67&68

340 30 6
                                    

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

           *ASEELA*👩🏻‍🦱👹
                  *BY*
*AMEERA ADAM*
        *FOLLOW ME @WATTPAD*
              *AmeeraAdam60*

https://chat.whatsapp.com/JvgnWylSuGw9wq5MVGAjEz
   

                    67&68
_*GABA ƊAYA WANNAN SHAFIN NAKU NE MASU KARANTA LITTAFIN ASEELA, INDAI KINSAN KINA KARANTA BOOK ƊIN NAN KI ƘADDARA AZUCIYARKI WANNAN SHAFIN NAKI NE😊😊*_

   _AMMA FA SAI DAI KU KARANTA DA HAƘURI BAN TACE SHI BA_🙊

       _Washegari tun sassafe Mahaifiyata ta shirya ta sa nima na shirya, karyawa kawai mukayi muka ɗauki hanyar wannan ƙungurmin dajin da muka je muda Hajiya Tani, lokacin da muka isa gurin bokan rana tuni ta fara buɗewa muna isa bakin bukkarsa muka hangeshi acen gaban wata jingegiyar biahiyar kuka ya runtse idanunsa yana wasu irin surutai, anan muka jirashi har ya ƙarasa abinda zai sannan ya ƙaraso wajenmu, kallanmu yake ɗaya bayan ɗaya sannan ya bushe da dariya yana faɗin, " Lallai yau kun zamto masu sa'a domin yau na gana da Garke duk kuwa wanda yazo a irin wannan ranar dole ma mu biya masa buƙatarsa, saboda wannan wata irin mafificiyar rana ce agaremu da muke cikin tsananin farin ciki " Murmushin jindaɗi mahaifiyata tayi, gaba ya wuce muna biye dashi a baya cen mazauninsa yaje ya zauna, motsa baki Mahaifiyata ta farayi tana shirin magana dan haka ya dakatar da ita da hannunsa sannan ya ɗago da idanunsa ya ce, " Bama buƙatar ƙarin bayani, kinzo ne akan cin amanar da Aminiyarki tayi miki tsakanin ƴarki da tata ƴar " cikin azarɓaɓi Mahaifiyata ta fara magana, " Boka dama zuwan da nayi gurunka kenan, abinda nake so da kai araba tsakanin Hannatu da Abdurrahman akuma ninninka soyayyarta a zuciyarsa ko nawa ne ka faɗa zan bayar " Kafeta yayi da Idanu sannan ya ce, " Me kike ci na baka na zuba? Aikinki ko sisin kwabo bazan karɓa ba kuma zan baki laƙakanin da har abada babu wani boka da zai iya karya shi, Abdurrahman ko a hanya yaga Hannatu idan bishiyar cen zata kulaki zai kulaka " Cikin jindaɗi Mahaifiyata ta fara rattabo masa godiya kamar wacce ya yiwa kyautar hajji, wata kwalba ya ɗauko mai ɗauke da wani irin jan ruwa aciki kamar jini, juyata ya fara yi sannan ya miƙo mana ya ce, "Wannan kwalbar da kike gani kije ki binneta a inda kikasan Hannatu da Abdurrahman zasu iya tsallakawa, ga wannan turaren ki shafa shi ki bi hanyar da kika san zaki haɗu da shi na tabbata ko uwarsa bata isa ta hana ya aureki ba, waɗancen kayan aikin da na taɓa baki su a baya ki haɗa su ki ƙona, alokacin ta bamu maƙudan kuɗi masu yawan gaske, ta zubarwa su Garke jinin bunsurai dana baƙaƙen zakaru da baƙar Jaɓa shiyasa lokaci guda kika ga ya juya miki baya, wancen karan aiki tayiwa Garke yanxu kuwa Garken da kanta ce tace amiki aiki tunda kinzo a lokacin da muke ganawa, lallai ke mai sa'a ce domin ba kowa ke riskata acikin wannan yanayin ba, sama da shekara Ashirin ina gurin nan kece ta huɗu acikin waɗanda suka taɓa riskata ina ganawa da Garke, ku tashi ku tafi indai kun aiwatar da abinda muka baku buƙatarku ta biya kamar kin aureshi kin gama,, kuma muddin kika shiga gidansa sai dai mutuwa ta raba, a kwai wani ƙulallen abu da zai iya faruwa anan gaba tsakaninki da shi amma har yanxu mudubina ya gagara haska mun duk abinda zai faru " muna gama saurarensa muka xube muna masa godiya sannan muka baro gurunsa, ko ajikinmu babu wanda ya lura da maganarsa ta ƙarshe mudai burinmu muje mu aiwatar da abinda ya bamu domin biyan buƙatar kanmu._

   _Bayan mun koma muka fara neman hanyar da zamu aiwatar da wannan aikin da boka ya bamu ba tare da wani ya ganmu ba, dabara ce ta faɗowa mahaifiyata tace zata je da duku-dukun asuba ƙofar gidansu inyaso sai ta binne yanda aairinmu bazai tonu ba, hakan kuwa akayi kafin kwana biyu tuni muka aiwatar ta komai yanda ya kamata, tun daga ranar kullin sai na zama kamar wata ƴar yawo musamman idan yamma tayi ina dakon haɗuwata da mahaifinku koda zaizo hira gurun Hannatu, sai da shafe sati guda ban haɗu da shi ba domin kusan duk zuwan da zanyi hanyar ƙofar gidansu ko insamu ya ajiyeta a mota ya wuce ba tare da ya fito ba ko kuma na hangi kurar motarsa ta wuce har Allah ya ci dani wata rana suna tsaye suna hira, jikina har ɓari yake saboda yanda nayi arba dashi, kafin na ƙarasa gurinsu sai da na saita nutsuwata cikin muryar kissa nayi ƙasa da murya nayi musu sallama, jin ƙamshin turarena ne yaja hankalinsa har ya ɗago dan ganin maiyin sallamar, ɗago idanunsa yayi dai-dai haɗa idanunmu guri guda kafeni yayi da idanunsa kamar mai san tuna wai abu, ɗan jim yayi yana nazari ganin haka ne yasa Hannatu cikin tsiwa ta fara magana, " Ke dallah sakarya meye haka mutane na zaune suna hira zaki zo ki wani tsomo musu baki mai ya kawo ki gurin? " a zabure ya ɗaga kai yana kallonta tana shirin cigaba da magana ya buga mata tsawa yana faɗin, " Ke bakida hankali ne me kike yi a gabana  Matar da nake shirin aure kike gayawa haka, ki shiga taitayinki inba haka ranki zaiyi mummunan ɓaci " A duniya tunda nake bantaɓa jin farinciki irin na ranar ba, nan da nan naji kaina yayi wani irin girma take na fara watsa mata harara ina wani fisge kai gefe, Kallona yayi yana duba agogonsa ya ce, " Dear muje na sauke ki a gida ni bansan ma mai ya kawo ni gurin wannan yarinyar " Hannatu tunda ta saki baki cikin mamaki take binmu da kallo saboda gaba ɗaya kanta ya ɗaure da mamaki tana shirin magana tuni ya buɗemun gidan gaba na shige, shima ya zagaya ya shiga da ƙarfin gaske ya bawa motar wuta muka bar ƙofar Gidansu Hannatu yayin da ta faɗa gidansu tana rushewa mahaifiyarta da matsanancin kuka._

ASEELA COMPLETEWhere stories live. Discover now