11&12

435 57 5
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/L7dj60ptcAV3Oe1X6hAyBT

   
                    11&12

            Alh Kabeer na ganin haka ya juya cikin zafin nama kai tsaye office ɗin Dr Musa ya wuce, banka ƙofar yaji anyi da ƙarfin gaske azabure Dr ya tashi saboda ba ƙaramin tsorata yayi ba, Alh Kabeer na zuwa ya fara masa magana, " Dr yarinyata tana cikin wani yanayi tana buƙatar agajin gaggawa fito kaga halin da ta ke ciki " ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Dr Musa, ganin yanayin da Alh Kabeer ya shiga ya tabbatar masa da akwai damuwa, da hanzari ya yi bakin kofa cikin sauri ɗakin da suke ciki ya shiga, Hjy Kaleesat ya gani riƙe da jaririya tana hawaye, yana kai idanunsa kan babyn yaci karo da hawayen jini na gangarowa a idanunta, tsoro ne ya fara shigar sa gabansa ya hau bugawa, kamar ance ya kalli kwayar idanunta sai gani yayi idon nata ya juye fari tas kwayar idon sai juyawa ta ke kamar ana juya ƙwallo, ƙuuuuuuuuuuu cikin Dr ya karta ja da baya ya farayi cikin tsoron abinda idanunsa suka gano masa.

     Ganin haka yasa Alh Kabeer ya buga masa wata uwar razananniyar tsawa, ba Dr ba hatta su Hjy Kaleesat sai da suka tsorata, kallansa yayi ahassale ya far magana cikin kausashshiyar murya, " Wannan wane irin shirmen banza ne kana ganin yarinya tana wannan halin ka ƙi kayi wani abu wallahi idan wani abu ya faru da ita sai ka gane baka da wayo, ka zo ka bata kulawar da ya da ce da ita " tsoro ne ya kuma ɗarsuwa azuciyar Dr Musa suna kuma haɗa ido da Babyn yaga da ƙwalalo masa idanu kamar ƙwayar idon zata faɗo harta na wani ta le ba ki, wannan shi ne gaba kura baya siyaƙi ilahirin jikin Dr banda rawa ba abinda yake yi kamar mai rawar ɗa ri haka ya dinga yi, saboda tabbas yasan muddin wani abu ya samu babyn nan kashin sa ya bushe ba shi kaɗai ba harda iyalansa da waɗanɗa suke ƙarƙashin sa, tunda kowa yasan matsayin Alh Kabeer da faɗa ajin da yake da shi, takowa yake ahankali cikin rawar murya ya ce, " Ur Ex ka dubi ƙwayar idanunta da kyau ko wani Malamin zaka yiwa waya yaxo ne??? " Alh Kabeer ji yayi kamar Dr ya watsa masa ruwan zafi, aykuwa azafafe ya fara masa magana, " U r very stupid, are u Mad muna asibitin zaka ce na kira wani Malam, look wallahi-wallahi duk abinda ya samu gudan jini na ku kuka da kanku, wallahi ba kai kaɗai ba har ahalinka sai sunyi dana sanin abinda ka aikata " ganin Alh Kabeer ba da wasa yake ba yasa Dr ya ƙarasa yayi shahada ya karɓi babyn  hannuwan sa sai karkarwa suke, tafe yake agaba Alh kabeer na biye da shi abaya har zuwa ɗakin da aka tanadar da shi na jarirai ne domin duba lafiyarsu, da farko Nurses ya ce zai sai su goge mata jinin idanunta su gyara amma Alh ya ce sam bai yarda ba, Dr da kansa ya gyara mata fuska kafin su gama tuni tayi bacci sai sauke ajiyar zuciya take a hankali, haka nan kayan aikin da ya goge jini dasu yana gamawa yaga jinin jiki ya koma wani irin baƙiƙƙirin da shi.

          wasu allurai Dr ya ƙara yi mata sannan ya je ya kwantar da ita akan gadon jariran da aka tanadar domin su, ajiyar zuciya Alh Kabeer ya sauke sai ayanxu hanakalinsa ya kwanta, ya jima atsaye akanta yana ƙare mata kallo wata irin soyayyarta ce ta ke ƙara ratsa cikin jikinsa, sun kuyawa yayi ya kai bakinsa dai-dai goshinta ya manna mata kiss, acikin zuciyarsa yana ayyana, " wai yau ni ne na ga abinda Kaleesat ta haifa wai ni ne yau naga ƙwai na ƴata ta ciki na" ɗaga hannunsa sama yayi yana godewa ubangiji bisa ni'imtashi da yayi da wannan babbar kyauta, kallanta ya ƙarayi baccinta ta ke hankali kwance, daga goshinta dai-dai inda ya sumbace ta gani yayi gurin yayi ƴar taruwar jini sannu ahankali gurin yake ƙara rinewa shatin bakinsa na ƙara fito, mamaki ne ya kuma cika sa juyaww yayi da sauri ya koma ya kira Dr Musa, Dr na gama jin bayaninsa cikin zuciyarsa gaba ɗaya yaji ba daɗi har ji yayi inama ankwana biyu da yin CS ɗin da tuni sallamar su zaiyi dan ya gaji da wannan bala'in, wannan karan harda Alh Abdurrahman suka shiga cikin ɗakin sai dai abun mamaki suna shiga babu komai akan goshinta, haka suka tarkato suka fito cikin zuciyar Alh Kabeer yana wasi-wasi, ahankali Hjy Kaleesat ta turo ƙofa ta leƙo saboda tunda aka fita da ƴarta taji zuciyarta bata cikin nutsuwa, karo suka ci da Alh Kabeer tare suka koma ciki ganin yanda ta ɗaga hankalinta yasa yayi mata bayanin halin da baby ke ciki cikin kwanciyar hankali.

           Fitowa yayi ya koma gurin Abokin sa bayan ya zauna ya yi masa kallan tsaf sannan ya ce, " Abokina muji da matsalar da ta fara fusakanto mu yanxu kana nufin Inna Larai kaima ka ganta da idanunka??? " jinjina kai Alh Abdurrahman yayi ya ce, " haba Abokina kasan bazan ma ƙarya ba, tunda muke na taɓa kawo maka irin wannan hirar ne??? " shiru Alh Kabeer yayi ahankali yana furta, " Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, lallai akwai matsala " tsaf ya kwashe shima abinda ya gani da musababbun ciwon Hjy Kareema ya gaya masa, jikin Alh Abdurrahman sanyi yayi cikin sigar jimami ya ce, " ni ina ganin kodai masu kama da su muke gani?? amma mutanen da suka mutu tun shekarun baya ya za'ay su dawo? na tabbata wanda ya mutu ya mutu kenan har abada " Kan Alh Kabeer ya gama kullewa kallan abokin nasa yayi ya ce, " haba wane irin kama abinda har ji nai ana kiran sunanta ka ce mun kamanni gaskiya akwai wani ɓoyayyen al'amari " Alh Abdurrahman ya ce, " to Allah ya tsaremu da mugum ji da mugun gani " gaba ɗaya suka amsa da Ameen, sun  jima suna tattaunawa atsakaninsu daga ƙarshe Alh Abdurrahman yayi masa sallama ya wuce.

         Kwanan su huɗu a hospital ɗin aka sallame su suka koma gida saboda gurin Cs ɗinta yayi kyau yanda ake buƙata, tun daga wannan lokaci Babyn su bata kuma nuna wani abu na al'ajabi ba, ƴan uwa kuwa ta ko'ina sai zarya suke agidan Ex Kabeer, Ranar suna na zagayowa aka raɗawa yarinya sunan ASEELA saboda tun Hjy Kaleesat na da ƙaramin cikin taci burin sawa abinda zata haifa, idan Namiji ne asa masa sunan ANSAR idan kuma mace ce ASEELA, basuyi taron suna aranar ba sun ɗaga sai sati mai zuwa wato sati biyu da haihuwa saboda jikinta ya ƙara yin ƙwari kafin lokacin.

       A ranar da akayi suna cikin dare kimanin ƙarfe biyu da rabi na dare 2:30 am, suna cikin bacci sama-sama Hjy Kaleesat ta fara jiyo kukan jariri, da sauri ta yunƙura ta tashi gadon Aseela dake gefensu ta duba sai gani tayi wayam, wani irin hautsinawa cikinta yayi da sauri ta shiga tashin Alh Kabeer tana sanar dashi, kuma har zuwa lokacin basu daina jin kukan da ke tashi na jariri ba, atare suka fara dube-dube amma ba ita ba dalilinta, daga hanyar waje suka cigaba dajin kukanta buɗe ƙofa sukayi suka fice, daga cen wajen Falo suka ji kukan nata yafi tsananta, har rige-rigen sakkowa suke daga step ɗin bene dan zuwa gurinta, kafin su ƙarasa falon suka ji shiru da azama suka ƙarasa suna fita falon suka hangota daga cen wajen ƙofar da zata sada ka da baranda kwance cikin towel ɗinta aƙasa, Alh Kabeer ne ya riga ƙarasawa yana zuwa sai ganin giftawar wani dogon mutum mai fararen kaya yayi  ta baya wani irin gashi gareshi hargitsatstse, jiki na rawa yasa hannu ya ɗauke Aseela sai dai ga mamakinsu bacci ma ta ke babu alamu damuwa atattare da ita, kallan juna sukayi kowa da mamaki azuciyarsa, daga wajen hanyar Step ɗin bene tafiya suka fara ji kamar ana hawa sama, wannan karan ba ƙaramin tsoro ne ya kama su ba, Alh Kabeer ne yayi ta maza ya wuce gaba Hjy Kaleesat na binsa abaya.

     *DA ALAMA LABARIN BAI MUKU DAƊI BA SABODA BANGA RUWAN COMMENTS BA SAI TSIRARU DAGA CIKINKU,INA JIN ZAN WARE MASU COMMENTS NA BUƊE MUSU GROUP INDINGA TURA MUSU, SABODA INNA CE NA DAKATA DA TYPING BANYIWA MASU COMMENTS ADALCI BA.*

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now