tace, " lafiya kalau Alhaji ya ka baro ƴaƴan nawa, ina Ƴata Khaleesat? " cikin girmamawa yace, " Wallahi duk suna lafiya sunce agaishe ku " gaisawa suka gama yi Inna Larai na mitar Alhaji Yakubu bai sanar da ita zuwansa ba da ta yi masa tuwon Shinkafa miyar zogale kamar yanda tasan yana so, Falon Alhaji Yakubu suka wuce suka shiga hirarsu ta abokai.

    *ƊUNBIN COMMENTS ƊINKU YA FARANTA MUN ZUCIYA IYA WUYA ANA TARE.*

TOFA MUN FARA SHIGOWA DUNIYAR SU INNA LARAI😂🤣

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEOnde as histórias ganham vida. Descobre agora