87&88

339 23 2
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*
   

                    87&88

          Alhaji Kabir ya jima a tsaye yana nazarin ta yanda zai fara aiwatar da aikin da ya kawo shi, a gefe ɗaya tsoro yake karya taɓa ɗaya daga cikinsu asirinsa ya tonu, kallansu yake ɗaya bayan ɗaya da mamaki saboda yanda ya gansu kamar waɗanda aka saukarwa da wata masifa ta bacci, wata mata ya hango ita da Ɗanta a jingine jikin bango ga kwanon abinci a gabanta da alama abinci suke ci ita da Ɗanta bacci yayi gaba da su.

      Takawa yayi zai zagaya ta baranda yaci karo da MUNIRA, Munira ƴar Alhaji Abdurrahman ce. Budurwa ce batafi shekara goma sha Shida zuwa sha bakwai ba, juye-juye yakeyi yana shirin janyeta har ya samu ya janyeta ta lungun Baranda ya kaita. cikin sauri ya aiwatar da abinda Boka ya umarceshi sannan ya buɗe bakinta ya zuba mata garin maganin da Boka ya ce shi ne wanda za'a saka abakin bayan ya kusanceta.
  
      Yana zuba mata garin maganin jikinta hau karkarwa haɗe da ɗaukan wani irin zafi, da sauri ya matsa daga gurin yana kallan abinda Munira take yi, bayan wani lokaci ta tsagaita da abinda jikinta yakeyi, hannu yasa a hankali ya janyota ya ƙara mayar da ita gurin da take kwance.

       Dube-dube ya farayi domin yaga yarinyar da tayi dai-dai da wacce boka yace a turawa garin magani ta gabanta, cen gefe ya hango wata ƙaramar yarinya wacce batafi shekara Uku zuwa huɗu tana kwance kusa da mahaifiyarta, ƙarasawa gurin yayi yana tafiya a hankali har ya ɗauko yarinyar mahaifiyarta ta motsa da sauri ya ajiyeta a tunaninsa farkawa zatayi, amma sai gani yayi ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci, a hankali ya ɗauki yarinyar ya zagaya gurin da yayi amfani da Munira ya kwantar da ita, runtse idanunsa yayi yanajin tausayin yarinyar gani yake kamar bazai iya ba, cen daga sama sai ji yayi amfara magana, " Kayi ka aiwatar da abinda ya kawoka idan ba haka ba lokaci ya ƙure maka kai zamu fansa a madadinsu "

      Garin maganin ya damƙo da hannunsa sannan ya tura acen ƙasa yarinyar, kamar yanda Jikin Munira yayi da farko haka itama ya dinga karkarwa daga baya kuma ya daina, yana ƙoƙarin mayarwa da yarinya wadonta daga cen jikin katanga ya hango wani ƙaramin Maciji yana tahowa da sauri yaja gefe, ga mamakinsa sai gani yayi macijin ya shiga ta ƙasan yarinyar, tsoro ne ya kamashi jikinsa ya hau karkarwa magana ya ƙaraji anyi masa.

       " Kai ɗauke ta ka mayar da ita inda ka ɗaukota kayi sauri ka fice daga gidan, kuma idan ka fita karka sake ka waiwayo bayanka, shikenan ka gama aikinka sauran namu ne kayi nasara a rayuwa dama kuma kaiɗin mai nasara ne, ka tafi kanka tsaye babu abinda macijin nan zaiyi maka " ana gama masa magana yaji wani ƙwarin gwiwa ya ƙara zuwar masa, ɗaukan yarinyar yayi har zuwa lokacin jikinta rawa yake yaje ya mayar da ita inda ya ɗauko ta.

       Yana mayar da ita ya juya fice daga gidan ya shiga motarsa ya koma gida, lokacin da ya koma da kansa ya ƙara buɗe ƙofa ya shiga da mota securities ɗinsa basusan ma ya shigo ba, yana parking motarsa ya fito ya wuce cikin gida kai tsaye bedroom ɗinsu ya nufa, yanda ya fita ya barta haka ya dawo ya samu Kaleesat tana bacci.

    Gefen gado ya zauna ya rafka tagumi wani irin yanayi yake ji a jikinsa sam ji yayi bai kyauta ba, tunanin rayuwa ya shiga  yi ruɗaninta take yaji nadama tazo cikin zuciyarsa, hawaye  ne ke zubo masa ta ko'ina daga idanunsa ya jima a haka sannan ya tashi ya koma kan gado ya kwanta a haka bacci yayi awon gaba da shi.

      Bayan Kiran sallar asuba kamar waɗanda aka farko dasu haka suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya, suna mamakin irin baccin da sukayi, wannan matar me yarinya ce sukaji ta rushe da kuka tana ɗora hannu aka, da sauri duk akayi kanta.

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now