59&60

295 31 11
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    59&60

       _Lokacin da muka baro kogon dutsen Mai ifritu sai da mukayi tafiya mai nisan gaske sannan muka ƙaraso titi Alhaji Musa ne ya kira wani mutum a waya ya ce masa yana buƙatar gida kamar yanda ya saba karɓa duk lokacin da ya kawo ziyara cikin garin, daga nan inda muke zuwa gidan mutumin bamuyi wata tafiya mai nisan gaske ba muka ƙarasa cen gidan, gida ne madaidaici mai ɗauke da ɗakuna huɗu da kitchen da banɗaki, sana'ar mutumin kenan bawa manyan mutane haya idan sun zo garin basu da wani mahalli, gidan tsaf yake a gyare bashi da wata matsala, Alhaji Musa ne ya bada umarni aka kawo mana abinci da abinsha wanka mukayi saboda gajiya bamu wani jima ba kowa ya kwanta._

     _Washegari tunda farar safiya muka ɗauko hanyar dawowa gida, Lokacin da muka isa wani ɗan ƙauye abakin wata kasuwa mukayi parking muka shiga wani ƙaramin resturent muka ci abinci, bayan mun fito zamu muna bakin mota wasu Almajirai biyu wa da ƙani suka ƙaraso gurinmu suna bara, gaba ɗaya na manta da alewar gurina sai Alhaji Abdurrahman ne ya tunamun ba musu na ɗauko alewar na haɗa musu da ɗari biyar na basu, take suka zube suna mun godiya kamar waɗanda nayiwa kyautar hajji, motar mu muka shige muka kuma cigaba da tafiya har muka ƙaraso cikin garin kaduna intakaice muku dai acikin Kaduna na ƙarasa rabar da sauran alewar hannuna, lokacin da muka ɗauko hanyar Kano muna tsaka da tafiya Alhaji Musa yace mun, " Mutumina yanxu zaka gane Mai Ifritu ba ƙaramin hatsabibi bane Wallahi ina gaya maka mutumina daga yanxu zuwa kowanne lokaci kana iya jin kyakykyawan labari indai kuɗi ne ka riga da ka gama yinsu indai dukiya ce sai dai wani ya nema agurinka " Murmushi nayi na ce masa, " kana ganin aikin mutumin nan yana ci kuwa? " kallona yayi da mamaki ya ce, " Lallai Habibu har yanxu da sauranka " Alhaji Kabeer da ke zaune a kujerar baya ya ce, " nifa lamarin bokan nan sam hankalina bai kwanta dashi ba anya kana ganin lamarinsa babu shirka aciki? " tsuke fuska Alhaji Musa yayi ya ce, " Tun tashin farko dama fa ba dole nayiwa kowa acikinku ba kuma da muka je sai da ya zayyanowa kowa matsalarsa, ruwanku ku koma ya magance muku matsalarku ruwanku ne ku haƙura amma ni dai nasan waye Mai Ifritu da tsilge na tabbata Alhaji Habibu nan gaba zai baku labari " haka muka cigaba da tattaunawa har muka ƙaraso gida daga nan kowa ya kama gabansa yayi mahallinsa._

       _Kwana ɗaya da dawowarmu daga Jos na samu aikin wata kwangila daga hannun wani babban ɗan siyasa, bazan ja muku da nisa ba tun daga wannan ranar harkokin kasuwancina suka cigaba da bunƙasa, maroƙa da mabuƙata haka suka dinga dafifi a ƙofar gidana, kowa ya dubi rayuwata data yarana sai yayi sha'awarmu, tun daga wannan lokacin sai nake ziyartar Mai ifritu akai-akai har takai da mun ɗinke ni da shi._

           _A kwana a tashi muna cigaba da rayuwa harkokin samu na cigaba da buɗemun, wata rana na kaiwa Mai Ifritu ziyara ina shiga cikin kogon dutsen sa na ci karo da Hajiya Saratu tana durƙushe gaban Mai ifritu, lokacin da mukayi arba da juna gaba ɗaya mamaki ne ya kamamu, sai bayan da kowa ya gama kai buƙatunsa gun Mai ifritu bayan mun fito har nayi gaba Hajiya Saratu ta dakatar dani tana roƙona akan karna sanar da maigidanta na ganta agurin Mai Ifritu, cikin mamaki na kalleta nace, " Dama kin san nan gurin ne kuma ya akayi mai gidanki bai san da zuwanki ba? "_

        _Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, " Wannan wani sirrina ne amma dai ina neman wannan alfarmar agareka " cikin halin ko inkula na amince da buƙatarta dan gani nake babu ruwana tunda ba abinda ya shafe ni bane, daga wannan ranar sai ya zamana duk ranar da zanje kusan ko yaushe sai mun haɗu da ita acen, hakan ne yasa Mai Ifritu yake haɗawa aljanu guda aikinmu suke yi nida ita_

       _Lokacin da harkokina suka binƙasa jindaɗin duniya na same shi ta kowacce siga, sai Alhaji Musa ya kuma yimun hanyar wani gawurtaccen boka dake cen Garin Ekiti, wannan tafiyar da mukayi mu biyu kawai muka yi ta daga ni sai Alhaji Musa, lokacin da naje gurun wannan bokan sai da na raina kaina kasancewar ya shafe Mai ifritu hatsabibanci da izza saboda shi yayi rayuwarsa ne aƙarƙashin ikon manyan baƙaƙen aljanu, Bakin wani teku muka je muka tsaya nida shi zuwanmu ke da wuya Alhaji Musa ya kalleni ya ce, " ciki fa zamu faɗa " kallansa nayi cikin tsoro da fargaba nace masa bazan iya ba shammata ta yayi ya fisgi hannun yana faɗin, " GUDUBAR BIN GUNGAR " har sai da ya ambata sau uku, kawai sai ji nayi wata guguwa ta ɗauke mu ta sauke mu acikin wata babbar da'ira mai ɗauke da fasalin masarautar aljanu, muna ƙarasawa gurin muka hangi wani guri wuta naci daga cikin wannan wutar wani gabjejen baƙin mutumi ya bayyana, sunkuyawa mukayi har cen ƙasa cikin girmamawa muka gaida shi, muna ɗagowa mukaji anfara wasu irin surutai da sam bama fahimtarsu, inanan tsaye ina mamakin irin shu'umancin wannan bokan ganin wata ƙwarya  mukayi agabanmu tana tafarfasa da wani irin ruwa mai yauƙin, daga cen gurun ƙasurgumin bokan nan mukaji yace, " Ka ɗauki wannan ƙwaryar ka juye rabin ruwan cikinka a jikinka, da sauri nabi umarnin abinda aka cemun, tun kafin na sauke ƙwaryar na nemeta na rasa, da'irar gurun da muke ciki ne ta ɗauki wata iriyar girgiza kamar zata tsage sai zuwa wani lokaci mukaji ta tsagaita, wani kan ƙwarangwal na gani agabana anjiƙeshi da wani irin baƙin jini, daga cen gurin bokan mukaji ya fara magana, " Harka mutu talauci bazai raɓi gurun da kake ba ka ɗauki wannan ƙwarangwal ɗin kaje ka kaishi cikin rijiyar Mai ifritu sannan ka samu matar aure kayi mu'amala da ita, karku kuskura ku tsarkake jikinku har sai kun shiga cikin kogon dutsen sa, zansa Aljanu suyi muku rakiya domin gujewa hatsabibancinsa, dalilina nayin haka kuwa shine, domin inmallaki ruhinsa aƙarƙashin ikona sai ka kula sosai domin ninasan waye Mai Ifritu koni da ka ganni anan ina shakkarsa haka muradina bazai kammala ba harsai na mallaki ruhinsa, wannan kan ƙwarangwal ɗin da kake gani na kakan mai ifritu ne na goma labarin zuwanka naji nasa aka ɗauko mun shi a maɓoyar sirri, idan zakaje kogon dutsensa karkayi sallah ta wunin ranar idan har kayi haka babu abinda Mai Ifritu zai iyayi maka, idan kayi haka babu abinda zaka nema aduniya ka rasashi."_

_KUYI HƘR DA WANNAN SABODA RASHIN NEPA, INDO SARƘA FANS KU DAKA CE NI_🤭

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now