19&20

377 33 4
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    19&20

          *BAYAN KWANA BIYU*
          Ganin jikin Aseela yayi kyau ya sa basu kuma samun wata damuwa ba, kuma duk dokokin da Dr. Aryan ya gindaya musu suna ƙoƙarin kiyaye su musamman dokar da ya ce musu karsu kuma haɗa Kausar da Aseela guri guda, ranar da suka cika kwana uku da zuwa suka shirya fita shopping domin siyayyar abun da ba'a rasa ba, acikin danƙareriyar motar Alhaji Habib suka fita Alh Habib na driven shikuma Abokin nasa na daga gefen mazaunin driver, sai Hjy Kaleesat a baya ita da Hjy Aisha suna hirarsu, Inna Furaira na cen kujerar bayan su Hjy Kaleesat tana riƙe da Aseela, tafe suke suna ƙarewa yanayin ƙasar kallo sai da yayi zagaye da su sannan suka wuce wani Shopping Mall, gaba ɗaya suka fito suka shiga ciki suka fara zaɓar kayayyaki kala-kala, haka itama Inna Furaira ba'a barta abaya ba domin ta ɗan ɗauki abinda taga tana da buƙata, sun kashe kuɗi sosai bayan sun biya aka sanya musu kayan acikin booth, fitowarsu harabar gurin ke da wuya suna tsaye Alhaji Habib na nunawa Alhaji Kabeer hanyar da zata sada su da Hospital ɗin da za'a fara kai Aseela sai jin dariya suka yi daga cen gefensu, wata mata suka gani da alama mahaukaciya ce saboda yanayin shigarta, tana da ɗan shekaru aƙalla zata iya shekara arba'in da biyar zuwa hamsin, matsawa gurin Inna Furaira tayi ta ƙarasa tana ƙyaƙyata dariya tana magana cikin yaren indiyanci, idan tayi maganar tayi maganar sai ta nuna Aseela dake hannun Inna Furaira, ganin abun nata ba na ƙare bane yasa Alhaji Kabeer ya zaro kuɗi ya miƙa mata da niyyar ya koreta, ƙin amsa tayi tana nuna masa Aseela da ke hannun Inna Furaira ta cigaba da surutanta, gajiya sukayi suka buɗe motarsu suka shiga suka barta a tsaye, tana ganin motarsu ta fara tafiya  tabi bayansu aguje tana ɗaga musu hannu tana surutai.

           Bayan sun fara tafiya Hjy Kaleesat ta cewa Alhaji Habib, " Daddyn Kausar ku ne kuke jin indiyan wai matar cen mai take faɗa ne? " jim yayi saboda bayasan gaya musu me yaji tana faɗa agame da ƴarsu Aseela, jin haka yasa Alhaji Kabeer ya ce, " nima nayi mamaki kuma sai naga kamar ta na nuna Baby Aseela " Hjy Aisha ce ta ce, " eh wasu surutan shirme ne take faɗa akanta bakwa ganin mahaukaciya ce sai sokiburutsun ta ta ke akan Aseela " sosai Alh Kabeer ya tsaida nutsuwarsa yana faɗin, " mai ta ke faɗa " Hjy Aisha bayani ta fara musu ta ce, " Aseela ba ƴarku ba ce, wai ruhin wasu ce ku naimar mata maganin gargajiya zaku samu waraka, idan ba haka ba muddin kuka barta ta girma ahaka ita ce ajalin ɗaya daga cikinku wannan alwashin ankullashi ne sama da shekara goma, zaku kaita asibiti kuma zasu ce aƙara mata jini to duk wanda ya bada jininsa aka sa mata zata dinga ɗaukan fansa da fuskarsa ne, ku san yanda zaku yi da ita tun yanxu kuma tun bata gagareku ba amma muddin kuka bari ta kawo ƙarfi dole jinin ɗayanku zai salwanta, zata shayar da jinin ɗayanku wajen shugaban ruhinsu hahahahaha ina faɗa muku ba ƴarku bace babban kuskurenku da bakwa harka da magungunan gargajiya, hahahahaha fansa fansa tazo ɗauka idan bakuyi da gaske ba har wanda babu ruwansa ma abin zai shafa, hahahaha nidai ku bani abinci zanje majamu'a kunsan gurasar mama tafi kowaccce daɗi, ina ƙara maimaita muku karku bari aɗebi jinin wani daga cikin ku kuma kunyi kuskuren sake haihuwarta......" tana tsaka da faɗar haka muka shigo mota muka taho to shi ne fa ta biyo ta na cewa, " ku zo kuji inkuka bani gurasa zan gaya muku duk hanyar da zaku rabu da ita cikin ruwan sanyi kuxo nan ku bani gurasa banasan kuɗi bana karɓar kuɗi. " kusan nan ma suna da mahaukata kamar dai cen gida Nigeria.

               Cikin halin ko'inkula Alh Kabeer ya ce, " lallai wannan surutan kam sai na marar kan gado Allah ya bata lafiya da sauran mahaukata baki ɗaya, ita kuwa Hajiya Kaleesat jikinta ya gama sanyi ta so  ta fahimci wani abu daga cikin maganganun mahaukaciyar, sai yanzu ne ta zurfafa tunaninta ta fara tunanin abubuwan da suke faruwa da ita tun daga samun cikin Aseela har zuwa haihuwarta, ita kanta ta fara zargin wani abu tanaji aranta anya kuwa Aljanu basu musanya mata Aseela ba kuwa, kukan jini kashin jini ƙwarangwal aƙwayar idonta, anya wannan bai isa ya sa sun fahimci wani abu su buɗe idanunsu ba?? Mai yasa mahaukaciyar bata dubi kowa ba sai Aseela Anya babu ƙamshin gaskiya amaganar ta kuwa, duk cikin zuciyarta take wannaan maganganun gaba ɗaya jin zuciyarta ta ke adagule babu walwala, har suka ƙarasa gida Hjy Kakeesat ta kasa katabuss idan suna hira suka sako ta sai dai tayi murmushin yaƙe ta amsa musu da ummm ko hmmmm.

        A  daren ranar kusan kwana tayi ido biyu babu bacci tana saƙa da warwara, dake Aseela agurin Inna Furaira ta ke kwana ranar sai Hjy Kaleesat ta barta agurunta suka kwanta tare, wajen ƙarfe uku da rabi bacci ne yayi awon gaba da Hjy Kaleesat bata jima da bacci ba ta fara wani mummunan mafarki, wata yarinya ta hango yar ƙyaƙyƙyawa batafi shekara hudu zuwa biyar ba aduniya, tunkaro ta take yi ƙwayar idonta ya juye babu ko ɗigon baƙi aciki, tana ƙarasowa gurinta ta taga faratan yarinyar sunyi zaƙo-zaƙo harshenta na fidda wani baƙin ruwa, da ƙarfin gaske ta kaiwa Hjy Kaleesat yanka tana faɗin, " kin fara fahimtarmu dole mu ɓatar dake domin ɗaukan fansa "  cikin ikon Allah, Allah ya bawa Hjy Kaleesat ikon karanto Addu'a tana kaiwa yarinya duka agoshinta, ihu yarinyar ta fasa atake ta ɓace daga gurin, afirgice ta farka tana furta kalmar Innalillahi.....Tashin ta ne yayi dai-dai da jin kiran sallar asuba shiyasa ma ta taje ta ɗauro alwala ta tashi Alh Kabeer sannan ta gabatar da sallar Asuba, tana idar wa ta ɗau carbinta ta koma kan gado tana ja har bacci ya kuma ga ba da ita.

        Cikin baccinta taji ana tashin ta afirgice ta buɗe ido Daddyn Aseela ta gani riƙe da ita yana faɗin, " Kaleesat tashi mu wuce Asibiti kinga halin da na farka naga yarinyar nan aciki " idanunta ta kai kan Aseela aykuwa tayi arba da yarinya na zirarar da hawayen jini ga gefen goshinta nan yayi wani ja kamar wacce ta bige agurin ko aka doketa agun, ta ke gaban Hjy Kaleesat yayi wata irin bugawa har sai ta da sa hannu ta dafe gurin, ganin ta kasa tashi kuma bata ce uffan ba ya sa ya rufeta da faɗa, jiki a sanyaye ta yunƙura ta tashi ta sake kaya ta karɓi Aseela, karo na farko kenan da taji sam ciwon Aseela bai ɗaga mata hankali ba hasalima ji tai yarinyar ta fara fice mata daga ranta, Inna Furaira ta leƙa ta taso sannan suka fice alokacin tuni Alh Habib ya kunna mota yana jiran fitowarsu.

       Kai tsaye wani babba Private Hospital suka wuce suna zuwa aka karɓe ta likitoci suka fara baje basirar su akanta, bayan wani lokaci sai ga Doctor ya fito ya nemi ganawa da su, ba musu suka bi bayansa bayanin farko da ya fara musu shi ne ana buƙatar ƙarawa Aseela jini.

     *IDAN AKAMUN ƘWAUREN COMMENTS NEXT SAI KUJI KIƊAN GENERAL A SAMA.*🤣💃🏼

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now