17&18

399 35 1
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    17&18

             Jikin Alhaji Kabeer har wani irin karkarwa yake saboda tsoro da tashin hankalin abinda ya ga Kausar na shirin aikatawa ga Aseela, da sauri ya sa hannu ya amshe ta zuciyarsa na wani irin lugude saboda ɓacin rai, Hajiya Kaleesat mutuwar zaune tayi saboda gaba ɗaya ta sadddaƙar Aseela ta tafi shikenan  shiyasa ma ta kasa katabuss ko motsi ta kasa yi, Alhaji Habeeb ne ya kalli abokinsa cikin rashin jindaɗin abinda ya faru ya ce, " Abokina kayi.......... " katse shi Alh Kabeer yayi yana ɗaga masa hannu sannan ya ce, " kar muyi haka da kai, sai kace bansan matsalar ciwon Kausar ba? Yanxu bari mu wuce Hospital adubata ina ganin hakan zai fi " jam Alhaji Habeebu yayi sannan ya ce, "  Ciwon Aseela sai ya ke mun yanayi da na Kausar akwai Dr Aryan dake zuwa duba ta har gida ko shi zan kira bamu da nisa dashi " ba haka Alh Kabeer ya so ba sai dai dan kar yaga baiyi maka kara bane ya sa ya amince, Inna Furaira dake gefe duk tayi wani fiƙi-fiƙi tsoro duk ya kamata musamman da ta ga yanda Kausar ke zaro idanu tana surutai sai abun yayi mata kamar yanayin Aljanu, ita kuwa aduniya ba abinda take tsoro sama da Aljanu da kuma mai Aljanun, cen ta takure da jikin kujera sai muzurai ta ke tana bin gefe da gefen ta da kallo ƙarar abu kaɗan zata ji ya sa zabura aguje.

           Da kiran Likitan da zuwansa ko minti goma ba'ayi ba, shigowa yayi cikin falon bayansa goye da jaka kamar yanda ya ke yiwa Kausar itama Aseela cewa yayi akaita ɗakin Kausar har rige-rigen buɗe ƙofa suke, kwantar da ita Daddynta yayi akan gado ya koma cen gefe yana kallo, Likitan da ke falo yana jiran fitowarsu juyawa yayi ɓangaren Inna Furaira suna haɗa idanu yaji idonsa na masa wani irin zugi da raɗaɗi ta ke wani baƙin jini ya ɗigo daga cikin idonsa, afakaice yasa wani farin ƙyalle ya goge, watsa mata mugun kallo yayi aykuwa ta ke cikinta yayi wata irin kartawa, abunda ta gani acikin idanunsa shi yafi komai ɗaga mata hankali zuciyarta na lugude ta hau karanto Ayatulkursiyyu harda su Li'ilafiƙuraish da Inna'anzalnahu jikinta banda ɓari ba abinda yake yi, saboda yanayin da mutanen falon suke ciki yasa ko kaɗan ba wanda ya fahimci halin da Inna Furaira ta ke ciki, da sauri ya sa kai ya shige cikin ɗakin, Alhaji Kabeer na tsaye yana kaiwa da komowa yaji shigowar likitan, kallo ɗaya yayiwa Alh Kabeer yace masa ya fita ya bashi guri, badan yaso ba ya fito daga ɗakin yana waiwayen Aseela da a lokacin ko numfashi bata yi.

           Alhaji Kabeer na fitowa Dr. Arjun yayi wata girgiza a take yanayin hallitarsa ta sauya zuwa wani tafkeken ƙwarangwal mai mummunar halitta, wani irin baƙin ruwa mai yauƙi ne ya gangaro daga cikin bakinsa yana shirin ɗiga a ƙasa da sauri ya ƙarasa dai-dai kan Aseela ya buɗe idanta wannan ruwan mai yauƙi ya ɗiga cikin ƙwayar idon ta, jikin ta ne ya hau wata irin karkarwa atake fatar jikinta ta fara daddarewa tana tsakewa ta jima a haka sannan ta fara komawa dai-dai yanda ta ke da farko, ahankali yarinyar ta buɗe idanunta ta sauke su akan ƙwarangwal ɗin nan, suna haɗa ido ta fara masa murmushi zanƙwala-zanƙwalan hannunsa yasa ya ɗauko Aseela yana rungumeta ajikinsa sa, kafeta da ido yayi sannan ya fara magana cikin hautsinannan yarensa, " murginsah fisasik linsaku yaukalbitins gursun ulsatkinbar midraskin zararansik mulbastu jinkasbuhu tadsinfar minsartunfat kilalin girbarn kinbar kin " ( Na hane ki da kuma bayyana komai ga waɗancen mutanen, domin kuwa idan kina haka zasu kaimu inda za'a bayyana musu ko mu su waye daga haka za'a nemi a yaƙe mu ta ƙarfi da yaji, banda kashin jini ko hawayen jini nan gaba duk wanda yayi miki abu na baki umarni ki ɗau fansa akansa ko wane ne, wancen karan anyi nasara akanmu wannan karan mu ne da nasara, nasara ta mu ce kafin ɗaukan fansa da sannu lokacin mu na nan tafe, BABBAN KUSKUREN SU HAIFAR KU DA SUKA ƘARA YI amma awadin kwanakinsu ya fara ƙarewa " banda murmushi ba abinda Aseela ta yi yana gama magana ta tsuke fuska sai ga hawayen jini na fita daga idonta, motsa baki ta farayi kamar mai magana tanayi tana wutsul-wutsul da hannu da ƙafafuwa, wage bakinsa ƙwarangwal ɗin yayi kamar mai dariya ya ce, " kinsak munfarkaf kiladinsa?? munafinga jalkinsba warbartikas mudraba wurjankinxa kujaimatus ?? " ( bazaki iya daina kowanne daga ciki ba? aykuwa hakan bazai yuwu ba dole sai dai ki ɗauki ɗaya ki bar sauran wanne zaki ɗauka?? )  hawayen jinin ne ya tsagaita ta kafe shi da ido ta hau kifta masa idanu, kwantar da ita yayi ya kai hannunsa wajen hawayen jinin yana gogewa da wannan farin ƙyallen, yana gama gogewa yasamu kyallen ya matse mata guntun jinin abakinta sannan ya ce, " Madri mafri magri marsar fintaskinbasi kulmansu " ( Na yarje da hawayen jini amma banda ragayya ko yafiya ko da akan Iyayenki ne )  yana gama faɗa yayi wata uwar girgiza atake ya rikiɗa ya koma siffarsa ta farko yana ɗaga hannu yana yiwa Aseela Bye bye, tana ganin ya bi bakin ƙofa ta fashe ta wani irin matsanancin kuka, Alhaji Kabeer na jin haka ya zabura zai shiga ɗakin Alhaji Habib ya dakatar da shi yana faɗin, " ƙa'idar Dr. Aryan ba'a shiga sai bayan minti biyar da fitowar sa " jiki ba ƙwari Daddyn Aseela ya koma ya zauna amma cikin zuciyarsa zumuɗin ganin ƴarsa yake yi musamman da kukanta yake karaɗe dodon kunnensa , Dr Aryan bayani ya fara musu kamar haka, " matsalar ciwonta yana shi ge da na Kausar sai dai da ɗan banbanci kaɗan, na Kausar bata kukan jini Aseela nayi, Kausar tana da matsalar ƙwaƙwakalwa yayin da Aseela koda ta girma zata tashi rass ba irin matsalar Kausar, Kausar ba komai take ci ba naga kayan abinciccika ita kuma Aseela babu abinda bazata ci ba indai tayi niyyar cinsa koda kuwa mutane basa ci, aguji ɓacin ranta sannan aguji haɗa su guri guda saboda gudun aukuwar tashin ciwon kowanne daga cikinsu, masu irn matsalar su basu da yawa a faɗin duniya hasali ma kuma babu maganin ciwonsu na warkewa har abada sai dai asamu wanda zai lafar da ciwon kuma ba kowanne guri ake samu ba, dan haka ku kiyaye ina musu fatan samun lafiya me ɗorewa atare da jinsin su " yana ƙarasa maganar ya gyara zaman jakar sa, Alhaji Kabeer da Hjy Kaleesat jikinsu ne yayi sanyi gaba ɗaya zuciyarsu ba daɗi, jiki a sanyaye Alh Kabeer ya ce, " likita godiya muke " kallan Alh Habib yayi ya ce, " nawa ne kuɗin aikin sa? " kafin Alhaji Habib yayi magana Dr. Aryan ya ce, " mun fi shekara goma tare bana karbar kuɗinsa sai dai insa shi yaje majami'a ya je bakin hanyar ya ajiye kuɗin mabarata zasu ɗauka, kabar yimun godiya saboda duk yiwa kai ne " yana gama maganar ya goya jakarsa abaya yayi hanyar fita kafin ya fice suka kuma haɗa ido da Inna Furaira yana watsa mata harara.

            Alhaji Kabeer ya ce, " dama har yanxu akwai waɗanda basu damu da abin duniya ba, ji fa irin ƙoƙarin da yayi amma wai bazai karɓi kuɗi ba " dariya Alh Habib yayi ya ce, " kabar gara ayni ban taba cin karo da sakaran likita kamar wannan yaron ba "  tattaunawa sukayi sannan suka wuce ɗakin da Aseela ke kwance, abin mamaki kamar ba ita ke kuka ba har tayi bacci abinta sai sauke ajiyar azuciya take, basu jima ba Alhaji Kabeer ya ɗaukota suka fito daga ɗakin, riƙeta yayi tsam a hannunsa kamar wani zai kwace masa, Inna Furaira da ta ke cen gefe zuru tayi tana ta naxarin maganganun Dr. Aryan, gaba ɗaya ji tai sam bata yarda dashi ba ko kaɗan bai mata ba musamman da ta lura da irin kallan ta yake ta watsa mata da jinin da ta gani ya ɗigo daga idon sa.

            Hajiya Kaleesat ce ta kalli maigidan ta jiki ba ƙwari ta ce, " Daddyn Aseela ya jikin nata? " miƙa mata ita yayi ya ce, " jiki da sauƙi sosai kingan ta " karɓarta tayi ta zurawa ɗiyarta ta idanu tana jin wani irin yanayi game da ita, Alhaji Habib ne ya ƙatse shirun nasu da, " wallahi ba yawon da bamuyi ba akan ciwon Kausar amma ikon Allah ko ina mukaje babu waraka sai da Allah ya haɗa mu da Doctor Aryan sannan cikin ikon Allah komai yake zo ma da sauƙi " Alhaji Kabeer na shirin magana kamar wacce aka tsunkuna Inna Furaira tai farat ta ce, " Alhaji dan Allah a ina kuka haɗu da shi?? " Hajiya Kaleesat ido ta zubawa Inna Furaira saboda sanin da tayi mata ko agida idan suna magana kowacce iri ce da Daddyn Aseela bata taɓa sa musu baki, shi kuwa Alhaji Habib azatonsa tambayar da Inna Furaira tayi taga ƙwarewar aikin likitan ne, shiyasa cikin zumuɗi ya bata amsa da, " Baba wallahi wata rana naje shopping a wani Mall muka haɗu da shi yaji ina waya da wani Dr ina sanar masa ciwon Kausar to bayan na gama sai ya yi mun bayanin shi ma likita a ƙasar Italy, ya ɗan bar aikin sa ne na wani lokaci ne cikin ikon Allah ya fara duba Kausar sai kuma gashi muna ganin nasara " Inna Furaira farat ta kuma yi ta ce, " Alhaji kenan bakasan gurin aikinsa ko wani nashi ba? " Hajiya Kaleesat ce ta kalli Inna Furaira ta ce, " Inna Furaira lafiya wannan tambayar fa " sai alokacin taga wautar da tayi sannan ta tuno da matsayinta agaresu, cikin girmamawa ta ce, " ayi hakuri Hajiya " murmushi Alhaji Habib yayi ya ce, " ba komai kinsan likita kamar Dr Aryan dole ajinjinawa ƙoƙarinsa shiyasa ma ta ke ta tambaya ta " Hajiya Aisha ce ta shigo cikin ɗakin bayan ta zauna take ƙara tambayar jikin Aseela, daga haka wani part ta wuce dasu ɗan madaidaici mai ɗakuna huɗu guda uku falo ne babba sai ɗakuna biyu acikinsa kowannen da toilet acikinsa, sai kuma wani ɗaki acen gefe idan akabi ta wata siriyar hanya ita ce zata sadaka da gurin, agyare yake tsaf ko ina sai ƙamshi ne yake tashi, agajiye Hajiya Kaleesat ta kwantar da Aseela sannan ta fara rage kayan jikinta, Alhaji Kabeer ne ya fara shiga wanka bayan ya fito itama ta faɗa toilet, sannan suka fara jero sallolin da ke kansu, acen kan dianning aka jere musu komai da zasu buƙata na abinci da kayan sha, sai kuma kayan ƙwalam da maƙwalashe  sun ji daɗi ƙwarai musamman yanda suka ga mutanen gidan suna ta nannan dasu  shiyasa ma suka saki jiki sosai kamar suna cikin gidan su, a ɓangaren Inna Furaira itama ruwa ta watsa ta jero sallolin dake kanta sannan ta koma gefe guda ta zauna tana lumshe ido, fuskar likitan ɗazu ne yake mata yawo acikin ƙwayar idonta ga wani irin tsoro da taji ya na mamaye zuciyarta, idanunta alumshe ta fara karanto addu'o' tanayi tana shafewa jikinta, buɗe idon yayi dai-dai da wulgawar mutum ta gefen labulayen ɗakin, takurewa tayi guri guda gabanta na duka uku-uku, ƙurawa gurin ido tayi lokaci ɗaya taji tsoron ya kau daga zuciyarta bayan karanto ayoyin Alƙur'anin da tayi, kai tsaye gurun da aka tanadar mata na cin abinci ta wuce, buɗewa tayi ta fara bawa cikinta haƙƙinsa sai da tayi ƙat sannan ta wuce akan gado ta kwantar da haƙarƙarinta.

*FATAN ALKAIRI GAREKU ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA ƘARA MIƘA GODIYA TA GAREKU BISA GA ADDU'O'INKU AKAN YARANKU KWANA BIYU DA BASU JI DAƊI BA, NAGODE ƘWARAI ALLAH BAR ZUMUNCI MASU KIRANA AWAYA MASU MUN MAGANA TA WHATSAPP, MUTANEN WATTAP DUK INA GODIYA ALLAH YA BAR ƘAUNA UBANGIJI YA HAƊA FUSKOKINMU ACIKIN ALJANNAH.*👏🏼👏🏼👏🏼

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETENơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ