61&62

307 31 4
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    61&62

          _Lokaci guda na sha jinin jikina domin na fahimci wata manufa daga gurin wannnan gawurtaccen bokan, na lura da san cimma burinsa ne zai sa na aikawa Mai Ifritu abinda ya umarceni, fargaba ta ɗaya taya za'ayi na iya aikatawa Mai Ifritu abinda ya sani alhalin shi da kansa ya jinjinawa hatsabibancinsa, gaba ɗaya kaina ne ya kulle zuciya ta tamun babu daɗi na rasa me yake damuna, ina shirin yi masa magana daga cen gefe mukaji faɗowar wani abu faaaaaaf da sauri muka juya muna kallan gurin, wani mutumi muka gani yana sauke numfashin wahala, cikin tashin hankali da razani mutumin nan ya fara jan ciki yana roƙon GUBUBAR BIN GUNGAR, " Dan Allah kamun afuwa ka yafemun karka cutar dani, ni kaɗai na rage agurin mahaifiyata kuma ta tsufa idan ta rasa ni zata iya shiga cikin wani yanayi, ya kai GUDUBAR nasan na aika laifi agareka musamman dana bijirewa umarninka, amma na roƙeka ka bani dama ayanxu xan wanzar da duk wani abinda kake buƙata " wata iriyar dariya GUDUBAR ya ƙyaƙyace da ita sannna ya kalli wannan mutumin ya ce, " Ka tafka babban kuskure sanin kanka ne GUDUBAR baya afuwa bare yafiya ga duk wanda ya saɓawa umarninsa, dole inhukuntaka da hukunci dai-dai da laifin da ka aikata mun " Yana gama faɗa ya hurowa mutumin wata irin iska acikin iskar bakin nasa waɗansu irin ƙwari ne suka dunfari jikin mutumin, ta ko'ina suke kaimasa cizo banda ihu da ƙarajin sa babu abinda yake tashi agurin, da alama ƙwarin nan jinin jikinsa suke zuƙa lokaci guda mukaji ya daina wannan kururuwa numfashinsa ya ɗauke wanda yake tabbatar mana da mutuwarsa, alokacin nan na shiga tashin hankalin da tunda nazo duniya ban taɓa shigarsa ba, jikina banda rawar ɗari babu abinda yakeyi gumi ta ko'ina sai yankomun yake, gefen wata bishiya ya kalla sannan ya ce, " Kai Mai fanduƙa ku maida shi inda kuka ɗauko shi " tun kafin ya gama faɗa muka ga mutumin nan ya ɓace daga gabanmu._

      _Ina cikin jimami na riski muryar bokan nan ya ce mun, " Kai Habibu inafatan kaji abinda muka umarce ka? "  saboda sauri har taune harshena nake domin na amsa masa saboda gaba ɗaya na gama tsorata, yana jin  na amsa masa, ya cigaba da cewa, " Bazan karɓi koda sisin kwabonka ba wannan aikin da na saka shi ne ladan biyan buƙatarka, lokacin zamanku yaxo ƙarshe acikin daula ta dan haka ku runtse idanunku " babu ɓata lokaci haka muka rintse idanunmu nida Alhaji Musa wata irin guguwa mukaji na yawo damu na ɗan wani lokaci sannan muka fara jin hayaniyar mutane, buɗe idanmu ke da wuya muka riskemu acen babban titi inda muka yi Parking ɗin motar mu, Mamaki ne ya kamani cikin zuciyata nake jinjina hatsabibanci irin na wannan hatsabibin bokan, Motar mu muka shiga muka ɗauko hanyar gida._

       _Tunda muka dawo gida abun duniya ya dameni na rasa ta wane hali zan ɓullowa lamarin Mai Ifritu wannan shi ne ake cewa gaba kura baya siyaƙi, tunawa nayi da cewar ya umarceni da sai nayi mu'amala da matar aure kafin naje gurin Mai Ifritu nan ma rasa abinyi nayi na rasa wacce mace zan samu wacce zata amincewa buƙata sannan kuma daga baya bazata tonamun asiri ba, Mata ta ce ta faɗo mun araina atake wani tunani ya tsargo mun domin nasan ko sama da ƙasa zata haɗe bazata amince da wannan baƙatar tawa ba, Hajiya Saratu ce ta faɗomun araina sai kuma na rasa yanda za'ai na sameta har mu tattauna tunda bani da lambarta bare muyi keɓancewar sirri da ita, tunowa nayi da wayarki Aisha a take na ɗauki wayarki na duba Number ta cikin sa'a kuma na sameta, da sauri nayi na ɗauka nayi Saving ɗinta da Alhaji Abdurrahman2 saboda koda wata rana zata kirani bana kusa kar asamu matsala, tunda nasan Aisha bata ɗaukan wayata muddin taga kiran daga Abokaina ne._

        _Cen cikin Bedroom ɗina na shige sai da na sanya key har a falon farko sannan na kirata bugu biyu naji ta ɗauka, bayanin kaina nayi mata sannan na gabatar mata da tawa buƙatar, ɗan jim tayi sannan taƙi amincewa da buƙata ta, ganin haka ba ƙaramin tashin hankali ya sani ba, ashe itama tayi haka ne saboda kar nayi zargin ko ta saba irin wannan mu'amalar tun cen da jimawa, sai dai itama ta roƙeni buƙatarta akan cewar muddin ta amince mun to duk abinda ta nema agurina bazan bijire mata ba, da sauri na amsa mata kasancewar ina cikin ruɗani nidai burina bai wuce na tsallake siradin boka GUDUBAR ba._

        _Rana muka tsaida nida ita akan zamu tafi cen garin Jos mu aiwatar da wannan aikin da aka sani, sai da na jaddada mata sosai a ranar karta kuskura tayi Sallah ko da ta Asuba ce inba haka ba sai asamu matsala, kamar yanda  muka tsaida rana haka ta shiryawa Maigidanta Alhaji Abdurrahman ƙarya akan zataje Kaduna gidan Yayarta, Hanya muka ɗauka nida ita har muka sauka acen garin Jos wani Hotel na kama mana azuwan sauka nayi nida matata, sai da muka gama duk masha'ar mu sannan muka ɗau hanyar Kogon dutsen Mai Ifritu da wannan ƙoƙon kan ƙwarangwal ɗin nan acikin leda, muna tafe jikina banda rawa babu abinda yake yi duk wanda ya kallemu sai ya fahimci irin tashin hankalin da muke ciki, shigar mu cikin dajin da Mai Ifritu take tsoronmu ya tsananta har gani nake kamar bazan iya aiwatar da abinda aka umarceni ba, kamar daga sama mukaji anfara faɗin, " KU TAFI KANKU TSAYE MUNA BIYE DAKU BAZAI CUTAR DA KU BA, ZAMU TAIMAKA MUKU HAR ZUWA BAKIN KOGON DUTSENSA, SAURAN AIKIN ZAMU BARKU KU AIWATAR DA KANKU DOMIN BAMU IKON TSALLAKAWA ZUWA CIKIN KOGON DUTSENSA " ɗan sakin jiki mukayi amma duk da haka muna cikin damuwa har muka ƙarasa cen bakin Kogon dutsen da Mai Ifritu yake ciki._

        _Kamar yanda al'adar gurin Mai Ifritu take sai da muka ambace shi sau uku sannan mukayi ta maza muka shiga dukda gaba ɗayanmu kowa gabansa dukan uku-uku yake yi, Muna shiga muka ƙarasa bakin gurin zaman Mai Ifritu kamar yanda muka saba samunsa yana bakin rijiyarsa yana tsaubbace-tsubbacensa, shigarmu cikin kogon sai gani mukayi ya sa hannu bibbuyu ya dafe kansa yana kwarma wata irin ƙara mai ɗaga hankalin mai sauraro, Yana cire hannunwansa ya kalleni da Rinannun idanunsa da suka fara canja launi zuwa koraye  yana faɗin, " Kunci Amanata kun haɗa kai da GUDUBAR dan ku cutar dani, tabbas nasan yau mummunar rana ce agurina tunda duk bincikena na kasa gane su waye ke tafe zuwa Kogon dutse na, amma da sannu shuɗaɗɗun aljanun kogon dutsena zasu ɗau fansa akanku" hantar cikina ce ta kaɗa jikina ya fara karkarwa tsoro ya ɗarsu cikin zuciyata, kamar raɗa haka naji Muryar GUDUBAR yana faɗin, " Idan ka jira sauraron kalamansa zai hallaka ku batare da kun aiwatar da abinda ya kawo ku ba kai maza ka jefa ƙoƙon kan ƙwarangwal ɗin nan kuma kuyi gaggawar barin gurin inba haka ba ruhinsa zai cigaba da bibiyar rayuwarku ba tare da kunsani ba " yana gama faɗa na jefa wannan kan ƙwarangwal ɗin acikin rijiya, da sauri muka miƙe tsaye muka ɗau hanyar fita jikinmu na karkarwa, har munkai Bakin ƙofa mukaji ya ƙwalla wata ƙara, a tare nida ita muka juya muna ganin halin da yake ciki, Naman jikinsa ne yake daddarewa wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga jikinsa daga cikin rijiyar kawunan ƙwarangwal ne babu adadi suka zuro kawunansu suna tsotsar wannan ruwan dake fita daga jikinsa, wata yana muka gani ta fito daga jikinsa ta tunkaro mu da sauri muka fice daga cikin Kogon dutsen, muna fitowa muka farajin wata irin ƙara lokacin guda wannan kogon dutsen ya fara rugujewa yana ruftawa ciki, ganin haka yasa muka baza da gudun gaske ba mu muka tsagaita da gudu ba sai da muka kusa ƙarasawa gurin da jama'a suke._

  *INA MATUƘAR GODIYA A GAREKU ƳAƳAN BAIWA NAGODE DA ADDU'ARKU UBANGIJI YA BIYA MANA BUƘATUNMU NA ALHERI, INA ƘAUNARKU FISABILILLAHI ALLAH YA BAR ƘAUNA❤️❤️.*

    _Ummou Aslam Bint Adam_😉

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now