95&96

255 31 1
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*
   

                    95&96

       Cikin Alhaji Kabir ne ya kaɗa take gumi ya yanko masa shiru yayi bai tanka ba, Bello ne ya karɓe zance da, " Kai baka isa ka aikata abinda Allah bai hukunta ba dan haka rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah " Hajiya Khaleesat takawa ta farayi zata tafi Bello ya ce, " Hajiya inasan ki dakata zuwa wani lokaci kaɗan har mu samu mu raba ƴarki da wannan Azzalumin " Hajiya Khaleesat ba dan taso ba ta dawo ta zauna.

    Bello wayarsa ya ciro ya kira lambar wani Baffansa dake gaba da rugarsu, kiran farko ya ɗauka bayan sun gaisa cikin harshen fullanci Bello ya cigaba da cewa, " Baffa wani aiki ne ya taso mai matuƙar girman gaske inasan ka taho da ɗalibanka domin ku mu haɗu guri ɗaya, idan babu damuwa a yanzu nake san ku ƙaraso domin barin sa zuwa wani lokacin yana da matuƙar haɗari " daga cen ɓangaren Baffa yace, " Bello yanzu haka ban gida na fita da shanu amma yanzu haka na kusa ƙarasawa gida, zan kira su Ɗahiro su kintsa kafin na ƙarasa sun shirya sai mu taho " cikin jin daɗin kalaman Baffa, Bello ya amsa masa yana godiya sannan sukayi sallama.

       Bello na gama waya tashi yayi ya shiga ɗakin Goggo cen jikin bango wata jakar fatarsa ce a saƙale,ɗaukota yayi ya fito ya fara fito da kayan cikinta garin magunguna ne kala da waɗansu iri acikin kwalabe sai garinsu habbatussauda, ajiyesu yayi a gefe ya ɗauko wata ƙaramar ƙwarya ya fara tofi acikinta, ya jima yana tofin acikin ruwa sannan ajiyeshi a gefe yasa murfi ya rufe, suna nan zaune babu me cewa wani uffan kowa da abinda yake nazari a cikin zuciyarsa.
        Daga cen gefen gurin da Bello ya ajiye maganungunan nan wuta ce ta fara ta shi da sauri yayi ta maza ya ɗaukesu, wutarce ta cigaba da ci abinka da bukka take sauran kararen gurin suka kama,wutar ba ƙaramin tsoro ta basu ba da sauri suka fara ɗebo ruwa a tulu suna zubawa amma wani abun mamaki kamar fetir suke ƙara mata,Bello ne ya ɗauko wannan kwaryar da yayi tofi ya dinga bi yana watsawa wutar,cikin ikon Allah duk inda ya watsa sai dai kaga wuta ta mutu ƙurmus, kafin wani lokaci wutar gaba ɗaya ta mutu sai ɗan ƙauri-ƙauri da yake tashi, mutanen rugar duk sunyi carko-carko a ƙofar gidansu Bello kowa yana ganin ikon Allah, wasu kuma mamaki suke inda su Bello suka san waɗannan baƙin ƴan birnin masu ƙatuwar mota, ganin wutar ta mutu yasa Bello ya sallamesu ya ce musu su bawa baƙi guri zasu huta, badan sun so ba ɗaya bayan ɗaya haka suka fara tafiya kowa ya koma gidansa.

      Tafiyarsu babu jimawa su Baffa suka shigo wajensu Bello, zama sukayi bayan sun gaisa Bello yayiwa Baffa bayanin Gunguri da ikirarin da yake yi, Baffa jinjina kai yayi ya ce, " Tabbas babu abinda ya gagari Ubangiji da shi muka dogara kuma zai isar mana, kai Ɗahiro ina magungunan da turare? " Ɗahiro ciro wasu magunguna yayi Baffa da kansa ya taka gurin Aseela dake zaune a gefen Alhaji Kabir,yana sa hannu zai ɗaukota ta fara mutsu-mutsu da wani irin gurnani mara daɗin sauraro, take gashin kanta hautsine idanunta suka juye babu baƙi sai farin gabaɗaya, Baffa riƙe ta yayi da ƙarfinsa cikin zafin nama tayi wata irin girgiza kaɗan ya rage Baffa ya kai ƙasa, tashi tayi da gudun gaske ta faɗa kan cinyar Hajiya Khaleesat tasa hannuwanta biyu ta shaƙe mata wuya, juyowa tayi da wata irin murya mara daɗin sauraro ta ce, " Duk wanda ya kuakura ya kusanto inda nake takan wannan zan fara zartar da hukuncina " Hajiya Khaleesat banda kakari babu abinda takeyi idanuwanta gabaɗaya sun furfito harta fara fita daga hayyacinta, Bello ne ya ce, " Lallai ka cika matsoraci indai har sai ka laɓe a bayan mace sannan zaka aiwatar da mugun ƙudirinka " Baffa wani tunani yayi yasan tabbas suka yimasa fito na fito abu mai sauƙi ne ya nemi halaka ta, cikin dabara ya cewa Gunguru, " Munji abinda ka faɗa amma kai me kake so daga gurunmu " Gunguru ƙyaƙyacewa yayi da dariya sannan yace, " Sai ni Gunguru jikan Kunkuru,  Sai ni kabari kowa ya shigeka ya shiga kenan, Sai ni wuta mai tsananin azaba ko Ɗan goye na tsoronki, so nake gaba ɗaya kowa ya kama gabansa nikuma ku barni a inda na saba dan rabani da Aseela sai kun shirya "

     A hassale Bello ya ce, " Babu inda zamu tafi kuma dole ka bar jikin yarinya, yarinyar da bataji ba bata gani ba " Gunguru najin haka ransa ya ɓaci ya ce, " Haka kace " cikin kwarin gwiwa Bello yace, " Ƙwarai haka nace " Bello be rufe baki ba Gunguru ya kafa bakinsa a jikin ƙirjin Hajiya Khaleesat ya fara zuƙar jininta, take numfashinta ya fara sama ta fara fita hayyacinta nan take ta yanke jiki ta faɗi.

       Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin mutanen gurin yayi ba, Alhaji Kabir ihu ya fasa da sauri ya faɗa gurun Khaleesat dake kwance yana jijjigata cikin tashin hankali yana kiran sunanta.

    Baffa gani yayi idan sukayi sanya sai gunguru ya ƙarar dasu ɗaya bayan ɗaya, bismillah yayi ya fara karanto wasu ayoyi daga cikin ayoyin Alƙur'ani, kai tsaye ya tunkari Aseela da ƙyar ya ɓamɓareta daga jikin Hajiya Khaleesat, gurin da aka cire Aseela wato saitin kirjin Hajiya Khaleesat yayi jawur, da ƙafin gaske yake santa sai da yasa Ɗahiro ya barbaɗa wani garin magani da wani turare a ƙasa sannan ya zaunar da Aseela a dai-dai gurin,kamar haɗin baki gaba ɗaya sukayi bismillah suka fara karatun Alƙur'ani, a gefe ɗaya ga turaren magunguna nan yana ci acikin kasko.

INA MUKU FATAN ALHERI GABA ƊAYA🥰🥰🥰🥰🥰 WANNAN SHAFIN NA ƳAN AMEERA ADAM PALACE NE❤️❤️❤️ KUYI YANDA KUKE SO ALLAH YA BAR ƘAUNA🥰🥰🥰🥰🥰🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now